← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 179

Sashe 157

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"UNAIZA"! a yayin da ta ke ƙare mata kallo na ban al'ajabi, kamar fatalwa ta rame ta bushe ta ƙanjame, Irin rigar da aka dawo da batool itace a jikinta launin ja guntuwa wadda da kadan ta zarce mazaunanta ta yi wani irin haske, babban abunda ya tayar ma Angel hankali yakushin akaifar da ta gani akan fuskarta, wuyanta da fuskarta duk sun faffashe ta ko'ina red marks ne, hatta la66anta a fashe su ke sun kumbura, idanuwanta sun ƙanƙance daga gani ba ƙaramin kuka tasha ba, kamar ma bata a cikin hayyacinta, tsananin tashin hankali ne akan fuskar Angel, zuciyarta ba ƙaramin tashi tai ba, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, tsakanin majnun da ya ke yin shessheƙar kuka da kuma Unaiza da ke A tsaye jikinta na kerma, gabanta na faɗuwa ta soma tafiya tana tunkarar su, koda majnoon yai arba da fuskar Angel nan ta ke ya kware baki yana kuka yana ambaton sunanta, da gudun gaske Angel ta nufe shi tunkan ta ƙarasa gaban shi a wani slow ta zube saman gwiwowinta dab da shi ta sanya hannayenta biyu da ke yin kerma ta rungumo shi zuwa jikinta, tsabar tausayin shi da ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske tamkar ranta zai fita, sautin kukanta ne ya karaɗe cikin ɗakin nasu, Wanda silar hakan ya farkar da masu Bacci, A firgice kowan nan su yai wurgi da bargon shi a lokaci ɗaya su ka mimmiƙe zaune saman gadajen su suna faman mutsustsuke idanuwan su da hannayen su, ba zato ba tsammani idanuwan suka sauka akan Angel da ta rungume majnoon a ƙirjin ta, babu wanda Ya lura da Unaizah a cikin su,

Da ƙarfi Deeja ta furta sunan shi"CHINONSO!" ai ko da gudu Suka diddiro daga saman gadajen su Jamimah hada tuntu6e garin yin sauri jin an ambaci sunan abokin wasan ta, Azeeza ta watso da gudu, Gaba ɗayan su ne suka hallara a bakin benen Suna kallon shi, Hankalin su yai mugun tashi Zuciyoyinsu sun karaya, ganin irin tabbunan da ke a saman fatar shi, masu saurin kuka tuni sun fara irin su azeeza, tuni ta zube saman gwiwowinta tana yin kuka.

Hawaye ne kwance a cikin idanuwan su, Batool dake a tsakiyar su tana bin bayan majnoon da ido, tuni ta gane cewa su ne sabbin prisoners É—in da Angel ta bata labari akan su, waÉ—anda giants su ka tafi da su.

Muryar deeja a rauna ce ta furta "Inna lillahi wa inna ilayhir raji'un! Mutanan nan basu da Imani, mugaye ne azzalumai, Ku jibi yadda suka canza mishi halittar shi! Bawan Allah dame zai ji! Da ta6in hankalin dake damun shi ko kuwa da lalurar da yake fama da ita? Ga shi ƙarami dashi baisan komai ba, amma a haka su ka yi amfani dashi, Allah kaɗai yasan irin cutarwar da su ka yi mashi, nashiga uku ni yau! Mu kuma haka rayuwar mu zata ƙare a wulaƙance......." wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta wanda ya hanata ƙarasa maganar, Jamimah sai kuka take yi tana faɗin "Wayyo Allah Majnoon ɗina, Waya yayi maka haka? Jikin ka duk jini! Waye ya cutar min da kai"! Tsananin tausayin shi duk ya kamasu, Jikin batool ba ƙaramin sanyi yayi ba, ta duƙar da idanuwanta ƙasa hawaye ne kwance a cikin su, har yanzu babu wanda ya lura da Unaiza acikin su, Angel kaɗaice tasan da zamanta a wurin.

"Wacece wannan?" Ras gaban su Ya faɗi jin muryar batul tana tambaya, kusan atare suka ɗago da idanuwan su suka sauka kan fuskar Unaiza, Muryar su da alamun mamaki suka ambaci sunanta "yar Gidan daddy!" A tsorace suke kallonta, tun daga ƙasa har zuwa sama, girgiza kai Deeja tai muryar ta aruɗe ta furta "I can't believe it! Unaizah ke ce kika koma haka? Ko dai idanuwana ne su ke nuna min ba dai dai ba? Meya same ki har haka? Ina abubuwan ki su ke"?

Maganar da Deeja ta yi ce ta jawo hankalin su zuwa ga kallon ƙirjin Unaiza, Tsabar firgici ne yasa wasu daga cikinsu suka daddafe saitin zuciyoyinsu da tafin hannayen su, hatta Angel da ke a zuƙunne rungume da majnoon sai da ta zabura ta miƙe tana kallon ƙirjin Unaiza dake a shafe kamar Allon bango, babu nono babu alamar shi a wurin, yanayin kallon da su ke bin ta dashi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi, ruɗani da firgici.

Batul ce ta yi ƙarfin halin cewa bai kamata mu tsaya muna kallonta ba, tana a cikin mawuyacin hali, mu taimaka mata ta shiga ciki" miƙa hannu batul ta yi da niyar ta ruƙo hannun Unaiza, a firgice ta shiga girgiza mata kai, babu wanda yai tsammanin zata iya yin magana duba da irin raunatar da jikinta ya yi.

"Don't let anyone touch me, just leave me alone, I don't want to see any of you, I hate you, saboda kun 6oye min gaskiya, a lokacin dana tambaye ku ina ne nan ba ku faÉ—a min ba......" A wahalce ta ke yin maganar cikin karyayyar murya,

"Tuntuni naso na faÉ—a maki gaskiya amma Danish shine ya hanani saboda gudun halin da zaki shiga idan kika ji, Unaiza kada ki ga laifin mu, because we're not the reason you came to this prison! Your father is an evil tyrant who sacrificed you to meet his needs, Unaiza mahaifin ki ya cuce ki baya son ki fiye da yadda baki tunani......" zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Angel, Yawu ta haÉ—iya mai É—acin gaske, ga dukkan alamu zuciyarta ta gama karaya.

"I can't believe what my heart is telling me, that my father lied to me and brought me here to humiliate my life, ko a mafarki ban ta6a tsammanin hakan ba, saboda yana sona fiye da yadda ya ke son kan shi....." cikin shessheƙar kuka ta yi maganar tana nuna ƙirjin ta da index finger ɗinta, girgiza kanta ta yi hawaye na cigaba da bin fuskarta, ta ɗaura da cewa

"Duk da ba a ƙasa ɗaya muke rayuwa dashi ba, yana bani kulawa, kowace rana sai ya kira ni video call don yaji lafiyata, yasha faɗa min cewa bashi da tamkata a duniyar nan, nifa har ce min yai akaina zai iya 6atawa da kowa har mahaifiyar shi saboda ƙaunar da ya ke yi min, tun da na taso rayuwata ba a ta6a yi min tsawa ba, balle har ta kai ga ata6a lafiyar jikina, nayi rayuwar gatanci, Masu aikin dake kula da ci na da sha na sun fi mutun shidda, abunda nake so shi ake girka min, sannan a baki suke bani abinci, ina da likitocin da ke duba lafiyar jikina wanda mahaifina ne ya ɗauki nauyin yin hakan, Angel ko tari nayi sai an kira Dr ya duba ni, komai na ke so sai daddyna ya yi min shi, I don't ave any financial problems, before nabar gida ina da dala miliyan 2 a cikin account ɗina, wanda shine ya zuba min su don in yi sharholiyata, idan zanyi birthday sai na za6i ƙasar da nake so inje a shirya min party, suturar sanyawata duka babu na ƙasa da dubu ɗari, duk wani abu da kika sani mai tsada na mallake shi, a rayuwata bansan babu ba, bansan menene rashi ba............" dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana jan majina, tun da ta soma magana hawaye basu daina gangarowa saman fuskar Angel ba, idanuwanta sun canza launi sosai, tausayin unaiza ya ta6a zuciyarta, da zuciyoyin su Deeja da ke sauraronta, Azeeza tuni ta ɗauki majnoon ta ɗaura shi saman laps ɗinta ta ƙanƙameshi tana ta lallashin shi ita da jamimah kamar zasu ɗauke mashi ciwon da ke a jikin shi.

"Dan Allah ki daina magana, kina ƙara ma kan ki ciwo, ni tausayi kike bani," idanuwan batul cike tab da ƙwalla ta yi maganar, murmushin takaici Unaiza ta saki tana kallonta,

"Idan banyi magana ba zuciyata zata fashe ne, bakisan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata bane, nagaza yarda da abunda zuciyata ke raya min na cewa mahaifi na ne ya yaudare ni, Shine ya kawo ni nan don a Wulaƙanta rayuwata, Mahaifina fa! Wanda yayi silar zuwana duniya!......." girgiza kai ta ɗan yi fuskarta jawur, tasa harshe ta lashe ƙwallar da ta gangaro ta saman la66anta, duk suna kallonta gwanin ban tausayi.

"Nasan bana jin magana, sannan bani haƙuri indai akan biyan buƙatar kaina ce, amma ban ta6a ganin masifa da bala'i ido da ido ba sai dana tsinci kaina a hannun waɗanda suka fi ni iya shaiɗanci, sun ƙarar min da komai, sun kashe min rayuwata, babu abunda yai saura a jikina, yadda su ka yi treating ɗina ko dabba sai haka, An ci zarafi na an wulaƙanta ni an ƙasƙantar dani kamar karya........." A gigice Angel ta daka mata tsawa wadda ita kanta bata san ta furta ta ba, Ta yi hakan ne saboda gudun kada Unaiza ta furta abunda aka yi mata agaban su Hannah, saboda ta fahimci cewa tana acikin hayyacinta tasan komai da aka yi mata, tunanin ta bai gushe ba, idan kuwa harta buɗe baki ta faɗi ainihin me aka yi mata, zasu fuskanci tashin hankali.

Sosai Ta fashe da kuka Saboda tsawar da Angel ta yi mata, jikin su duk yai sanyi, ta sagar masu da gwiwa, Angel ta yi danasanin tsawar da ta daka mata, ganin yadda take ta yin kuka, ga jikinta da ke ta yin kerma yasa Angel ta miƙa mata hannu, cikin sanyin murya tace

"Am sorry bada son raina na yi maki tsawa ba, ki yi haƙuri ki daina kuka, ki zo mu shiga ciki, na yi maki alƙawarin zan taimaka maki akan duk wani abu da ya dace," hawaye jaga jaga akan fuskar Unaiza da ke kallon Angel, cikin sanyin murya tace "idan kin yi min alƙawarin zaki taimake ni inaso dani da ke mu ke6e, akwai maganar da nake son yi da ke," Jinjina kai Angel tayi alamar gamsuwa da maganar ta, sai da ta fara kallon su Deeja waɗanda ke a tsaye cirko cirko, hawaye sharkaf akan fuskokin su,
Chapter 157 · 0% Book details