← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 128

Sashe 92

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Da daddare Nihal ce zaune dakin Ammi suna hira turo kamar da akayi ne yasa Ammi juyowa washe baki Ammi tayi tana cewa, "dan albarka kamar kasan naka rai na" murmushi sultan ya saki tare da zaman kusa da Ammi yace, "matar yanzu kin daina ji dani kin fi ji da kishiyar ki na lura," Nihal dake gefe tana jin abinda sultan ke cewa tunda ya zo ko daga kai ta kalle shi taki se shi dake fama satar kallan ta ganin bata da niyar kallan shi yace, "Hayaty ki shirya zaki rakani wani waje yanzu" dagowa Nihal tayi karfa suka had'e ido da sultan Ammi ce ta katse masu tunani da cewa, "yau fitar masoya za'ayi kenan" murmushi sultan ya saki yana cewa, "matar baki kishi na ma ko toh shikenan," murmusawa wa Ammi tayi tana cewa, "toh ya zanyi tunda kamin kari koma dai minene ni ce on top" sakarwa Ammi pack yayi a goshi yace, "kamar kin sani yar tsohowa" dariya Ammi tayi tana cewa, "ni ba tsohuwa ba ce" dariya sultan ya tintsire da ita tare da ficewa, Ammi tace, "Nihal tashi ki shirya kiyi kwalliya sosai daga gani fitar nan, na da mihimmaci, tunda fita da mai gida ne ya kamata ki kure a daka" murmushin yake Nihal ta saki tare da cewa, "toh..! zata fice Ammi tace "ko da yake dawo, wannan aikin se jakadiya" zaman Nihal tayi tana cewa a zuciyar ta fita da shima se anyi wasu iyayi shi yasa ya samu waje yana yadda yaga dama, dawowar Ammi da Dara ne ya dawo da Nihal daga duniyar tunani Dara ce tace, "muje ko" gyada kai Nihal tayi tabi bayan Dara zuwa dakin ta, shirya Nihal tayi cikin wata dark green gwon rigar ta kama jikin Nihal sosai bakin ta ya sha red Jan baki, bakin yayi dan karamin da shi parking gashin ta Dara tayi sannan ta bata veil Apple green colour da fost silver ta feshe mata jiki da turare me kamshi wani irin kyau Nihal tayi sannan suka fito, lokaci yayi dai-dai da fitowar Nazili zata wuce dining area birki ta ci tana kallan Nihal zuciyar ta na lugudan bakin ciki, bakin ta kasa shuru yayi tace, "jakadiya ina zaku je da wannan daran kusan 7:30pm" murmusawa Nihal tayi tare da katsewa jakadiya hanzari tace, "zan fita da muradin rai nane ma'a mijin na sultan" Nihal ta ida zancan tana tsare Nazili da ido irin ki mutu idan kin ta shi murmushi daya fi kuka Nazili ta saki tana cewa, "hakan na da kyau dama fitar masoya da daddare tafi, musanman sultan da bashi da lokaci da rana," murmusawa Nihal tayi tace, "kamar kin sani, kinyi tunani da kika gane haka..! Nazili na kokarin magana sultan ya shigo main parlour cikin wanka shi na suit kamar kullun yayi wani irin kyau, shock Nazili tayi da kyar take danne abinda ke yunkurin fito mata dan ji take tamkar tayi hauka, ga wani fitinan kamshin sultan daya wuce ta ta shaka wanda ko kallan ida take be ba yana can yana kallan Nihal dan ji yake kamar ya hadiye ta saboda so jikin Nazili rawa yake saboda baccin rai tana kallan Nihal dake mata alama da ido taga yadda gogan nata ya rud'e ko kallan kowa ba yayi tana malallancin murmushi har sultan ya karaso gaban yana smile ya kama Hannun ta tare da sakar mata pack yace, "hayaty kinyi kyau sosai" cikin yauki Nihal tace, "na gode,"
"muna iya tafiya" sannan suka fice suna makale da juna Nihal na waigen Nazili da tayi mutuwar tsaye suka fice.

Suna isa compound Nihal ta zame jikin ta tare da daurewa tace, "ina zamu ne cikin daran nan baka san naje makaranta na dawo na gaji bane, lokacin hutawa nane yayi dan dai kawai a gaban Ammi kayi maganar nan shiyasa zan bika dan bazan iyayi maka musu a gaban ta ba, amma daga yau karka sake min haka Sultan", sultan ko zuba mata ido yayi yana kallo yadda take masifa da dan karamin bakin ta ji yake kamar yayi kissing nata, sannan Nihal tayi gaba, yana kokarin bud'e mata murfin mota tace, "bana so ina da hannu" sannan ta bude ta shige ta zauna sultan ya zagaya ya zauna.

Hawayan bakin ciki ne suka fara zubowa Nazili gabaki daya kayan dining ta daga ta watsar tana haki gabaki daya bayin dake part din Ammi fitowa sukayi da gudu suna kallan barnar da Nazili tayi da sauri Aziza ta karaso gaban ta tana cewa, "Gimbiya me ke faruwa? dafe kai Nazili tayi tana cewa, "kai na ze fashe juyawa yake ina bukatar iska..! Nazili ta ida zancan a tsawace da sauri Ammi ta karaso ta kama Nazili tana cewa, " abar kauna ta mike damun ki, kika shiga wannan hali" Ammi ta ida zancan tana kwalla da kyar Nazili ke maida numfashi cike da tsiwa tace, "Ammi ku fida ni waje ina bukatar iska, kowa ni matsiyaci ya koma bakin aikin shi kunyi tsaye kuna kallo" janyo hannun ta Aziza tayi Ammi tace, "Ku fita da ita ta samu iska, abar kauna ta duk abinda kike so shi za ayi maki sannu kin ji" Ammi kuwa hankali ta duk ya tashi har da hawaye tace mi ke damun Nazili ne dan bata kawo ma ranta fitar su sultan bace ta gigitata haka ba, su na fita gander suka nufa suna isa Nazili tace, "ki tafi ki ban waje ban san ganin kowa kusa dani, natsani ganin fuskar kowa" Nazili ta ida zancan cikin tsawa Aziza na tuntube ta bar wajan zamewa Nazili tayi daga resting chair ta zunduba wani irin ihu tana kuka tamkar ranta ze fita cikin kuka tana cewa shikenan ta kwace shi har abada, bazan taba yadda ba se na kwato abuna, kuka Nazili take bana wasa ba tana sanbatun tamkar mahaukaciya dafa ta da akayi ne yasa Nazili dako da jajayan idanuwan ta ba kowa bane se Alex da ya shigo garden yana waya da family din shi ji kuka ne ya sashi nufo wajan, tsare shi Nazili tayi da jajayan idanuwan ta da kyar ta iya furta, "me ya kawo ka nan? na fada bana san ganin kowa, ka tafi ka bani guri bana san ganin kowa..! Nazili ta fada a tsawa ce Alex ko tausayi ta bashi ya rasa dalilin dake sata yawan kuka da shiga damuwa bata rasa komai ba amma ta jefa rayuwata cikin damuwa, mikewa tsaye Nazili tayi cikin shashekar kuka tace, "tunda baza ka bani guri ba ni zan baka tunda kai baka gane ya ran da nake maka" takawa Nazili ta fara tayi tamkar wadda tayi shaye-shaye saboda jiran dake dibar ta luuu ta tafi zata fadi Alex ya taro ta yana cewa Gimbiya..! Gimbiya..! Da karfi yana taba kumatu ta amma ta sume daukar ta cak Alex yayi ya nufi cikin gida a rude.
Chapter 92 · 0% Book details