Sashe 99
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan take angel ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume, kamar jira suke Yi giant ɗin Ya fita, Haris yai wani irin kukan kura ya duro daga saman gadonshi, Ya kai ma Danish farmaki, kwalar rigarshi ya damƙa ya jijjiga shi, Hawaye na fita Cikin idanuwanshi yace"Ka kashe mu danish! Ashe dama baka da hankali? Kai wani irin wawan mutun ne sakarai soko maloho, wanda baisan Ciwon kanshi ba, wlh ka karya mini zuciyata ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka Iya ruƙo hannun batool ka damƙa ma giant ita, don aje acutar da rayuwarta, ashe na yaudari kaina bansani ba, mugu azzalumi, wawa daƙiƙi...." Kafin haris ya ƙarasa maganar shi, Gaba ɗaya sauran ƴan uwan nasu suka tarar ma danish, bugu ta ko'ina suka shiga kai mashi, Kamar sun samu jaki, Hada matan duka suka nannaɗe hannayen rigunansu suka dunga bugunshi, amma ko gizau baiyi ba. Har saida suka fasa mishi hancin shi da bakin shi jini ya soma zuba, tukunna suka sake shi, anan ƙasa ya kife idanuwanshi sunyi jawur tamkar garwashin wuta, wani irin jiri yake gani, ya rasa meke yi mishi daɗi, ta ko'ina ga6o6in jikinshi raɗaɗi suke yi mishi domin kuwa ba ƙaramin bugu suka yi mashi ba, sun haɗa mishi Jini da majina sun xautar dashi,
Kowa sai faman haki yake yi, Kuma babu wanda yaji tausayin shi, suna a tsaitsaye cirko cirko suna kallonshi, sai faman juyi yake yi, tun da suke dashi basu ta6a jin tsanar danish ba sai yau daya nuna musu true colour dinshi, mugun zargin shi suke yi, tabbas shima yana atare da giant shiyasa yake goya musu bayan duk abunda suke yi. ÆŠan jakar uba,
Haƙiƙa Danish ya yi breaking heart dinsu, hawaye ta ko'ina akan fuskokinsu, Ji suke kamar su tattake shi ya mutu su huta, tun da baida amfani acikinsu, tare da shi ake haɗa baki a cutar da ƴan uwansu,
"Daga rana irin ta yau kada ka ƙara kiran mu da sunan ƴan uwanka, mugu azzalumi" Javed ne yai maganar, deeja tace"dama tun jiya da aka dawo dani, naga sauyi atare dashi, ko sannu baiyi mini ba, ashe hada shi ake haɗa baki a cutar damu,"
Mubeen yace"ae ni banso muka barshi da rai ba, wlh da mun sani mun karkarya ƙasusuwan Jikin shi, " yana magana yana cije le6e,
"Danish baida tausayi baida imani, yau ya tabbatar mana da hakan, shi É—in ba jinin mu bane, don haka ya tattara ya san inda dare yai mishi tun kafin muyi silar mutuwarshi,"
Duk wannan suratan da suke Yi, danish yana kwance, numfashinsa na fita sama sama, daga gani yana acikin mawuyacin halin da shi kanshi baisan Ina zai tsoma ranshi ba,
Hancin shi dake bleeding jini duk ya wanke farar fatar fuskarshi, muryarshi adisashe yake faɗin "ku taimaka mun da ruwa in sha" wani irin kallo mai kama da harara suka shiga jefa mishi, haris yace koba ruwa ba? Ka jira ka gani, don ubanka, " rai a6ace yaje ya ɗauko robar ruwan dake a ƙarƙashin gadon Batool ya dawo ya tsaya agaban danish, Ya buɗe murfin robar ya watsa mashi ruwan duka akan fuskarshi, yana gamawa ya jefar da robar ruwa aƙasa yace"Iya taimakon da zamu Iya yi maka kenan, ni banga ma amfanin kallonka da muke Yi ba, ku wuce muje mu xauna. Mubar shege ya ji ajikin shi". Yana ji yana gani ƴan uwanshi suka juya mishi baya, Suka nufi gadajensu su ka zazzauna, zuciyoyin su acike da alhinin rashin Batool da suka Yi,
Hanna ce ta lura babu angel acikinsu, babu wanda ya lura da cewar ta sume a bakin ƙopar shiga sashen toilet dinsu.da sauri ta miƙe daga zaunan da take a gefen gadonta, sai da ta fara zuwa karkashin gadon batool ta ɗauko wata robar ruwan, Ta nufi inda angel take kwance ƙasa, Ta buɗe murfin robar ta ɗan ɗebo ruwan a tafin hannunta ta watsa mata saman fuskarta, nan take angel taja dogon numfashi ta fatser dashi, muryar ta cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan batool tana faɗin An raba ni da ƴar uwata, innallahi'wa' inna ilaihirraji'un! Wannan wata irin rayuwace
"Angel ki tashi xaune," muryar hanna ce ta katse ta, jikinta duk ba daɗi, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe xaune tana faman huci sumar kanta duk ta tarwatse har tana kokarin rufe mata idanuwanta, bakowa ta ke kallo ba face danish dake kwance a ƙasa yana juyi, hannayenshi dafe da forehead ɗinshi,
Da buɗar bakinta sai cewa tayi"me danish yake yi araye batare da kun kashe shi ba"? Fuskarta babu wasa tai maganar, haris yace"munso muyi hakan amma sai muka ƙyale shi, bawai don mun haƙura ba ne, Xamu jira ne har time da za'a dawo mana da batool muga awani yanayi take ciki, idan ta tsira shima xai tsira da ranshi, muddin kuwa batool tarasa ranta a silar shi, wlh shima sai yabi bayanta, duk irin ƙaunar da nake yi mishi, xan rufe ido ne da hannu na zan kashe shi. Inya so nima daga bisani in haɗiyi zuciya in mutu"
Zuciyar angel har wani tafarfasa take Yi, sam ba haka taso ba, ta yi niyar tayi mishi bugun mutuwa har saiya haukace, Amma sai ta haƙura ta ƙyale shi ganin irin yadda jini ya wanke fuskarshi, koba komai Ya ɗanɗani irin zafin da suka ji acikin zuciyoyinsu,
"Angel, ki tashi muje saman gado ki kwanta" girgixa kai angel tayi tare da cewa"Kibarni anan kawai, ba inda zanje yau sai naga abunda ya ture ma buzu naɗi," gyaɗa kai hanna tayi tare da miƙewa ta juya ta koma saman gadonta ta zauna,..
Duk sunyi zugudum cike da zullumin awani hali batool take aciki, a lokacin da ba su yi tsammani ba, suka ga hasken ɗakinsu ya ɗauke, duhu ya mamaye idanuwansu, Da sauri javed Ya miƙe ya lalubo fitilunsu Ya kunna su, ɗakin yayi haske, yau fa ba bacci dare ya koma tamkar da rana, Jimamin rashin ƴar uwarsu suke ta yi, ba wanda ya damu da danish, gaba ɗaya sun manta da azeeza dake a sume Cikin ƙarƙashin gado,
Har dare ya tsala, babu wanda ya runtsa acikinsu, sai daga bisani ne, Haris ya lallashe su, har ya samu suka kwanta, shima ya kwanta zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin tausayin danish, amma haushin shi ya hana ya taimake shi, bashi kaɗai ba. Hatta sauran ƴan uwan nashi, duk sun damu. Da danish, tsoransu kada ya rasa ranshi,
Ganin sunyi tsit Yasa ta fara tunanin ko sunyi bacci ne, duk da tasan zaiyi wuya yau su iya runtsawa, sai dai su yi likimo, amma wannan duk bai dame ta ba, Don yau taci alwashin saita dura tagar nan kodan taje ta taimaki rayuwar ƴar uwarta, kamar yadda tayi alƙawari, bazata bari a lalata mata rayuwar ƴar uwarta ba, yunƙurawa tayi tare da miƙewa, taje saman table ɗinsu ta ɗauko fitila, Ta juya ta nufi cikin toilet ta buɗe ta shiga ciki, wannan karan ko jam lock bata sanya ba, a buɗe tabar ƙofar, domin kuwa jininta akan akaifa yake, Komai zai faru sai dai ya faru ko a mutu ko arayu,, tsakanin ita da danish, yau saita dura tagar nan, Ita kaɗai tasan irin ƙuncin da take ji acikin zuciyarta, bayan ta ajiye fitilar a ƙasa, da ƙarfi ta janyo bokitin ƙarfen ta jingina shi jikin bangon tagar, tana ƙoƙarin hawa taji motsin mutun ya shigo Cikin toilet ɗin, a waske ta juyo baya don taga wanene, Bata yi mamaki ganin shi ba, ai yanzu ta daina ganin shi a matsayin mutun, ita da taga zahiran ɗazu da jam lock ya cire kanshi,
A tsaye yake jikin shi duk ba ƙwari, wani abu daya ɗan ɗaure mata kai, Jini daya 6ata fuskarshi yanzu babu shi, aranta tace"nasan bai wuci shi ne ya lashe shi ba, tun da ɗazu ma naga yasha na batool, Maye kawai, "
Yadda suke fuskantar juna, kamar abokan gaba ne suka haÉ—u a filin daga, banbancin kawai babu makami ahannun su,
Cikin muryar fushi tace"kada ka kuskura ka matso ku sa dani, because I can harm you, I hate you Danish, I don't wanna see you, you are a bad person without faith and compassion,"
Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"You should understand me, I am innocent, I am doing what is right........" wata irin tsawa ta daka mashi yayin da take nuna shi da index finger ɗinta tace"ban damu da duk wani abu da zaka ce ba, wawa daƙiƙi, wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har ka kuskura kace zaka hana In dura tagar nan sai na yi maka mummunar illar da zata sa ka gaza takawa da ƙafafuwanka,"
A matuƙar ruɗe danish yake kallonta, baisan ya zai yi ya fahimtar da ita ba,
Ganin yana yunƙurin taka ƙafarshi xai tunkarota yasa ta takai hannu ta fusgi bokitin data ajiye ta ɗaga shi sama tana faɗin"Idan ka kuskura ka ƙara taku ɗaya, I will drop this bucket on your head idiot," a wani irin raunace yake binta da kallo, duk da irin gargaɗin da take yi mishi hakan baisa ya dakata da yin tafiyar ba, yana tunkararta, ganin dai dagaske so yake ya hanata, aikuwa da sauri ta ajiye bokitin ta haye tare dakai hannu ta ɗaɗɗago da glass ɗin, Ta dure shi ƙasa, Tana yunƙurin hawa bisa tagar, Taji ya damƙi ƙafafuwanta daƙarfi, a ƙoƙarin ya janyota ta faɗo Cikin rashin sa'a ya zame wandon Jikinta gaba ɗaya ya sabule ƴan fararen cinyoyinta santala santala suka bayyana a suffarsu, saboda tsabar jaraba ko waiwayon wandonta bata yi ba, A haka ta dire tagar ta faɗa ta baya.................."
Ta tafi tabar danish a tsaye hannun shi ruƙe da wandonta, don ma Allah yasa rigar uniform ɗinsu tana da ɗan tsayi ta rufe ass ɗinta duka,
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*