Sashe 64
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
direct dining area Nihal ta wuce lokacin kowa ya halara maimartaba ne kadai babu kasancewa tare da waziri zasuyi dinner cikin natsuwa Nihal ta karaso dining area tunda Sultan ya hango Nihal ya kafe ta da idanuwan shi yana kallan yadda Nihal ke takowa of coz he can't stop looking at her, muryar Nihal ce ta daki dodan kunna shine yasasa dawowa daga duniyar tunani, tana cewa cikin siririyar muryata "barka da war haka! Nihal ta fada tana mai jan kujera kusa da Sultan lumshe ido yayi saboda kamshin turaran Nihal daya ziyarci hancin shi iskar bakin shi me sanyi Sultan ya furzar zuciyar na tsana ta harbawa, gabaki daya yan dining suka amsa "barkan mu juna" ban da Nazili dake ta faman aika wa Nihal da mugun kallo, murmushi mom tayi tare da taba kumatun Nihal tace, "masha Allah daughter kinyi kyau," murmushi Nihal tayi tana sunkuyar da kanta kasa, Yakumbo dake gefe tana kokarin serving Sultan abinci ne Nihal ta kalla kalaman Dara ne suka shiga dawo mata a kwakwalwa bata san sada ta rikewa Yakumbo hannu ba kallan juna ido cikin ido suna Shiga yi yakumbo da Nihal take anan yakumbo tasha ruwan jinin jikin ta tana kallan Nihal, ita kanta Nihal ta rasa dalilin da yasa ta tsani yakumbo, ba yakumbo ba kad'ai har Gimbiya jalila da Ashad se da suka kalli juna, murmushi Nihal tayi tare da cewa, "na hutace ki zanyi serving nashi da kaina! Ammi dake gefe da mom ba karmin dadi suka ji ba Gimbiya jalila ko wani kulutun bakin ciki ne ya Mata tsaye a makoshi, me yarinyar nan take nufi da yin hakan! yakumbo data ja baya ta tsaya tsanar Nihal da Sultan na kara narkewa a zuciyar ta, tana kallan su ta kasan ido, Ashad ma kallan Nihal yake yana tufka yana warwara, kallan juna Ashad da Gimbiya jalila sukayi suna aika wa juna su sako ta kasan ido kamar haka lalai kam akwai jan aiki a gaban mu!, warmer Nihal ta bude tare da serving sultan abincin data girka da kanta Sultan dai shuru yayi yana tunanin dalilin da zai sa Nihal ta hana shi cin abincin da kowa ze ci, turo mashi plate din da Nihal tayi ne ya sasa dawowa daga duniyar tunani tsare Nihal yayi da ido itama din kallan shi take Basmal ce ta katse masu tunani dacewa, "gaskiya Aunty na kina ji da yayana yanzu wannan abincin da kanki Kika girka? na zo zanci Dara ta Hanani wai na yayana nane, gaskiya aunty na kina nuna mana launin fata shi se a dafa mashi nashi da ban gashi kamshin abincin duk ya cika mana hanci daga ji zeyi dadi, gaskiya nima zanci! Nasim dake kusa da Basmal yace, "nima! rufar ma wermar sukayi suna zubawa suna santi spoon daya Basmal tayi tare da lumshe ido tace, "gaskiya food din nan yayi sweet, Ammi ya Kamata ki dandana" to Ammi tace Dara na serving nata abincin, murmushi yake Nihal tayi tana kallan sultan a hankali ya sa spoon a plate din spoon daya yayi tare da lumshe ido ganin idanuwan su Ammi na kanshi yasasa saki smile tare da daura hannuwan shi saman na Nihal a hankali ya furta "thank you hayate! tare da manna mata pack a lalausan hannu ta, tsare shi da ido Nihal tayi tare da yin saurin ta zame hannun ta dake cikin na sultan tare da kauda Kanta tana mai cigaba da cin Abinci, Nazili dake zaune ta cika fam kamar ta tarwatse aje spoon din Hannun ta tayi ciki plate tare da sakin murmushi rainin hankali tace, "Nihal! Dago da idanuwan ta Nihal tayi tana kallan ta murmushi ta saki tare da daga gira tace, "amma nayi mamaki yadda kika iya girki dama gidan almajirai ana daura tukunya? Kuma ko ana daurawa, I think ba dai irin wannan ba se dai tuwon dawa miyar kuka! idan ansamu na Allah bani wahidi! Gabaki daya kowa na dining se da yasha ruwan jinin jikin shi Gimbiya jalila ko dadi ta ji sosai ganin tsinkin da Nazili kewa Nihal ko ba komai ta biya ta a daran nan, Mom ko ji tayi zuciyar ba dadi ita da Basmal da Ammi jikin su yayi sanyi, tsare ta da ido Nihal tayi tana kallo tana hadiye-hadiye d'aga gira Nazili tayi tare da cewa, "Na manta fa ashe almajirai d'ai-d'aya ne ke da gida amma ke nasan baku da shi saboda rashinshine...! Sultan ne yace, "Nazili ! Cikin angry voice saboda Kalaman Nazili sun fara sosa mashi zuciya, duk da cewa ba Karya Nazili take ba yes Nihal almajira ce but now she is my wife, yanzu ta tashi daga almajira ya Kamata Nazili ta dinga gyara Kalaman ta! tsare Nazili da ido Sultan yayi, lumshe ido Nazili tayi tare da ware su ta furta "Ni fa tanbaya kawai nake ina ta iya abincin nan" Nazili ta fada tana tsare sultan da ido lumshe ido sultan yayi saboda kalaman Nazili na bata mashi rai sannan ya bud'e idanuwan shi ya sauke su kan Nazili da suka sauya launi cikin lokaci daya zuwa ja, yace, Nazili! Shuru Nazili tayi tana kallan Nihal dake kallan ta Sannan ta kara jefawa Nihal da tanbaya da cewa, "dama gidan almajirai ana abinci? murmushin da yafi kuka ciwo Nihal ta saki, tare da kallan sultan tace, "almajirai suma suna rayuwane kamar yadda mutane ke rayuwar su, kamar yadda ma'aikata ke zuwa aiki haka suma suka dauki almajiranci kamar yadda kike samun gata gaban yan'uwan ki suma haka almajirai suke samu, suna rayuwa cikin jin dadi da walwala kamar yadda kowa yake yi, da almajirai da masu wadata duk daya suke a wajan Allah , Allah baya duba gatan da mutum ya samu ko daula da yake ciki da zuciya yake anfani, haka suma almajiran suna samun kyakyawar rayuwa tun da gashi nima na samu har na auri sultan kuma a haka ya ganni yake so,! Nihal ta ida zancan tana kallan fuskar sultan tana tsoran karya watsa ta, shima din sultan kallan ta yake yana hadiye-hadiye sannan yayi murmushi yana kallan Nazili Wanda ta canza lokaci daya kamar tayi kuka, maganar da Nihal tayima Nazili ammi taji dadin ta sosai shuru Nihal tayi tare da numfasawa ta cigaba da cin abincin ta, daura hannu shi Sultan yayi saman na Nihal tare da rike shi sosai, shi kan shi be san yana aikata hakan ba ture plate din gabanta Nazili tayi tare da cewa, "se da safen ku" ta bar dining area zuciyar ta a dagule da takaicin yadda sultan ke nunawa Nihal so ko a gaban waye tasan ba komai ke dibar shiba se Kyan fuskar ta, ta dau Alwashin se ya wayi gari ta kona fuskar ze dawo hayacin shi mtsww cikin zafi rai Nazili ta fada a fili, "tallaka kawai,! bayan ankamala dinner kowa ya wuce part din shi.