← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 128

Sashe 113

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

malam ne ya nisa yace, "Alhamdulillahi ala kulli hali lafiya ta samu, Allah mun gode maka da ka kawo karshan wannan matsala, Ah malama bai kamata kina jifar dan'uwan ki da wad'an na kalamai ba, bai kamata aga laifin shi ba tunda idan na fahimci bayani ku akwai rikitacan alamari game da labarin da kuke badawa mai rudani da alamar sahannu a cikin alamarin ku, tana iya yuyuwa musibar data fada maki ita ce ta fada mashi tana iya yuyuwa shima samu akayi mashi, kina iya ganin farak'u aka mashi da iyalan dan uwan nashi" maimartaba yace, "wannan gaskiya ne baza a yanke hukunci lokaci daya ba" waziri yace "tabbas..! malam yace, "yanzu yarda za'ayi ya kamata muje kauyan na su suyi magana ta fahimtar juna su sasanta kan su, idan har alamarin ya hada da junu sai muyi mashi magani dan samun waraka ko ya kace ran ka ya dade? nisawa maimartaba yayi yace, "duk yarda kace malam haka za'ayi ni dai fata na Nihal ta kasan ce da yan'uwan ta matsala dake tsakani su ta warware ta samu SAUYIN RAYUWA kamar kowa ni d'a mai gata, idan Allah ya kai mu sai mu shirya muje shanonon gabaki daya" kowa yayi na'am da zancan maimartaba sannan taro ya watse mazan suka wuce masallaci mata suka wuce bedroom dan dauro alwala.

Wuni yau zungur Nihal na makale da Dara kafar Dara kafar Nihal sai tsiya ake mata kan yarda duk tabi ta likewa jakadiya tamkar za'a kwace mata ita daga ita har jakadiya baka gane mai kwakwar wani saboda nunawa juna su tsantsar fari ciki da kokarin faran ta wa juna su.

Da daddare Nihal ce kwance ta daura kanta saman cinyar Dara tana cin fruit tana zuba mata shagwaba dan wanna cikin nata har da shagwaba yake sata da fada na karfi da yaji, sultan ne ya shigo dakin cikin fara'a ya zauna cikin ladabi Dara tayi yunkuri gaishe shi yace, "haba haba umma ko a da can baya ina hana ki bale kuma yanzu da kika zama surukata" murmusawa Dara tayi tana jin dadi irin girmamawar da sultan ke nuna mata tun ba yau ashe da raban wata rana zai zama surikin ta, bata da abinda zata iya cewa su maimartaba saboda halacin da suka mata ya kai, kallan Nihal sultan yayi yace, "hayaty gabaki daya yau kin manta dani ko dadi umma, ko magani ki na dare baki sha ba" sunne kai Nihal tayi tana kallan sultan ta kasan ido da yake ta faman aika mata da kallo mai cike da tsantsar kauna, Dara ce tace, "Dare ma ya riga da yayi ya kamata ku wuce shashan ku sai ta samu ta sha magani yanzu nan ma na gama yi mata bita kan rashin san ci abinci da takeyi, gobe da safe ma cigaba da hira d'iya ta" turo baki Nihal tayi tana kallan sultan kamar karamar yarinya tace, "Ni kam yau tare zamu kwana da Umma," dan zaro ido sultan yayi yana kallan Nihal da tayi mursisi umma tace, "ba za'ayi haka ba ki lallaba ki bi mijin ki, in dai nice kullun ina cikin gidan nan ba guduwa zanyi ba, kuma yarda kike fama da laulayin na ai sai likita bokwan turai" sai da sultan ya fakaici idanuwan Dara yayi ma Nihal gwalo yana cewa, "fada mata dai umma" Nihal kuwa tayi kincin-kincin da rai ba yarda ta iya haka ta mike tabi sultan tana turo baki.

suna fitowa parlour sultan yace, "fushi ake dani dan na hana a kwana da Umma saki ran ki magani zan baki sai ki koma kin ji hayaty" sultan ya ida zancan yana kashe mata ido cike da zolaya didira kafa Nihal take tana dukan kirjin sultan cikin sigar shagwaba tace, "ai kasan umma baza ta bari ba shiyasa ka ce haka" Nihal ta ida zancan tana ja ma sultan kumatu hannu ta ya kama ya sakar mata pack cikin tafin hannu ta yace, "ina san ki mata na, nayi sa'ar samun ki a matsayin matata..! murmushi Nihal ta saki tana wasa da bottle din rigar sultan tace, "nafi kowa sa'ar mijin ina matukar sanka love" a hankali sultan ya daura labban shi sama lips din Nihal ya sakar mata kiss tare da daukar ta cak suka wuce part nasu Nihal nata zuba mashi shagwaba.

Washe gari da safe bayan kowa ya shirya cikin shigar shi ta alfarma gabaki daya kowa na sanye da alkyabar shi mai tsadar gaske sai dai duk ta maimartaba tafi ta kowa tsada daga ta shi sai ta sultan, bayan sun gama breakfast suka dunguma gabaki daya suka wuce parking space Dara da Nazili mota daya suka shiga sai mom da Gimbiya jalila mota guda Ammi da Adda mota daya maimartaba da waziri mota guda Ammar da Basmal na mota daya sai Ashad da malam ciki mota daya sauran motar ta fadawa sultan da abar kaunar shi cikin mota suna makale da juna a gidan baya duk da har a lokacin zuciyar Nihal bata daina tsinkewa ba ganin haka yasa sultan daura kan Nihal sama fafadan kirjin shi a haka motocin suka tashi zuwa shanono.
Chapter 113 · 0% Book details