← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 128

Sashe 59

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yauma kamar kullun Nihal na zaune tana karatun exam dan yanzu karatun ya zamar bata jiki, dan bata so ta fadi jarabawa, murda kofar da akayine ya sata juyowa, sultan ne sanye cikin milk night dressing din shi wando da riga mai dogwan hannu, kallo daya Nihal ta mashi tare da kauda kanta tana bita karatun ta, drewar sultan ya bud'e tare da ciro wasu kaya dake cikin Leda a hankali ya tako gaban Nihal ya tsaya tare da aje ledar saman sofa dagowa Nihal tayi karaf suka had'a ido da sultan cikin honey voice din shi Sultan yace, "ki shirya gobe da safe zanyi dropping naki a school, insha Allah gobe zaki fara exam, zaku fara da English and basic technology ga uniform din da zaki saka komai na gama hadawa" har sultan ya kai aya Nihal na kallan shi wani irin dadi ya lulube ta ko ba komai gobe zata fita tasha iska dama ta gaji da zama waje daya, maganar da Sultan yayi ne ya dawo da Nihal daga duniyar tunani tsare ta da ido Sultan yayi tare da had'e rai yana cewa, "saura kuma idan kinje karkiyi kokarin ki dage ki ci exam's din idan har kika fadi bazan cigaba da biyan kudi na ba ana maki lesson mara anfani ba," wani irin kallo Nihal ta watsa ma Sultan tare da cewa, "Ni kuma idan naci bazan cigaba da zama ana min lesson ni kad'ai ba! se dai ka kaini makaranta nayi karatu kamar yadda kowa keyi idan ba haka ba, zan fadawa Ammi irin zaman da muke! shawara ta rage naka" Nihal ta ida zancan tana daukar littatafan ta dake saman sofa zata raba ta gefan sultan ta wuce fisgo ta Sultan yayi Nihal ta fada saman fafad'an kirjin sultan kallan juna suka shigayi mai cike da sakwanni mutsu-mutsu Nihal ta fara tana neman kwace kanta tana kallan Sultan fuskar ta daure, can kasan makoshi sultan yace, "Ai dama duk abinda zan maki ina yinshi ne saboda Ammi ba saboda ke ba, amma ki sani baki isa ki sani nayi abinda banyi niya ba, kuma dama kin aure nine saboda kin san cewa Ammi ce weakness dina! murmushi Sultan ya saki tare da cigaba da cewa, "hakan da kikayi is good, amma ki sani baza ki taba cin galaba a kaina ba" ya ida zancan yana kara matsewa Nihal hannu ta, da karfi Nihal ta fisge hannun ta har tana tafiya taga-taga zata fadi Sultan ya taro ta fadawa tayi saman fafadan kirjin sultan da karfi Nihal ta ture Sultan tana cewa, "Ai nima ina zaune da kai ne saboda Ammi kuma har yanzu ina jiran ranar da zaka bani takadata ma'ana ranar da zaka sakeni! saboda bana jin zan iya zama da mutumin da bana so baya sona! har karshan rayuwata kuma ida har baza kamin abinda nake so ba Sultan ni kuma se na fadawa Ammi irin zaman da muke,! Nihal ta ida zancan tana tsare Sultan da ido shima din kallan ta yake kamar yadda take kallan shi idanuwa waje kokarin rabawa Nihal tayi ta gefan sultan zata wuce kara fisgo ta Sultan yayi ya wurgata saman sofa saboda kalaman Nihal sun fara bata mashi rai har ita zata ce tana zaune da shi ne saboda Ammi, zaro ido Nihal tayi waje tare da kara shigewa jikin sofa dan wannan karan Sultan ya bata tsoro, cikin kakausar murya Sultan yace, "toh miyasa da aka tashi yin auran bakin fada wa Ammi baki so na ba,? se kikayi shuru da bakin ki saboda kin ga daula oh what? karki manta fa nasan mi yasa kika aure ni kin aure nine saboda kiyi ruining life dina do you think ban sani bane let me tell you something duk abinda za kiyi karki kuskura ki bari Ammi na ta shiga wani hali Nihal if not! Wani malalacin murmushi Nihal ta saki na rainin hankali tace, " Ni ban ce ana ruining life dina ba, daga taimako na zama matar ka ba tare da sanin family dina ba! an fada mana cewa ni shegiya ce ko bani da asali ne, se kai ne zaka ce ina ruining life naka da ni da kai wake ruining life din wani? me yasa baka fadawa Ammi baka iya zama da almajira a matsayin mata ba bari kaji Sultan kamar yadda baka so na nima haka bana sanka,! na san cewa auran nan kayi shine saboda Ammi idan har baka so Ammi ta shiga wani hali dole kayi min abinda nake so, maganar daula ko what ever karkayi tunanin kudin ka na dadani da kasa sultan ko daya kuma daga yau karka kara kashe min ko sisi cikin kudin ka! Maganar da Nihal keyi ma sultan ba karamin soya mashi zuciya take ba musanman idan ta furta bata san shi kamar yadda baya san ta, juya mata baya Sultan yayi zuciyar shi na kuna tana tafarfasa kamar zata fito waje saboda bacin rai juyowa ya kumayi lokacin idanuwa shi sun rine zuwa ja ya nuna Nihal da dan yatsa tare da sauke hannuwa shi ya fice da sauri daga dakin ya banko mata kofa da karfi kamar ze cire, lumshe ido Nihal tayi tare da dafe goshi tana sauke numfashi

***********

bangaran minal da nawwara kannan sultan dake boarding school suma shirye-shiryen exam suke, kasancewar suma JSCE zasu zana murna wajan su ba'a magana dan sun matsu su gama exam su dawo gidan Hutu, musanman da suka ji cewa suna dawowa za'a fara bikin Basmal, minal ce dake kwance saman bed kasancewar dakuna hostel din mutum uku-uku ne daya ke makarantar ta ya'ya manya ce murmushi Minal ta saki tana cewa, "Nawwara na matsu naga mun gama exam's din nan mu koma gida, gaskiya this time around baza mu dawo boarding ba duk wani biki da suna wuce ka yakeyi haka akayi bikin yaya Sultan muna school har yanzu bamu San matar ba" Nawara dake duba littatafan ta ce ta dago tare da gyara zaman glass din ta dake manne a idan ta tana cewa, "I miss home so much minal kema kinyi magana this time around zamu matsa ma Abba ya barmu a gidan tunda mun zama yan'mata, ya kamata ace ko wani biki muna zuwa" shukura dake gefe dariya suka saki ita da minal ita kanta nawwara dariya ta saki suka kara kwashewa dariya sannan kowa ya cigaba da duba littafin shi.

*WASHE GARI*

Kiran Sallah Asuba ne ya tashi Nihal dauke da addu'a a bakin ta, ta mike zaune tana waige-waige a hankali ta sauke idanuwan ta saman bed din Sultan ganin baya saman bed din, yasa Nihal tuna rigiwar da sukayi jiya barbaza gashin kanta Nihal tayi tare furta "am so stupid yesterday! Jikin Nihal ne yayi sanyi a hankali ta zame blanket din jikin ta Nihal, ta nufi bakin kofa, a hankali ta kama handle din kofar ta murd'a tare da tura kanta parlour tana waige-waige kwance saman three star ta hango sultan ya kudindi ne cikin blanket gyara gashin kanta Nihal tayi a hankali take takawa har ta karaso bakin kujera tana leka fuskar sultan, motsin da Sultan ya ji a kanshi ne yasa sultan fisgo Nihal da karfi ta fada jikin shi tare da aza mata wuka a wuya zaro ido Nihal tayi tana kallan Sultan da idanuwan shi ke a rufe, a hankali Sultan ya bud'e lumsasun idanuwan shi ya sauke su saman kyakyawar fuskar Nihal yana bin ta da kallo tare da janye wukar daya kafa mata a makoshi, cike da tsiwa Nihal tace, "oh my goodness sultan kiyayar da kake min har ya kai ka fara kokarin kashe ni, what wrong with you Sultan? juyawa Sultan baya Nihal tayi tana yan'kame kame tana kakabe kujeri tana satar kallan Sultan shima har a lokaci idanuwan shi na kan Nihal juyowa Nihal tayi tana cewa, "um ya kamata ka tashi ina so na share parlour kafin mu fita bana so lokaci ya kure min" Nihal ta ida zancan tana wasa da yatsun hannun ta, kallan agogan dake manne jikin bango parlour sultan yayi kusan 5:00pm sannan ya kalli Nihal tare da kara kallan agogan itama kallan agogan tayi tare da juyowa karfa suka hada ido da Sultan wayancewa Nihal tayi tana cewa, "ka tashi mana" zuba mata sexy eye's ball din shi Sultan yayi tare da cewa, "ki bari kiyi sallah mana first se kiyi duk abinda zakiyi" juyawa Sultan baya Nihal tayi tare da cije lips tana cewa, "Allah yasa karya gane kallan shi nake ya rai nani, to mima ya sani fitowa oh pah," da sauri Nihal ta bar parlour ta maida kofar dakin ta rufe jingina Nihal tayi da kofa tana maida numfashin turo kofar da taji anayi ne ya sata zabura da sauri ta bar jiki kofar sultan ne ya shigo rike da pillow da blanket kallan Nihal din yake da alamar tuhuma sannan ya aje blanket din hannu shi saman bed yana kokarin shiga toilet da gudu Nihal ta karasa tana cewa, "aaah!!! Birki Sultan yaci yana kallan ta rabawa Nihal tayi ta gefen sultan ta shige toilet ta maida kofa ta kule dan siririn saki Sultan ya ja yana cewa, "wannan yariyar ta fara rai nani da yawa se na koya mata hankali mtsww" sannan ya fice daga part din gabaki daya Nihal na bakin kofa tana jin fitar Sultan , ta fito daure da alwala ta gabar da sallah.
Chapter 59 · 0% Book details