Sashe 57
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Ammar ko bayan sultan ya warware ya samu waziri a kan maganar shi da Basmal sosai waziri ya ji dadi shi da Adda musanman Adda wadda kullun addu'a ta kenan yau Allah ya cika mata burin ta, koda waziri yayi ma maimartaba magana yayi na'am sosai ya nuna farin cikin shi kuma dama can ya so a hada shi da Basmal lokaci da za'ayi bikin Sultan se Allah be nufa ba, a haka suka gama maganar su tare da tsaida rana biki nan da wata daya murna wajan Basmal da Ammar ba a magana, Ammar ya so ace ma sati aka sa kamar yadda akayi na sultan of coz ya matso ya ga Basmal a matsayin matar shi.
Bangaran karatun Nihal maida hankali take sosai bata wasa ita kanta aunty Biola tana mamaki kokari irin na Nihal komai ta mata nan da nan ta dauka ya zauna mata karatun se san barka haka na addini ba'a barta a baya ba, mom ko ta zage se koya mata girke-girke take kala-kala, kullun kara kyau take da fresh ga wani girma tada kara komai na jikin ta ya canza ya kara girma, ta zama da's da ita, ita kanta tana mamaki kanta kamar ba Nihal yar talla ba.
Yauma kamar kullun bayan sun gama breakfast kasancewa yau weekend aunty Biola bata zo lesson ba, Nihal ce ke taya Dara kwashe kayan abinci da aka gama ci a dining suna kaiwa babba kitchen murmushi jakadiya tayi tana cewa, "Gimbiya ko gajiya bakiyi ya kamata ki je ki huta ba'a san Gimbiya da aikin wahala ba" Dara ta ida zancan tana aje warmer a zing, dariya Nihal tayi tana cewa, "wallahi umma idan kina ce min Gimbiya kunya nake ji dan Allah ki bari, damu da ku duk daya muke a wajan Allah bamu da wani banbanci" murmushi Dara tayi tana mai kara yaba natsuwa da hankali irin na Nihal tace, "toh Nihal diyar umma insha Allah zan daina kin ji" murmushi me nuni da farin cikin Nihal tayi tana taya Dara wanke plate din wanke-wanke kusan tare suka gama wanke-wanke sannan suka fara girki da sauran bayin, bud'e fridge Dara tayi ta ciro fruit tasa a boll zata wanke Nihal ta amshe tana cewa, "umma bari na taya ki gyarawa"
"Nihal baki gajiya da aiki kwata-kwata ya kamata ki rinka samun Hutu wannan aiki ai se mu" murmushi Nihal tayi tana mai cigaba da wanke fruits, Jakadiya ta cigaba da nunawa sauran ma'aikatan yadda zasuyi su kan su mamakin aikin Nihal suke yadda take sakin jiki da su kamar ba bayin ta ba, bayan Nihal ta gama gyarawa ta yanka tace , "umma na gama" murmushi Dara tayi tace, "madallah da kokari ki kai wa Ammi daga nan karki dawo ki huta , dan na lura so kike sultan ya dau mataki a kaina ina sa mashi Sultana aiki" turo baki Nihal tayi tana cewa, "kai umma kora ta kike ko ! Ta ida zancan tare da daukar boll din ta fita, murmushi jakadiya tayi tare da girgiza kai san Nihal na kara shiga ran ta , duk lokaci da tayi kokari matsawa kanta ta tuna ina ta san fuskar se ta wuni tana fama da ciwo kai a hankali ta furta Allah ka bayana min boyayyan almarin nan.
Direct bedroom din Ammi ta shiga koda ta shiga ammi na toilet saman stool ta aje boll din tana kokari fita idanuwan ta suka sauka kan Jakarta wadda ta leka daga karkashi gado wani irin dadi Nihal taji ta dad'e tana neman ta Ashe ammi ce ta aje mata, da sauri Nihal ta duka tare da zaro jakar tana murna bud'e jakar tayi tana duba abubuwan dake cikin ta lokacin yayi dai-dai da fitowar Ammi daga toilet, juyowa Nihal tayi tana murmushi tace, "Ammi dama ke kika aje min jakar nan kai amma na ji dadi, na dauka ta fadi shiyasa ko tanbayar ki bayi ba" murmushi ammi ta saki tana cewa, "Ai naga akwai abubuwa masu mahimmanci shiyasa na aje maki na so na baki tuntuni to mantawa nake" Murmushi Nihal ta kuma saki har fararan hakoran ta na bayana tare da cewa, "Ammi ga fruit ni da kaina na gyara maki idan kin gama ki sha magani ki na cikin drawer" harara Ammi ta makawa Nihal tana cewa, "toh ko shi mijin naki daya aiko ki se naga dama nake sha, wato shi yanzu ya daina matsamin ke kuma kin hau layi to ba zan sha ba na gaji," dariya Nihal tayi tana mai zama kusa da Ammi tace cikin sanyi murya, "Ammi please ki daure ki sha maganin ki kin ji, mu fatan mu ki samu lafiya ba komai ba kin ji kishiyar" Nihal ta ida zancan tana kashewa Ammi ido dundu ammi ta kaiwa Nihal ta kauce tana dariya ta fita da sauri.