← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 128

Sashe 36

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bud'e mashi kofa akayi ya shiga parlour Mom ya gani zaune wadda tun d'azu take zaman jiran shi, murmushi ta saki shi kuma Sultan ya wani kwabe fuskar kamar ze yi kuka ya k'araso tare da daura kan shi saman kafad'ar mom, a hankalin mom take shafa kan shi sultan yace, " Mom please kiyi ma maimartaba magana ya janye maganar nan bana san ta, don't like her, she's annoying" kissing forhead d'in shi Mom tayi tare da cewa, "this is ammi decision let her be," kuma yarinyar tamin ba ruwan ta, kayi tunani akan zab'in kaji my boy, ka ga Saboda maganar da kayiwa ammi har hawan jinin ta ya tashi, baka kyauta ba," shuru Sultan yayi duk se yaji ba dad'i ko kowa ze k'i zab'in ammi ya kamata shi ya bi, mikewa yayi tare da cewa, "bari naje na dubata"
"Bacci take yanzu Dr Amir ya zo ya dubata, ina ta kiran wayar ka bata shiga lokacin" shuru Sultan yayi can kuma yace, "kashe ta nayi saboda bana san a takurami" Mom ta girgiza kai tare da kiss cheeks din Sultan tace, "Sai da safe" murmushi yayi tare da rako mom har bakin part nata sannan ya koma nashi cike da tunani

*_Muje zuwa yanzu aka fara labari,🤪 idan Nazili taji Sultan zeyi aure ya zata kasance zata barsu bayan auran su sha iska kuwa? wani hali Ammar ze shiga idan ya gane cewa Nihal ce matar da Sultan ze aura shin ze hakura ya auri Basmal,! yaya karshen gwoggo da baffa ze kasance, Gimbiya jalila mi zata ji idan ta gane Sultan be san Nihal kuma itama bata san shi wani irin zama za suyi gashi kowa ze zuba masu idanuwa ne shin Sultan ze daina zargin Nihal na da had'i baki da su Gimbiya jalila koko_*🤔

_yawan comments yawan posting_🤣😂🤣 Nima daga wannan page d'in zan zama yar duniya walla

```Taku har kullun Salma mas'ud nadabo```
[1/7, 2:27 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊
💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
*Story*
*And*
*Writing*✍🏾
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest```)

*_Kyal kyal🤣😂🤣 Ashe dai haka sauyin rayuwa yayi farin jini😍 karku damu fan's insha Allah zan rink'a posting kullun sai dai idan laruru ne ya kama ni kusan jiki da jini🤪 jiya dai naga masoya da masu kira da masu magana a group da masuyi ta prvt duk na gode insha Allah zan rink'a kwamuso maku story kamar ba gobe_*🤸🏽‍♀🤸🏽‍♀

*Page: 63_64*

*Washe gari*

Shiryawa Sultan yake cikin wata suit Apple green colour da black inner tie d'insa the same colour da suit d'in Cufflinks yasa tea green diamond stone ke da su, Suit d'in ta kama jikin shi kamar Dan shi akayi kayan making his figure perfect, wani silver bezel wrist watch ya saka da wasu covered shoes black, masha Allah he looks breath taking, ya b'ata fuskar nan, despite he look magical handsome, fashe jikin shi yayi da turaran Al-haramain tare da k'ara gyara gashin kan shi, kallan Sinbul yayi tare da cewa, "ka dau ki briefcase d'ina ka kai min parking lot ka ba Alex" to Sinbul yace, tare da ficewa A hankali yake tafiya kamar me tausayin k'asa, a haka har ya k'arasa part d'in ammi saboda da tunanin ta ya kwana a ran shi yana shiga yaci karo da Jakadiya murmushi ta saki tare da cewa, "Ranka yadad'e ka tashi lafiya" murmushi Sultan ya saki tare da cewa, "Lafiya lau Dara" d'aga kira yayi tare da rik'e kugun shi yace, "Dara ina matar ne"
"Tana d'aki kasan jikin nata ya motsa"
"Toh Sultan yace tare da wuce wa bedroom d'in Ammi cike da shagwaba.

A hankali ya bude handle d'in kofar zaune ya hango ta saman gado gefe kuma Nihal ce zaune hannun ta dauke da plate din abinci tana feeding Ammi pepper soup d'in nama rago, sanye take da riga pink me hannu vest da mini sket black gashin kanta yasha gyara, tayi parking nashi da black ribbon daga k'asa ya nanad'e kamar taliya duk da ba kwaliya a fuskar ta tayi kyau sosai, kallo d'aya Sultan ya mata ya kauda kai tare da gyaran murya, gabaki d'ayan su juyowa sukayi a tare suka zuba mashi idanuwa, wani irin kyau Nihal taga Sultan ya k'ara mata har yafi lokacin da ta fara ganin shi, a zuciyar ta tace, " ya Allah wannan mutumin Akwai kyau masha Allah, amma daga ganin shi ba lalai yayi kirki ba ko fitsara da yayi ma ammi jiya ta nuna halin shi, shagwabe fuska Sultan yayi ya zama abin tausayi, Nihal na ganin haka ta aje plate d'in hannun ta saman bedside drawer tare da mik'ewa zata fita rik'e hannun ta Ammi tayi murmushi Nihal ta saki tare da yima Ammi pack a goshi tace, "bari na baku guri kuyi magana" murmushi Ammi ta saki tare da sakin hannun Nihal, A hankali ta taso har a lokacin Sultan na bakin kofa yana bin Nihal da kallo se da ta zo daf da shi sannan ya kauce tare da aika mata harara, kauda kai Nihal tayi dan baza ta juri kallan tsanar da Sultan ke mata ba tausayin kanta ne ya kamata, anya ko zata iya daukar irin cin kashin da tasha A hannu su gwoggo kuwa, lokaci yayi da ya kamata ta kwatar wa kan ta yanci lumshe idanuwa Nihal tayi tare zama saman kujera parlour tana tufka tana warwara.

Karasowa sultan yayi bakin bed d'in ya zauna yana murmushi a hankali ya kama hannu Ammi yayi kissing nashi tare da cewa, "Am sorry Ammi nasan ban kyauta ba, abin da nayi maki ji Ammi" kama kunnuwanshi yayi biyu tare da cewa, "ki yafemin Ammi" ya ida zancan cikin raunaniyar murya, Sauke hannuwanshi Ammi tayi tare da cewa, "Ni ya kamata na baka hakuri na had'a ka da abinda baka so, kuma gaskiya ka fad'a a matsayin ka, ya kamata ace Kasan daga wani tushen wadda zaka aura ta fito ni ya kamata na nemi yafeyar ka sultan" daura d'an yatsan shi Sultan yayi a lips d'in Ammi yana girgiza mata kai yace, "Ki daina fad'in haka Ammi indai zab'in ki ne, na amsa hannu bibiyu zan nunawa duniya cewa Ammi ta isa da Sultan ba maimartaba kad'ai ba, zan nunawa zab'in ki so" ya ida zancan yana killing smile d'in shi har dimple d'in shi na lomawa, murmushi Ammi ta saki tana cewa, "Da har zan janye maganar" ware idanuwa Sultan yayi tare da cewa, "So kike na Shiga wani Hali, ban k'arewa zab'in ki kallo ba se yanzu" ya ida zancan yana kashewa Ammi ido, dariya Ammi ta saki tare da Jan cheeks d'in Sultan tace "kai ko" wani irin dad'i Sultan ya ji ganin yasa Ammi cikin farin ciki, bin Ammi da idanuwa Sultan yake yana murmushin yak'e kenan idan har yana so Ammi ta kasance cikin farin ciki ya zama dole ya auri Nihal wani bakin ciki ne ya tokare mashi wuya, janyo plate d'in dake saman bedside drawer yayi tare da cigaba da feeding Ammi tana ci yana bata labari har ta cinye sannan yayi kissing goshin ta tare da ficewa.
Chapter 36 · 0% Book details