Sashe 5
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da Lantana ta bar duniya Larai ke kula da Tanimu da ƴa-ƴa ta bata gwada masu ban-banci komai tare take masu da ƴa'ƴan ta, sai dai Tanimu yasa ma ranshi baƙin hali Don gani ma yake kamar baƙin cikin Larai ne ya kashe masa mahaifiya, shiyasa kullum a ƙullace yake da ita, gashi bugu da ƙari Habu ya fishi komai tun daga ladabi da biyaya da iya zama da mutane, shiyasa malam yake nuna mai so ba Wai Dan baya San Tanimu ba, sai dan ya gyara halaiyar shi, hakan sai ya dasawa tanimu hassada a zuciyar shi da baƙin ciki gami da kyashin ɗan uwansa Habu.
Bayan wasu ƴan watan ni ma, inna ƙara samun wani cikin tayi tasha wahala sosai sannan ta haifi ƴa mace tun daga nan bata ƙara samun wani cikin ba, saboda wahalar data sha.
*Bayan Shekara Goma (10)*
"Yanzu saboda Allah Tanimu abinda kake kana kyautawa? Malam ya cigaba da cewa,
"kai kaƙi boko saboda Wai baka iya zarya daga shanono zuwa ƙauyen nan, sannan ƴar nomar ma baka iyawa har sai Habu ya dawo sannan shi zaiyi ta kai kana can kana yawon banza wannan ba rayuwa bace tashi ka ban guri," malam ya faɗa cikin tsawa.
Tanimu kansa dake duƙe gaban malam ne ya miƙe yana gunguni yana cewa, cikin gunguni, "tun da su uwar na da rai ai dole a fifita su akai na."
Inna dake bakin rijiya ce tace, "mikake cewa,? Tanimu Wai kai me yasa baza kayi hankali ba kullun in malam nama faɗa sai kaita magana kasa ƙasa bayan nace maku yin hakan tamkar zagi ne kake ma iyayan ka"
ko saurarata beyi ba yana huci ya fita.
Inna tace, "Allah ya shirya min kai Tanimu, sannan yaji kan Yaya".
Yana fita yaci karo da Habu ya dawo daga makaranta janye da kekyan shi, murmushi Habu ya saki yace, "Yaya"
Ɗaure fuska tanimu yayi yana ji kamar ya kashe shi, "shi Wai mai tarbiya Ai wallahi wata rana shi da kanshi zai ga bayan shi" maganar da Habu yayi ne ya katse mai tunanin da cewa, "dama Yaya dazu ne muka haɗu da malam Barau, rediyon sa ta lalace shi ne nace ya bani na gwada, ko zan iya gyara mai tun da ana koya mana sana'oi a makaranta, aiko ina kwancewa na gyara ta gyaru, shine ya ban narai hamsin."
Tanimu ne ya ƙara hade rai a karo na biyu tare da nuna hassada shi yace, "to sai akayi yaya Dan ya baka hamsin.?
"Dama hamsin ɗin zan baka, ka ɗau talatin ka bani ashirin tunda kai Babba ne" washe baki Tanimu yayi yace, "kai amma nagode ina ma laifin ka bar min hamsin ɗin tunda na fika buƙatar kuɗi"
Murmushi Habu yayi mai nuni da jin daɗi shi yace, "ka ɗauka yaya na baka" sannan ya shige gida bai tsaya saurara godiyar da Tanimu Ke mai ba.
Ɗauke da sallama ya shigo a bakin shi malam da inna na zaune a tabarma har ƙasa ya duƙa ya gaishe su sannan ya shige ɗakin su, ya cire uniform ɗin shi ya fito ɗauke da kayan zuwa gona, murmushi malam yayi yace, "haba malam Habu daga dawowa ba hutawa bare cin abinci zaka tafi gona, dawo ka zauna ka huta zuwa yamma ka je,"
ba musu ya dawo ya zauna inna ta zubu mai tuwo da miya ya ci ya sha ruwa yana ƙoƙarin miƙewa ne su Hassan suka shigo da gudu gida, tare da ƴar ƙanwar su Haulatu da alama daga makarantar allo suke.
Idi ne zaune da Tanimu saman tabirin mai shayi, Idi yace, "gaskiya Tanimu kayi ma kanka faɗa, na lura habu so yake ya ƙwace girman ka ya zama nashi, tun wuri ka tashi tsaye, in ba haka ba ka sha mamaki, nan gaba gonar malam sai ta zama tashi indai kana zuba ido, gashi har shanono yake zuwa makarantar ya hudawa"
wani bakin ciki ne Tanimu ya hadiye yace, "in dai ina numfashi a duniya zaka ga yadda zan mai da Habu sai ya zama marar anfani daga shi har ƴan uwan nasa da yake taƙama da su".
"ai ɗan kishiyar uwa ba ɗan uwa bane" inji Idi ya idar da zancan yana afa ƙuli a bakin shi.
```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo ```✍🏻
[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑
*Edit by*:
*Aliyu miko Muhammad*
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest ```)
https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-17394973194167/?refid=52&red=opera-speed-dial&-tn_-H-R
*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com
*Page: 11_12*
Yau ma kamar kullum Habu tunda safe ya tashi kasancewa yau ma yana da makaranta gashi dama sune manya a makaranta wato aji shida, kallon yaya Tanimu yayi dake ta sharar bacci har zanin da yake rufa da shi ya yaye janyo zanin yayi tare ficewa daga ɗakin ya rufo masa ƙofa.
Kai tsaye ɗakin Inna ya wuce zaune ya tarar da ita da alamu tasbihi take, tsugunawa yayi har ƙasa ya gai sheta, amsawa tayi cike da fara'a, sannan ta janyo damammiyar fura dake ƙarƙashin gado ta miƙamai, kusan a tsatsaye ya karya sannan ya mata sallama ya ɗau kekyan shi sai shanono.
Lamarin Tanimu ko Habu na fita, ya miƙe ya wuce Gona saboda tunda Idi ya bashi shawarar jiya ya daina wasa da zuwa gona da kiwo, dan shi bai ga dalilin da Habu zaiyi babakere a gonar mahaifin su ba.
Ko da Habu ya isa makaranta aji ya wuce, be wani daɗe ba malamin su na lissafi ya shigo, ya fara darasi tunda ya fara darasi Habu ne ke bashi amsa, a gaskiya Habu ba ƙaramin mai hazaƙa bane, shiyasa ko malamin makarantar naji da shi ko wata gasa za'ayi a birni da habu ake zuwa, har ya lashe kambun gasa, hakan yasa kowa ganin girman shi yake, gashi bugu da ƙari ga fasaha gyara a bubuwan ƙarafuna.
Akwana a tashi ba wuya wajan Allah, yau dai su Habu sun kammala karatun su na secondary, inda aka haɗa kwarya-kwarya walima haɗe malamai, inda Habu ya amshi kyaututtuka sosai a matsayin shi na dalibi mai hazaƙa, hatta Malam sai da ya samu tashi kyautar a matsayin shi na mahaifin Habu, haka suka baro shanono cike da ɗunbin farin ciki.
Suna isowa gida Habu ya shiga nunawawa Inna kyaututtukan da ya samu, albarka ta cigaba da Samai da fatan samun cigaba.
Sallamar Tanimu ce ta katse masu zance, cikin murna da sauri Habu ya tari tanimu yana nunamashi kyaututukan daya samu, wani ɗan abu ne ya janyo yana nunawa Tanimu Wanda yafi kowacce kyauta soyuwa a gareshi, gabaki ɗaya abun zagaye yake da kwalba yana sheki, ganin yadda Habu ke tattalin abun da ririta shi yasa Tanimu shu'umin murmushi, yana ayyana yadda zai watsa abun amsar abun yayi yace, "kai Habu amma dai wannan Abu da kyau yake,"
Murmushi Habu yayi yace, "shiyasa duk nafi sonshi, ba komai ke birgeni da shi ba sai wannan kwalbar da kyal kyalin da yake ciki, da yanayin yadda aka tsara rubutun dake cikin sa."
Murmushi Tanimu yayi gami da kallon Habu da gefan ido, kawai ya saki hannu sa kamar cikin rashin sani glass din ya tarwatse, rausaya kai Tanimu yayi tare da saurin duƙawa yana kallon Habu da gefan ido yace, "wayyo Allah Habu nama ɓarna," Habu dake tsaye sai da yaji babu dadi duƙuwa yayi yana kallon glass ɗin, ganin yadda tanimu duk yabi ya ruɗe ne ya sasa tausayawa ɗan uwan nasa saboda wani abu dabam sai tadawa kanshi hankali yake sannan yace, "haba yaya sai wani tada hankalin ka kakeyi saboda ɗan wannan abun ya fashe karma ka damu kan ka, tsautsayine kuma yana faɗawa kan kowa."
Ko inna?
Inna da fitowar ta yanzu tace, " aiko dai, Tanimu ka zo ka zauna ka ci abincin ka, kabar tada hankalin ka, tun ɗazu ma nayi ma kwaɗan zogale nasan kana so" murmushi na gefan baki Tanimu yayi tare da ƙara taka glass ɗin ya wuce ɗakin Inna.
Duƙawa Habu yayi yana kallon glass ɗin har ga Allah yana son abun amma ya zaiyi tunda ya tashi aiko Gaba ki daya, tsintsiya ya dauko ya share gurin tsaf, sannan ya kai sauran kyaututtukan ɗakin Inna.
Tunda Habu ya gama makaranta ya koma gona yana aiki sosai, wata rana Tanimu shi yake bari da aikin.
Kasancewar yana da sha'awar gyara gyaran kayan wuta sai ya zama na da ya dawo daga gona sai ya wuce gurin malam bala mai gyaran rediyo da keke, tunda habu ya fara zuwa ya fara aiki albarka ke sauka a wurin gashi komai nashi cikin zamani da boko yakeyi saboda yayi makaranta so duk wata waya yasan sunata shiyasa yake cin ribar aikin.
Kafin kace mi sunan Habu ya fara canzawa, an fara Kiran shi da habu injiniya saboda ƙwarewar shi wajen iya gyara ridiyo da keke.
```Taku har kullun Salma Mas'ud Nadabo`[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo*👑
*Edit by*:
*Aliyu Miko Muhammad*
🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the best```)

*Email* [email protected]

*Page: 13_14*
Kamar kullum yauma suna gona duk sun haɗa zufa sun gaji, bakin wata bishiyar mangworo suka yaɗa zango suna hutawa, Tanimu na gefe yana ɓallar rake, wasu ƴan matane su biyu kowace ɗauke da talla, suka nufo gurin kallo ɗaya zaka masu kasan basu da tsinki, musanman ƴar farar wadda da alama mai ta shafa tayi haske saboda kafar ta baƙin ƙirin take fuskar ta fara, bakin nan ya sha jan baki ana tafe ana taunar ciwing gum, sai da suka zo bakin bishirya sannan ido tayi wata tsayuwar ƴan talla tana fashe kwai tana cewa, "zaku sai gyaɗa" tana faɗa tana fari da ido tana karkarye karye, kau da kai Habu yayi saboda shi kwata kwata mata masu irin wannan dabi'ar ba burge shi sukeyi ba.
Tanimu ko duk ruɗewa yayi yana bin ido da idanuwa, dan shi bai taɓa ganin macen da ta kwanta mai a rai ba kamar ido ba, murmushi Tanimu ya saki tare da cewa.