← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 128

Sashe 66

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran sallah asuba ne ya tashi Nihal mika Nihal tayi dauke da addu'a a bakin ta kasancewar baccin jiya ba karamin dadi ya mata ba, ganin ta saman bed ne yasa Nihal zabura ta mike da sauri tana waige-waige tana tunanin me ya kawo ta bed ita dake kwana a sofa, abinda ya faru da ita jiya ne ya fado mata a rai murmushi Nihal ta saki tare da maida gashin kanta baya tace, ashe dai yana da kirki yaye blanket din jikin ta Nihal tayi ta fara takawa a hankali har ta isa bakin sofa ganin ba Sultan ya sata rike kugu tana waige-waige tabe baki Nihal tayi, kasancewar bata sallah gyara dakin ta shigayi yayi fes sannan ta Shige toilet ta sheka wanka ta fito lokacin gari ya fara haske sultan be dawo daga masalaci ba, shafe jikin ta da lotion Nihal tayi sannan ta bud'e drawer ta curo black rigar ta wanda akayi ma dinki kamar bubu, shiryawa Nihal tayi cikin kayan ba karamin kyau Nihal ta zubaba gaban rigar anjera ma shi white stone's masu masifar kyau lipstick Kawai ta shafa ma lips din ta tare da Karewa kanta kallo ta cikin mirror taba goshin ta Nihal tayi abinda ya faru jiyane ya fara dawo mata cikin kwayar idaniyar ta, murda handle din kofa da akayi ne yasa Nihal waigowa har gashin kanta iska na kad'a shi ido hudu sukayi da Sultan wanda shigowar shi yanzu kenan kallan ta sultan ya shigayi tun daga forehead din ta har kafafuwan ta wani irin kyau Nihal din ta Kara mashi, a hankali sultan yake takowa har ya Karaso daf da Nihal wanda itama din kallan shi take tamkar yau suka fara ganin juna su a hankali sultan yasa lalausan Hannun shi ya, talabo da fuskar Nihal yana kallan goshin ta lumshe idanuwan ta Nihal tayi, bin fuskar ta da kallo sultan yake yana kallan yadda eye lashes din ta suka wani kwanta kamar tasa na kanti a hankali Nihal ta bud'e lumsasun idanuwan ta, ta sauke su kan kyakyawar fuskar Sultan, kalaman Dara ne su ka Shiga yimata yawo a brain tana kallan Sultan take tausayin shi na shigar ta jin kamar tayi kuka ne yasa Nihal ja da baya tana maida gashin kanta Baya, kanta a kasa tace, "ina kwana" ko amsar sultan bata tsaya saurara ba, ta raba ta gefan shi ta wuce da sauri, babban kitchen Nihal ta nufa tana Shiga bayi suka zube suna kwasar gaisuwa amsa masu Nihal take cikin sanki fuska Sannan ta umarci Yasmin ta fere mata dankali ita kuma ta daura ruwan flaks cikin dankankanin lokaci ruwa ya tafasa ta juye a flaks lokacin har Yasmin ta gama fere dankalin Nihal bata wani dau lokaci ba ta soya dankalin tare dayin peper soup din yan'ciki ta juye a warmer Yasmin da bariri suka biyo ta da tray din abinci har part din su, suna zuwa bakin kofa Nihal ta dakatar da su tare da amsar tray din Karasawa da shi dining area ta jera komai umarni tabawa su Yasmin da suna iya tafiya idan tana bukatar su zata neme su to suka ce mata sannan kowa ya koma bakin aikin shi, zama Nihal tayi saman two star tare da kuna TV tana kallan MBC2 kamshi turaran Sultan daya mamaye mata hanci ne ya sata dagowa sultan ne sanye cikin suit din shi american rose color yayi kyau sosai sajan nan na shi ya kwanta luf-luf da shi red lips din shi yayi kamar yasa jan baki, Hannun shi na rike da briefcase, ya Allah Nihal kawai ta iya furtawa cikin zuciyar ta kauda Kai Nihal tayi dan kar sultan ya gane tana kallan shi ya raina ta ganin ya nufi dining area yasa Nihal bin shi a baya jan kujera sultan yayi tare da aje briefcase din shi ya zauna, plate Nihal ta janyo tana serving na shi abinci, tana serving nashi Sultan yana satar kallan ta ta kasan ido cikin zuciyar shi yana cewa, why this why do I always looking at her cute face, the most annoying thing yadda nake wasting time ina kallan ta I hate this , tura mashi plate din da Nihal tayi gaban shine ya sashi dawowa daga duniyar tunani a hankali Sultan ya fara cin abinci wani irin dadi abincin yayi ma Sultan jin testing din abincin yake kamar na jiya, amma yadda ya keyi da face na shi se ka rantse abincin ba dadi saboda yadda yake cin magani kamar yana cin mad'aci saboda baya so Nihal taga kamar abincin ya mashi ta raina shi, Nihal ko serving kanta tayi tana cin abinci a hankali da sun hada ido da Sultan se tayi kasa da kanta, shigowar yakumbo dauke da tray abinci ne ya Katse masu tunani lokaci daya itama yakumbo sakatarere tayi tana bin su da kallo tana mamakin waye ya kawo masu abinci, a haka har ta karaso tare da zubewa tana kwasar gaisu tana kokarin aje tray din Hannun ta da sauran bayin dake bayan ta suna kokarin aje na hannun su aje fork din hannun ta Nihal tayi tace, "yakumbo kuna yi tafiya da abincin aba ma wasu, daga yau bana bukatar ana kawo kowani kala abinci ba tare da izinina ba" galala yakumbo tayi tana bin Nihal da kallo tana Kara tabatar da zargin ta akan Nihal jan yan'mata kafafuwan su sukayi tare da kwashe Kayan abincin juyowa Nihal tayi tana kallan fuskar sultan a tunani ta ko ze watsa ta ganin kamar hankalin shi baya kan su yasa Nihal sauke ajiyar zuciya.

Gimbiya jalila ce ke zagaye daki tana huci kamar kububuwa tace, "yau ma yariyar nan koroku tayi da kwanikan abincin! Gimbiya jalila ta ida zancan tana zagaye parlour rai bace "wai mi yariyar nan take nufi da amshe ragamar girkin sultan a hannu ta, hakan na nufin ta gano boyayan sirrin mune komi? idan ko haka ne lahira za tayi bakuwa, saboda na tabatar da zargina a kanta fa yau na aika da breakfast shine zata koroku da shi"
"Ke ma dai Gimbiya kin gani, gabaki daya yanzu ta mamaye zukatan yan'gidan nan se abinda tace ga yaran nan na lura wani irin so yake mata ko dauke idanuwan shi baya iyawa a gaban mutane idan yana kallan ta se dai mu ce Allah ya kyau ta riga tayi kaka gida mtsww"
"tabas ko wata yarinya ta kusa ta zama gawa danni ba'a Shiga gona ta a kwana lafiya, kawar da ita awajena abune mai sauki, idan na kashe ta kin ga se ya fadi ya mutu" Gimbiya jalila ta ida zancan tana dariyar keta can kuma se tayi shuru yakumbo ta dasa da cewa, "Gimbiya kinyi magana Dan yariyar nan kadangaran bakin tuluce me hana a sha ruwa! tsaki Gimbiya jalili ta saki tare da shigewa Daki a fusace.

```Taku har kullun salma mas'ud nadab```
[1/7, 2:29 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 91_92*

A harabar prime college school motar Sultan ta faka a dai-dai bakin hall din exam, a hankali ya dago ido yana kallan Nihal dake makure jikin kofa murmushi Sultan ya saki ganin se faman bud'e kofa take amma ta kasa matsowa yayi dai-dai setin ta har suna jin saukar numfashin juna su, raba hannuwan shi Sultan yayi tare da bud'e wa Nihal kofa yana juyowa karfa suka had'a ido tsare ta da ido Sultan yayi kalaman da Nihal ta fada mashi jiya da dare suka shiga dawo mashi kamar a lokacin take fada mashi, lumshe ido Sultan yayi jikin shi ya kara sanyi sannan ya janye jikin shi ya koma ya zauna tare da gyara zaman suit din shi, tsare shi da ido Nihal tayi tana kallo dagowar da Sultan zayi karfa suka hada ido kauda kai Nihal tayi da sauri zata fice, Sultan ya ruko hannun ta tare da daura mata 1k sannan ya saki hannun ta yana cewa, "zanzo na dauke ki idan kin gama exam" kallan shi Nihal tayi tare da bud'e lalausan hannun ta tare da cewa, "mizan yi da kudin ka sultan, ka amshi kudin ka bana so! Had'e rai Sultan yayi tare da tsare ta da ido yana cewa, "na baki ne saboda Ammi ba saboda kai na ba," tab'e baki Nihal tayi tana cewa, "Nima na amsa ne saboda Ammi kawai" sannan Nihal ta fice daga motar har ta fice sultan na kallan ta, sannan motocin Sultan suka bar harabar makarantar

Murmushi Nihal ta saki tare da shakar iska me sanyi a hankali ta furta "Alhamdulillah alakuli hali,! cikin natsuwa Nihal ta karasa hall din da aka tanada dan yin exam tana shiga taga students duk zaune kowa na harkar gaban shi kujerin ne birjik kowani mutum yana da seat daya, a hankali Nihal ta karasa seat ta zauna kallo ne ya koma kanta kasancewar students din basu santa ba suka fara magana kasa-kasa mazan da matan, wadda ke bayan seat din tace tatabota juyowa Nihal tayi fuskarta dauke da murmushi Itama yariyar murmushi ta saki tare da cewa, "sannu ki"
"yauwa! Nihal tace sannan yariyar tace, "suna na Nana, ke kuma fa?
"Nihal..! Murmush Nana ta saki tana cewa, "amma dai ke external ce"
"Eh.! Nihal tace sannan ta juya bata wani dade ba aka fara raba booklet har aka zo kanta, Nihal taji dadi sosai ganin duk abinda ta karanta ya fito cike da jin dadi ta gama exam din ta na English suka fito kafin a shiga basic technology.
Chapter 66 · 0% Book details