Sashe 83
Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hall din dinner ya cika makil da yan'uwa da abokan arziki MC se zubu yake yanayi ma yan'uwa da abokan arziki sannu da zuwa, Amarya da ango tuni sun halara Ammar ya sha kyau har ya gaji yana sanye cikin brown shadda malin-malin tasha aiki da dark brown zare Basmal tasha kyau cikin red material da head red tasha kyau har ta gaji rigar se jan kasa take kallo daya zaka masu kasan sun dace da juna se smile suke sakarwa juna su mai cike da su da kauna, cikin sanyin murya Basmal tace ma Ammar, "har yanzu yayana da aunty Nihal basu zo ba Allah yasa lafiya" murmushi Ammar yayi yana cewa, "Rabin rai na suna kan hanya nasani kin ji" daga mashi kai Basmal tayi tana smile, Dr Amir ma ya zo tare da matar shi fatima Dr bello ma ya zo da matar Bilkisu biki dai se bidiri ake minal da nawwara sun zo se zuba rawar kai ake Nazili ma ta zo tana sanye cikin ashoben ta tasha kyau har ta gaji amma rashin ganin sultan ya sosa mata zuciya saboda tasan baya wuce yana wajan Nihal, irin yadda MC ya shiga wasa Nihal da sultan ne yasa gabaki daya hankalin mutane ya koma kan Nihal da sultan mutane se yaba kyan su suke da haduwa wasu mata har cewa suke dama su, a tunanin MC amarya da ango biyu ne a bikin shiyasa ya zage yana ta koda Nihal da sultan dake takawo se smile sultan yake tunda suka taho yake makale da Nihal, Nihal ko kunya duk ta ishe ta duk yadda taso sultan ya sake ta amma yaki itama murmushi yake kawai take, Nazili dake zaune mikewa tsaye tayi ta kafe Nihal da ido kallan kayan jikin Nihal din kawai take kishi ya rufe ta a fusace ta dau fost din ta zata fice, rike mata hannu da akayi ne yasa ta tsayawa cak a fusace Nazili ta dago Nihal ce ta rik'e mata hannu tana murmushi matsowa kusa da Nazili tayi cikin rada tace, "karkiyi tunanin bangane ke kika kona min kaya ba, saboda baki san gani almajira wajan dinner, kamar yadda kike fada kuma matar sultan, ina mai baki shawara kada ki kuskara sauran mutuncin dake tsakanin mu ya zube Nazili" matsowa Nihal ta kuma yi dai-dai setin kunna Nazili tace, "nasan cewa kina mamakin ina na samu kayan dake jiki na, anyway sultan ne ya dinka min saboda yana san farin cikin almajira...! kwace hannu ta Nazili tayi idanuwan ta a kankance tace, "what do you mean by tell me this nonsense Nihal, how dare you..! nuna Nihal da yatsa Nazili tayi sannan ta kad'a kai tace, "kinyi na farko kinyi na karshe, you must pay for this rubbish you have done to me Nihal" rike dan yatsan Nazili Nihal tayi tana cewa, "karki kara nunani da yatsa if not am gonna teach you a lesson, kuma ina so ki sani cewa sultan nawa ne ni kad'ai, sultan na almajira Nihal ne a haka ya gani kuma yake so I hope you get me right..! Nihal ta ida zancan tare da matsawa jikin sultan tana shumin murmushi idanuwan Nazili cikowa sukayi da kwalla tana kallan yadda sultan ya zagaye hannun shi a waist din Nihal, da sauri Nazili ta juya baya hawayan bakin ciki na bin kunci ta cikin zuciyar ta tana cewa, "Nihal you must pay, how dare you zaki sani kuka how..! da sauri ta bar hall din ko ganin gaban ta batayi, fadawa saman fafadan kirjin Alex da Nazili tayi ne ya sata tsayawa cak tare da rushewa da kuka, Alex dayake kokarin shigowa hall tsayawa yayi zuciyar shi na tsana ta harbawa da kyar ya iya banbare Nazili daga jikin shi yana cewa, "Gimbiya miya same ki..? ko saurara shi Nazili ba tayi ba ta ruga da gudu ta shige mota da sauri Alex ya bi ta a baya, amma ina ta figi mota cikin hight speed ta bar harabar wajan rike kugu Alex yayi tare furzar da iska me zafi juyowa Alex yayi ya dukawa ya dauki fost din da Nazili ta yadda a kasa yana kalla sannan ya maida ta ciki mota cike da mamakin yana yin daya ganta duk se be ji dadin hakan ba, har wata zuciyar na cewa ya bita.
hoto dai Nihal da sultan sun shashi kamar dinner bikin su Minal da nawwara ban da yaba kyan Nihal ba abinda suke, matan abokan Sultan se nan suke da Nihal, Nihal ko ta saki jiki da su ana hira har tanbaya suke yaushe sultan ze kawo masu ita, ansha dinner an cashe anyi ciye-ciye da lashe-lashe naira tayi kuka har ta raina kanta dinner tayi kowa ya gwangwaje a haka taro ya watse ana fatan Allah ya maimaita.
Washe gari ta kama ranar daurin aure a ranar ne misalin karfe 2:00pm na Asabar dinbin mutane suka sheda daurin auran *AMMAR MUSA WAZIRI DA MATAR SHI BASMAL UMAR MATAWA SARKIN KANO* manya-mayan kosushin gwabnati sun halari daurin auran da manyan yan'kasuwa da sarakuna na garuruwa daban-daban a nan ne hango ango sanye da fara shadda malin-malin shi da sultan sun sha kyau har sun gaji se murmushi suke saki suna mika gaisuwa ana masu kirari da bushe-bushe suna ta ruwan kudi da friends din su kowa ya gansu yasan cewa yau ranar farin ciki ce.
Cikin gida ma ya kacame anata busa algaita Amarya na sanye cikin had'adan lace din ta Ash da ratsin pink tasha silver alkyaba tasha aiki da gold zare can na hango Nihal sanye da lace milk me ratsin blue a jiki, dinkin ya kama jikin ta sosai se hada-hada take busar daka fara ne ze sheda maka angwaye sun shigo, busa karu tayi a gidan har angwaye suka shigo main parlour suna ta kwasar gaisuwa ana hotuna, Nihal ce dauke da wasu kaya zata wuce da su dakin Amarya sultan ta gani bakin kofa kallo daya ta mashi ta kauda kai tana kokarin wucewa amma sultan ya tare mata hanya matsawa tayi sultan ya kara tare ta matsowa sultan yayi kusa da ita dai-dai setin kunnan Nihal kamar me rad'a yace, "kin yi kyau my dear kamar na sace ki" kiri Nihal tayi tana kallan sultan tana kokarin tantance maganar daga bakin shi ta fito harara Nihal ta maka mashi can kasan makoshi tana cewa, "ai dama ni din mai kyau ce, se yau ka fara gani kyan nawa, ka fara matsamin fa" Nihal ta idan zan tana tsare sultan da ido kokarin rabawa tayi ta gefan sultan ta wuce fisgo ta sultan yayi ta fada saman fafadan kirjin shi zaro ido waje Nihal tayi tana cewa, "sultan cikin mutane fa muke baka ganinene, wai mi yasa kake min haka ne" Nihal ta ida zancan tana waige-waige sakar mata kiss sultan yayi a kumatu zaro ido Nihal tayi tare da ture sultan ta bar wajan da sauri tana waigen sultan, alamarin sultan yanzu ya fara ba Nihal tsoro Nazili dake tsaye bayan sultan duk abinda ya faru a idanuwan ta ya faru hadiyar zuciya ne kawai ba tayi ba saboda takaici, tare da kudirtawa zuciyar yadda zata bulowa Nihal.