← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 128

Sashe 79

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallan sultan Nihal take zuciyar ta na tsana ta bugawa fatan ta daya kar sultan ya gano ko ita wacece, murmushi Nihal tayi tare da janye hannun sultan zata rufe bedside drewar duk da tsoran dake ziyartar zuciyar ta dama wannan sauyin na shi ba karamin daure mata kai yake ba Allah yasa ba damar tona mata asirri ya samu ba, tsare ta da ido sultan yayi tare da cewa, "ya kamata ki bani hotan nima nasan mother in low na da father in low na saboda yanzu mun zama daya iyayan ki kamar nawa suke duk da basu raye zan so na san su," jikin Nihal mugun sanyi yayi amma hakan be hanata bud'e baki tace tare da nad'e hannunwan ta a kirji tana cewa, "Bana tunanin almajirai zasu zama iyayan ka babu wani anfani kallan hotan iyaye na" matsowa sultan yayi kusa da Nihal dan ja tayi da baya zuba hannuwan shi sultan yayi cikin aljihu ya tsare Nihal da ido kauda kai Nihal tayi tana kallan gefe tana kokarin boye hawayan dake kokarin zubo mata saboda karyar da ta zauna tayi ma iyayan ta, juyo da fuskar ta sultan yayi tare da sa dan yatsan sa ya dangwalo hawayan Nihal cikin honey voice din shi sultan yace, "duk bani hotan ne ya janyo kukan gani nayi tunda ina auran diyar su ya kamata na san su ko a hoto ne," sultan ya ida zancan yana kallan Nihal dake kallan shi kauda kai Nihal tayi tare nufar drewar a hankali ta bud'e drewar ta ciro hotan ta mikawa sultan, amsa sultan yayi yana kallan hotan murmushi sultan ya saki tare da cewa, "Ashe Nihal da umma take kama" zama Nihal tayi bakin gado tana murmushi mai had'e da kuka Allah ya gani tayi missing iyayan ta a hankali sultan ya karaso bakin gadan ya zauna janyo Nihal yayi jikin shi daura kanta tayi saman kafadar sultan tare da fashewa da kuka shafa gashin kanta sultan yake cikin sanyi murya yace, "Nihal ki daina zubar da hawayan ki Nihal, kuka baya maki kyau duk abinda ya dame ki addu'a ce maganin damuwar ki, kuka baya yaye matsala" ya ida zancan tare da dago da fuskar ta suna facing juna kuka Nihal ta kuma saki tare da cewa, "ina missing umma da Abba Nihal bata da kowa ko kanne bani da su bani da yaya ni kad'ai ce, bani da wanda zan fadawa damuwa ta rayuwar maraya bata da dadi" daura finger din shi sultan yayi saman lips din Nihal shuru Nihal tayi tana bin sultan da idanuwan ta wayanda suka rine zuwa ja, sultan ya katse mata tunani da cewa, "baki da yaya sama da sultan kannan sultan kannan ki, ko bakya so? sultan ya ida zancan yana tsare Nihal da ido murmushi Nihal ta saki tana cewa, "ina so" murmushi sultan ya saki tare da mika mata hannu yace, "friends..! Murmushi Nihal ta saki tana kallan hannun sultan a hankali ta daura nata tana cewa, "friends..! hannu sultan yasa yana gogewa Nihal hawayan ta daukar hotan sultan yayi tare da kara shi a fuskar Nihal yana cewa, "da gaske fa Nihal da umma take kama" murmushi Nihal ta saki kallan ta sultan yayi ganin yadda taji dadi, sultan cigaba da cewa yayi "Umma Nihal na missing naki" yadda sultan yayi maganar cikin sigar shagwaba kamar a gaban umma yake dariya Nihal ta shiga yi tsayawa sultan yayi yana kallan Nihal yadda take sakin dariya yana jin dadin hakan ko ba komai ya fara dasawa Nihal farin ciki a rayuwar ta insha Allah Ammar se yayi alfahari da shi, ganin kallan da sultan ke mata ne yasa Nihal daga mashi gira murmushi sultan yayi sannan ya ciro car key a aljihu shi ya kama hannun Nihal ya samata a hannun yana cewa, "Abba ne yace a baki" bud'e hannu Nihal tayi ganin car key ya sata zare ido tana cewa, "wannan kyautar da Abba ya bani tayi yawwa, kyautar dana amsa yau tayi yawwa gashi ni ko motar ban iya ba" Nihal ta ida zancan tana kallan sultan ja mata kumatu sultan yayi tare da cewa, "se na koya maki..! yana gama fadar haka ya fice shafa kumatun ta Nihal tayi tare da sakin murmushi tana kallan kofa.

Da daddare after an gama dinner Nihal da su nawwara dakin Nihal suka shige wasa suke yi da pillow suna goje-goje a dakin Nihal, se ihu suke suna dariri ku, Nihal ko yanzu gidan ba karamin dadi yake mata ba, musanman kasancewar ta tare da su minal duk da ta girme masu amma tsakanin su ba wani nisa bane sosai, Dara dake bakin kofa ce tayi gyaran muryar, gyaran muryar Jakadiya ne ya sasu natsuwa da sauri Nihal ta aje pillow hannun ta tana kallan jakadiya Dara ce tace, "dare yayi ku wuce daki, time din baccin sultana yayi" simi-simi minal da nawwara suka fice suna cewa, "se da safe Aunty Nihal, se da safe Dara" pack Dara ta masu a kumatu bayin su suka rufa masu baya, maida kofa Dare tayi ta kule, murmushi Nihal ta saki tana cewa, "umma ina wuni"
"lafiya lau Nihal, ke dai har yanzu bakya jin jikin ki ki biye masu kuna tsale-tsale kin ji dadi Nihal baki da wata matsala wallahi kowa naki ne," murmushi Nihal ta saki tana sunne kai tace, "umma ina jin dadi zama da su, suna debemin kewa sosai" Nihal ta ida zancan tana daura kanta saman kafadar Dara, Dara ce ta katse mata tunani da cewa, "kin ga ba hira ya kawo ni ba, zuwa nayi na shirya ki, kin san yau zaki koma part din mijin ki" turo baki Nihal tayi tana cewa, "umma ni fa na dauka daki na zan kwanta" murmushi Dara ta saki tana cewa, "bana san fihili da can ba tare kuke kwana ba ko da kina Asibitin ai kullun kuna like da juna," turo baki Nihal tayi tana kallan Dara tace, "yau ina so na kwana dake ne ki tayani fira umma nayi missing naki" harara Dara ta watsawa Nihal tana cewa, "ka jimin fihili shi bakiyi missing nashi ba se ni, so kike sultan ya fara yimana zarya a nan, kwana ki nawa asibiti yaran nan ai yayi kokarin, ki godewa Allah kin samu miji mai natsuwa amma ke baki gani Allah ya shirya min ke Nihal" turo baki Nihal tayi tana cewa, "kullun umma se kin yabe shi amma ni bakya yabona dana aure shi" murmushi Dara ta saki tare da ja ma Nihal hanci tana cewa, "ke ma ina yaban ki a wajan shi" tab'e baki Nihal tayi tare da rungume jakadiya shafa kanta jakadiya take har cikin ran ta take jin san Nihal, jin ta take tamkar diyar da ta Haifa da cikin ta.

Yasmin ce ta dauko bathrobe barira da ke tsaye tana zaman jiran Nihal mikewa Nihal tayi tsaye tare da mika hannu bathrobe aka bata kayan jikin ta ta cire tasa bathrobe ta shiga toilet Dara na biye da ita kasancewar yau ita zatayi mata wanka, saboda tsarin masaurata ne duk wadda zata shiga turakar mijin ta se ta sha gyara, cikin kwamin wanka Nihal ta zuru santala-santalan kafafuwan ta tare da sakin bathrobe din yasmin dake gefe ta dauka ta fice, wanka Dara tayi ma Nihal bayan ta kamala tasa ta cikin kayan kamshi kala-kala Nihal har mamakin gyaran da ake mata take se ka ce ta shekara ba tayi wanka ba, gashin kanta ma haka ya sha wanki sannan suka fito a tare, suna fitowa saman sofa Nihal ta zauna zaman sarauta barira na mata massage yasmin na shafa mata lotion me kamshi sannan akayi drying gashin kanta, mikewa Nihal tayi ta tsaya gaban tangameman mirror dakin ta, sakin bathrobe din jikin ta Nihal tayi wata yaloluwar riga bacci pink Dara ta dauko ta sakawa Nihal wadda ita da babu ba maraba dai-dai gwiwa rigar ta tsayawa Nihal kallan rigar baccin Nihal tayi ta cikin mirror tare da juyowa cike da kunyar rigar tana cewa, "Umma bana iya fita da wannan rigar dube ta fa, kunya nake ji Allah" harara Dara ta maka mata tare da cewa, "ki zauna nan har se an kwace maki miji..! mi wanna rigar tayi saboda Allah idan zaki farka ki farka ki rike mijin ji" Nihal ko cikin zuciyar ta cewa take su miji manya ita ina ruwan ta koma waza ta kwace shi ta kwace ita ba abinda ya dame ta, in banda yanzu ma daya sako ai ko kallo be ishe ta ba, shagwabe fuska Nihal tayi tana cewa, "Allah rigar kunya take bani dube ta shara-shara" ganin ba wasa a fuskar Dara yasa Nihal hakura tare da zama gyara mata gashi kanta akayi tare da jera wasu flowers masu kyau a kan gashi aka nanad'e kasan gashin kamar ganmu sannan aka tsantsara mata make up, har mamakin irin kwalliya da ake mata take maroon alkyaba Dara tasa mata tasha aiki da gold zare se kyalkyali take turare aka feshe Nihal da shi duk da kamshi da take zubawa, ita kanta Nihal data kallin kanta a mirror ta sheda kyada data zuba, wani magani Dara ta mikawa Nihal a cup amsa Nihal tayi ta shaye tas tana gama sha ta kwabe fuska sannan Dara ta ce, "muna yi tafiya" mikewa Nihal tayi tare da daura hula alkyabar a kanta Dara na gaba Yasmin da barira na bayan Nihal a hankali Nihal ke takawa zuciyar ta na tsana ta bugawa.

Bangaran sultan ma shirya shi akayi cikin sleep robe maroon sumar kanshi tasha gyara se zuba kamshi yake yana tsaye gaban mirror sinbul da barma na shirya shi, lumshe ido sultan yayi yana tunanin Nihal a hankali ya bud'e idanuwan shi a lokacin su barma da sinbul sun gama aikin sun kai a sunkuye suka fice.
Chapter 79 · 0% Book details