← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 128

Sashe 34

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Gimbiya jalila ta bushe da ita tare da mik'ewa tsaye tana zagaye d'akin ta tace, " woooo!! Ke yakumbo shiyasa nake yin ki" Gimbiya jalila ta tsaya cak daga zagaye d'akin da take ta na cewa, "Aikin ki yana min dad'i yakumbo, Ni ko Gimbiya jalila mi zan ba yakumbo yau na kyautata mata kamar yadda ta faran ta min rai yau," murmushi yakumbo ta saki tana gyara tsayuwar ta, kanta a k'asa tace, "Ranki yadad'e bani da wani buri da ya wuce na faranta maki, na kasance yar gaban goshin ki, na kasance baiwar ki na dawama ina bauta maki ke da ya'yan ki" watsa hannuwa Gimbiya jalila tayi ta waigo tana kallan yakumbo wadda kanta ke k'asa har a lokaci tace, "Indai wannan ne yakumbo kin samu bani da mahalukin dake sani farin ciki kamar ke yakumbo, me zai hanani baki wannan matsayin ke ce fa kikamin albishir da cewa ga halin da Sultan ke ciki ko ze shiga hhhhhhhh, lalala! Idan ko Sultan ya mutu yau" Gimbiya tayi far da idanuwan ta tace, "Ni da kai na zan ya'taki yakumbo ! Murmushi yakumbo ta saki tana fari da idanuwan ta na farin ciki tace, "nasan ma wannan mulelan iccan da yasha a kai, ko be je lahira ba ze iya haukacewa hhhhh"
"Um hakan yayi kyau yakumbo anjima kije ki biya samarin da sukayi aikin kuma karki ci ko sisi idan kin dawo zan baki naki kasan .

Alex ne daure saman kujera an rufe mashi baki da fuska cikin wani d'aki me tarkace se mutsu-mutsu yake yana gunguni , dariya jabir ya saki yana kallan Ashad, murmushi Ashad yayi a hankali k'araso setin jabir cikin rad'a yace, "idan be bamu had'in kai ba ka kashe shi kawai idan ka gama aikin ka kudin ka na jiranka, ni zan wuce gida nasan yanzu duk halin da ake ciki gidan mu an fara zaman makokin" dariya jabir ya saki yana juya kwalbar giya dake hannu shi sannan Ashad ya dafa kafad'ar shi tare da sa hula alkyabba shi ya fita da sauri shi, bayin shi na take mashi bays zuciyar fes.

A hankali jabir ya k'arasa gaban Alex tare da cire mashi abinda ke fuskar shi, ware idanuwa Alex yayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mashi yana girgiza kai yana gunguni, gira jabir ya d'aga yana dariya yace, "kana mamaki ne ko Alex,? um karkayi mamaki Alex Dan ka ganeni wato kai ne kake hana ruwa gudu ko? Jibir ya ida zancan yana takewa Alex kafafuwan shi ihu Alex ya sa duk da ba'a jin ihu idanuwan shi na zubar da kwalla bakin ciki, ba komai ne ke sa Alex hawaye ba se saboda jabir na d'aya daga cikin yara Sultan dake bashi kariya San da suna Uk ko a lokaci Sultan yafi ji da shi a kan Alex saboda addinin su d'aya yaran su d'aya shiyasa a lokaci Sultan ya bashi waje na musanman, shi ko Alex kiris ta ne kuma bature ne basu fara shiri da Sultan ba se da suka zo Nigeria shima dalilin da yasa hakan Alex ne ya tura kanshi da karfi cikin zuciyar Sultan har ya koyi Hausa saboda shi wannan dalilin yasa ko sanda ze dawo Nigeria ya biyo shi gabaki d'aya, shi kuma jabir yace ze zauna a can idan Sultan ya dawo UK ya rink'a bashi kariya Ashe duk munafirci ne ya hanashi biyo su, jabir ne ya katsewa Alex tunanin ta hanyar k'ara taka mashi kafafuwa k'ara Alex ya saki, jabir yace, "tanbayar ka nake banza me Jan kunne, idan kana San kanka da mutunci ka had'a kayan ka, ka koma UK my gay," jabir ya ida zancan yana matsewa Alex fuska, cire mashi salataf d'in dake bakin shi Jabir yayi, yana saki Alex ya saki k'ara jini nabin bakin shi saboda dukan da yasha kafin a sumar da shi a kawo shi wajan, cikin murya kuka Alex yace, "Why jabir me yasa kake so kaga bayan Sultan mi yasa? Sultan be tab'a cutar da kai ba hasalima yafi sanka a kanmu mi yasa kuke muzgunawa RAYUWAR Sultan" Alex ya fad'a cikin d'aga murya, matse mashi baki jabir yayi yana cewa, "malam daina min ihu" yana maganar yana zubawa Alex Giya saman ida ya ji ciwo ihu Alex ya saki fuskar shi ta k'ara ja abinka da bature, jabir yace, "Dalla malam rufe min baki, ce maka nake ka fita harkar Sultan ka koma k'asar Ku tunda nan ba k'asar uban ka bace ko kuma na kashe ka, ko kuma kabi ra'ayina muga bayan Sultan shine magana banza," sauke ajiyar zuciya Alex yake kamar ze shid'e yace, "Never jabir Allah bazan cutar da Sultan ba se dai ka kashe ni," yana maganar yana kwance hannu shi ta baya da glass d'in da ke zube a wajan, taso mashi jabir yayi hannu shi dauke da bindiga ya seta Alex, k'undinbala Alex yayi, ya ida kwance kafar shi rigima suka Shiga yi tsaka nin su karya mashi hannu Alex yayi jabir ya saki ihu sannan ya amshe bidigar dake hannu jabir ya harbe shi a zuciya a nan jabir ya duk'e yana fitar da hawayan wahala Alex ya cigaba da Harbin shi yana kuka yana cewa, "I hate u jabir, I hate u" ya k'ara fad'a cikin calm tune, nan jabir ya fad'i matace, Alex yayi kwallo da shi yana cewa, "fuck u, son of a bitch" ya tofa mashi yawu ya ja k'afafu shi yana tafiya yana ganin jiri yana kashe yaran jabir har ya fito ya shige motar su ya bar dajin.

```Taku had kullun Salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*Page: 61_62*

Tuki yake sauti k'ira'a AlQur'ani na tashi yana a hankalin har ya iso shanono ji yake baya iya sauka masaukin shi se ya fara ganin Nihal ko ze samu natsuwa, tunda ya shigo cikin garin bugun zuciyar shi ke k'aruwa ya rasa dalilin hakan, a haka har ya k'arasa kofar gidan su Nihal kasancewa yasan duk halin da ake ciki yanzu ta gama talla faka motar shi yayi tare da fad'ad'a murmushin shi ya bud'e murfin mota, wani Almajiri ya hango cikin sanyi murya ya cema Almajirin ya kira mashi Nihal, aiko Almajirin ya shiga, gwoggo dake daka ce ta d'ago tana kallan Almajirin, Almajirin yace, "Ana sallah da Nihal," tsaida dakar gwoggo tayi baki sake tace, "wake Neman ta" Almajirin yace, wani d'an birni ne murmushi Gwoggo ta saki tace, "kace mashi ya shigo," Almajirin na fita gwoggo ta shige d'akin bak'i ta gyara shi sannan tayi sauri taje ta tada sara dake bacci tace, "ke tashi Dan uban ki alheri ya zo mana tunda ita tatafi ke se ki maida gurbin ta," mikewa Sara tayi zaune tana kallan gwoggo cikin rashin fahimta, gwoggo tace, " ki tashi mana ko se ya shigo ya ganki kaca-kaca,"
"gwoggo wai wa?
"Wannan d'an birnin nane fa ya zo neman Nihal tunda bata nan ke se ki maida gurbin ta, ki tafi birni ki huta" far da idanuwa sara tayi dama tunda ta kyala ido da rasuwar umma taga ammar ta mutu da san shi, da sauri ta duro daga kan gado ta shige toilet dan watsa ruwa, Ammar na shigowa gwoggo ta mashi iso har parlour b'aki tana murmushi zama yayi tare da gaishe ta har a lokacin yana mamakin sauyin gwoggo ruwa da sob'o ta aje mashi, amma kwata-kwata hankalin shi na kan kofar d'akin ko ze ga Nihal sanyi idanuwan shi amma shuru sunkunyar da kai k'asa yayi zuciyar shi na tsanan ta harba, Gwoggo ce ta katse mashi tunanin da sakin kukan munafirci tana kuka tana cewa, " ba komai bane yasa na ce ka shigo gida ba se saboda maganar da zamuyi bata fad'uwa a waje," ta ida zancan tare da share hawayan ta da bayan zani, zuciyar Ammar k'ara tsinkewa tayi ya tattaro hankalin shi kan gwoggo ta cigaba da cewa, "se dai muce Allah ya shiryi Nihal saboda bayan tafiyar ka, Nihal ta fetsare k'afafuwata, ta shiga bi maza har ta kai ga ankamata da kwarto a d'aki suna shek'e aya," gwoggo ta k'ara rushe wa da kuka ta cigaba cewa, "ko da baffa ya kamata dumu-dumu se da yanke jiki ya fad'i, ba'a nan ta tsaya ba Ashe tana dauke da juna biyu data lura mun gane se ta had'a kayan ta, ta gudu yau kimanin wata guda kenan bamu ga Nihal ba , ba irin neman da bamuyi mata ba, amma ina tafigewa taitabin maza" zuciyar Ammar ce ke harbawa, zuciyar na fad'a mashi k'arya ne ya za'ayi Nihal ta aika ta haka yariyar da ko ida girma batayi ba, gwoggo ce ta katse mashi tunani da cewa, "sai dai ka nemi yar'uwar ta sara shi kad'ai ne adalacin da zamuyi maka, Nihal kuwa ta riga da ta cuceka se dai ka barta da Allah" gwoggo ta ida zancan tana kuka kamar gaska, ta fice

lumshe idanuwa Ammar yayi wasu hawaye na zubu mashi wato se dai suka ga bayan Nihal yanzu ina ze shiga Neman ta a duniya gashi bashi hotan ta ko d'aya.

Dariya gwoggo ta saki tana fita tare da cewa sara tayi sauri ta sami Ammar a d'akin baki aiko ta shirya cikin shada yellow ansha hoda kamar ta shiga cikin gari, ga uban jan baki kamar akuya taci dusa, sallama Sara ce ta katsewa Ammar tunani da sauri ya goge hawayan shi saboda ko tashi ya kasa yi bin sara yake da kallo Dan kusan tsoro ta bashi, washe mashi hakora tayi. Ji yayi kamar ya ranta ana kere da kyar ya tattaro natsuwar shi tare da daukar car key d'in shi ya aje masu bandil d'in dubu d'aya tare da watsawa sara harara yace, "ga abin kuke so nan na aje maku, "insha Allah Nihal tana hannu na gari mtsww" sannan Ammar ya sa kai ya fice ya bar sara sake da maki tana jujuya kud'in da Ammar ya aje masu.
Chapter 34 · 0% Book details