← Book details Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 128

Sashe 1

Sauyin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🕊 *SAUYIN RAYUWA* 🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing* ✍🏻
*By*
*Salma Mas'ud Nadabo* 👑

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the rest ```)

https://mobile.Facebook.com/Real-hausa-fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera-speed-dial&_tn--=H-R

Email:[email protected]
Facebook: www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

*GARGAƊI*
```Ban yadda a juya min wannan labarin ba, ta kowace hanya, ba tare da izini na ba. Don haka a kula a kiyaye. ```

*TUNATARWA*
```Labarin dake cikin wannan novel ɗin ƙagaggen labari ne dan faɗakarwa da nishaɗantarwa haka kuma suna yanda ke ciki|```

```BISMILLAHIRAHAMANIN RAHIM```

*Page: 01*

Wanke wanke ne jibge a tsakar gida Wanda ko gidan biki ne sai haka, yarinya ce wadda baza ta wuce shekara goma shahudu ba, zaune saman kujera tayani gulma, ta tasa wanke wanken gaba, sai sharar ƙwalla take inda sabo ya kamata a ce ta fara sabawa da wannan baƙar wahalar, kallo ɗaya zaka mata kasan a wahale take, ko kayan jikin ta sun sha ruwa har sun gaji, yar riga da zanine sun mata yawa saboda tsabar rama, ko ba'a fadama ba kasan yunwa na galabaitar da ita, fara ce amma saboda tsabar wahala tayi jirwaye bama a gane farin sai ta daga wuyan ta, tana ɗauke da dan siririn hanci da baki dan qarami pink, duk da kodewar da tayi hakan be hana aga kyan da Allah yayi ma *Nihal* ba,

Tsawar da aka daka mata ce ta sata ɗagowa a razane, cikin ɗaga murya indo tace, "dan uwar ki uban mi kike da har yanzu kin gagara gama wanke wankenan."

"Shegiya mai ruwan maita, kiyi ƙoƙari kisa na rasa cinikin safe, dan wallahi bazan lamunta ba" goge hawaye Nihal tayi tare da cigaba da wanke wanken da takeyi, dan sarai tasan wacece Gwaggo indo, dan ba yau ta saba rufe ta da duka ba.

Cikin sauri ta samu ta sauke kwanikan ta kai su ma'ajiya, qoqarin bude daki take, gwogo ta daka mata tsawa keeee!!!.. Birki Nihal taci ta juyo cike ta fargaba tana zare ido, harara Gwaggo ta aika mata tace, "mikike nufi da haka? sai kin gama taɓa ƙazamar uwar taki, sannan zaki dawo ki sheƙamin koko"?

"Masu siya susha su mutu kenan tunda ba uwar ki keda asara ba ko, aiko zan gwada maki kuskuran da ki kayi na ƙoƙarin shiga ɗakin Hansatu."

Janyo ta gwogo tayi ta soma jibga sai da ta mata lilis sannan tayi kwallo da ita kanta ya daki bango, qara sakin kuka Nihal tayi, Gwaggo kuma sai faman haki take tace, "narantse da Allah daga ke har Hansatun ba wadda ta isa ta ƙasarani wallahi uban kuma ya ja da mu ya zama gawa bale ku wallahi ƙarya kuke,"

"Bari malam ya dawo shima zanji dalilin aje min ku a gida, da bai watsa Ku almajiran ci ba daga ke har uwar taki"

"Na baki nan da yan mintina ki sheƙa koko, in kuma ba haka ba jikin ki ya gaya maki" sannan gwogo ta ja dogwan tsaki tana qoqarin shigewa ƙurya ɗakin ta, lallau san murmushi ta saki kamar ba ita ke hargowa ba tace, "a'a yar baba har antashi kenan"... "Eh wallahi Gwaggo" Saratu kenan ɗiyar Indo wadda ta daurawa san duniya ko tsinke bata so ya taba ta bale mutum

Kuka ne ya kubucewa wa Nihal tace , "astagafirilla Wannan wani irin *SAUYIN RAYUWA* ne ," jiki ba ƙwari ta miqe tare da Shiga madafa tana sharar ƙwalla, Saratu ta bita da harara.

Duk Wannan tijarar da Indo ta gama, duk a kunan umman Nihal tayisu wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata.

Ba ta taɓa tunanin ko a mafarki Ahalin *Tanimu* zasu wulaƙanta su ba amma sai gashi yau mutuwar malam taja masu tabbas sun ga *Sauyi Rayuwa*

```Taku ce har kullun Salma Mas'ud Nadabo
```✍🏻
[1/7, 2:22 PM] Salma 😛: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🕊 *SAUYIN RAYUWA*🕊

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

*Story*
*And*
*Writing*✍🏽
*By*
*Salma mas'ud nadabo*👑

*Edit by:*
*Aliyu Miko Muhammad*

🌲 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
(```We are the best among the best ```)

https://mobile.Faceook.com/Real-hausa-fulani-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=operaspeed-dial&-tn_-=H-R

Email:[email protected]
Facebook: www.Facebook.com/REALHAUSA FULANIWRITER'SFORUM.com

*Page: 02*

Kamala tatar kokon Nihal keda wuya, ta juye shi a bokitin da take zuwa talla da shi.

Ganin Gwaggo na ɗaki yasa tayi sauri ta shige ɗakin su, cike da sallama ta Shiga ɗakin tana mai kallan umman ta, dake kwance saman tabarma wadda ko motsi ba tayi daga idanuwan ta sai bakin ta, dake motsawa sakwamakwan ciwo da take, kallo ɗaya zaka mata kasan mahaifiyar Nihal ce, a hankali Nihal ta matso kusa da ita, duk da warin da take tabbas abinda Gwaggo ta faɗa gaskiya ne, babu abinda ummi keyi inbanda tashin wari kasancewa uwa uwa ce shiyasa ko jin warin ba tayi. murmushi ta kuma saki tare da daura hannun ta saman gashin umma, Wanda ya cukurkude amma duk da haka ana ganin tsawan shi da laushin shi, wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo ma umma, girgiza kai Nihal tayi tace, "umma na abin alfahari na, ki daina zubar da hawayan ki insha Allah zaki warke umma, ki rinƙa yawo kamar kowa kinji rabin raina," ta idar daal zancan tare da shafa gefen fuskar umma.

murmushi Umma tayi ta buɗe baki a hankali wadda ya mata nauyi tace,"Allah yasa maki albarka Nihal," "Amin Umma, sai kinyi hakuri yau Umma na naso ace tun kafin asuba na tashi, har na maki wanka amma yanzu lokaci ya ƙure," murmushi kawai Umma tayi Nihal ta miƙe har ta kai bakin ƙofa ta juyo tana kallan Umma sannan ta fita da sauri.

Cikin sa'a ko da ta fita Gwaggo na ɗaki sai shewarta da ke tashi ita da yar lelan ta, bokitin koko kawai ta ɗauka, sannan ta sa kai ta fita tana tafe tana sauri kansancewar har yanzu gari bai waye ba sosai, gashi ƙafar ta ko arziqin takalmi bata samu ba, sai zafi da fasan ƙafar ta ke mata haka dai ta samu har ta kai tasha, wato inda suke sai da koko.

"Nihal". "Nihal" sunan ta da ake ta kira ne ya sata waigowa cike da fara'a, "jummala".. "na'am".. "me yasa yau baki biyo min ba?. rausaya kai jummala tayi, "ina san zuwa Nihal amma abinda Gwaggo ke maki ne bana jin dadi shiyasa Nihal."

Rausaya kai Nihal tayi tace, "karki damu jummala lokaci ne ya kawo haka tare da sauyin rayuwa, yau kusan shekar hudu kenan raban dana tsinci kai na cikin fari cikin jummala" ta ida zancan wasu hawaye na sulalo mata hannu jummala tasa ta goge mata hawayan, ba komai ƙawata Allah yana tare daku ke da Umma , a haka suka ƙarasa har gaban bishiya suka zauna.

Wani ɗan matashin saurayi ne ya ƙaraso gaban su, cike da murmushi yana kallan jummala yace samin dan wakyan 50, sannan ya samu guri ya zauna yana kallan Nihal yace, ni ko jummala na rasa mi nayi ma ƙawar ki, bata min magana kullun fuskar ta daure ya fada yana kallan fuskar Nihal cike da fara'a, girgiza kai jummala tayi tace, "laaa wallahi baka fahimci Nihal bane shiyasa"

"To shikenan yanzu dai duka nawa ne kudin koko dana dan wakyen?

"Bana so ina ganin Ku anan kuna talla" duk Wannan zancan da saurayin keyi kan Nihal na ƙasa ko Kallan inda saurayin yake ba tayi, murmushi jummala tayi tace, "Ni ko kana bani mamaki, har yau ka kasa faɗa mana sunan ka, amma kullum sai ka siye kayan mu duka kuma da alama kai ɗan birnine ko?"

"Jummala Ashe ana gane yan ƙauye irin mu kenan"? dariya Jummala tayi ita da Nihal wadda sai a lokaci ta dan dara.

Wannan ɗan saurayin da ke zaune kusa da su Nihal ba yau ya far zuwa tasha ba, kuma kullun fes zaka Ganshi shi dai baza'a kira shi da fari ba amma dai ruwan tarwada ne, daka kalle shi kasan dan Hutu ne dan beyi ruwan dan kauye ba, har wa yau dai bai taɓa faɗa masu suna shi ba, duk sanda Jummala ta tanbaye shi sai yace mata sunan shi bawan Allah, hakan yasa Jummala ke Kiran shi da dan uwa haka itama Nihal duk da ba wata magana ke Shiga tsakanin su ba, amma duk san da ya zo sai ya kafe ta da idanuwan shi, hakan yakan sata jin nauyin shi, haka ya ƙirgo kuɗin ya basu sauran yace sunyi sadaka haka suka rinqa mai godiya, har yayi gaba Nihal tace, "yaya Allah ya biya maka buƙatunka na alheri, lalausan murmushi ya saki yace, amin Nihal, sannan suka cigaba da Raba talla, har Nihal ta dibar masu dan idan zata iya tunawa raban su da abinci tunda jiya.

Kasancewa juye sukayi yasa tun karge 10:00pm ta kamo hanyar gida jummala tayi hanyar gidan su, har ta shawo kwana taci karo da Mudi da alama ya sha ya bugu kallo ɗaya zaka mai kaji baka marmarin maimatawa, shine babba ɗan Gwaggo daga shi sai saratu wadda yayi mata nisa sosai ko wajan haihuwa, rabawa tayi ta gefan shi zata wuce, fisgota yayi ya kifa mata mari yace, "dan ubanki har kin isa na wuce ke ma ki wuce baki bari na gama wuce wa yo ko uwar ki Hansatu ta isa na wuce itama tazo zata wuce, tunda Mudi ya wanke ta da mari ta kafe wasu hawaye masu zafi na bin kuncin ta ko kallon ta bai kuma yi ba ya wuce, yana zuƙar sigarin da ke hannun shi zamewa tayi ƙasa tare da sakin kuka me cin rai sai da tayi kuka ta gaji sannan ta ja jiki ta Shiga ciki, muryar Gwaggo da dillaliya kawai ke ta shi a gidan.

"Haba Indo ke kanki kin sani ina maki sauƙin kayan nan kinfa san ke ka ɗai nake ma sauƙin kaya Indo"
"To shinkenan yanzu dai ki ajiye min su idan Malam ya dawo daga birni zan faɗa mai"."yauwa ko ke fa ƴar gari.
Chapter 1 · 0% Book details