← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 179

Sashe 14

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta yi mai i sarta tukunna ta shiga contact dinshi, Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira, wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya, Har ya katse kiran, ta kuma haɗa wasu numbobin ba'a ɗaga ba, kusan number waya biyar ta kira ma shi wasu ba'a ɗaga ba, Sai na ƙarshene a ka ɗaga kiran,

Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana, shiru taji ba'ace mata uffan ba, kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karaɗe kunnuwanta"who is on the line"?

Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace"Angel ce,"

Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta"kinsan dawa kike magana"?

Girgiza kai ta yi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace"a'a,"

"Ur age"? ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinya ce ƙarama,

"7yrs" voice É—in shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'?

"Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaÉ—ai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya"

"Can i call u video"?

Da sauri tace eh,

Nan take ya mayar da kiran Video call, É—ago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan ta yi picking, Bata ga komai ba a screen É—in sai duhu sosai, Amma shi wanda take wayar dashi da alama yana kallonta,

"I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale ido,

Shiru ta ji baya magana, saukowa ta yi daga saman gadon, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, Tana Cikin zagaye palour Tajiyo Sallamar daddyn ta,

A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers É—in data kira, tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci,

Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna,

"Ban fada maka bane kawai, Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana da aljanu, zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta same su tunda a nan Benazir ta haifeta, kuma kaga shi toilet madaddalar su ce,"acewar uzair,
Jinjina kai Taj ya yi"Yanzu menene mafita"?
Uzair yace"Mu tayata da addu'a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za'a dace ne,"

Taj yace"Allah Ya yarda, duk na damu wlh,"

Uzair yace"ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah zamu San abun yi,

Sun É—auki tsawon lokaci suna tattaunawa tare da uzair kafin ya yi mashi sallama ya tafi gida,

Tundaga wannan Lokacin, bai ƙara yin sakaci wurin kula da ita ba har tahfeez ya sanya ta, ya ci wahala kafin ya samu tafara zama Makarantar islamiyyar, da yake a kusa dasu makarantar take, idan ya kai ta yana barin makarantar take kamo hanya ta dawo gida, Kowa ya yi mamakin yadda a kai ta ke guduwa daga makaranta, dakyar ya samu tafara zama, tun tana yi ma shi kukan ba ta so harta haƙura ta zauna, bai ta6a bari ta zauna tana shiririta ba, Kullum sai ya tasa ta gaba tana maimaita karatun haddar da aka bata, babu abunda bai siya mata ba, Wanda ya danganci karatun addini, Cikin ikon Allah sai ga shi tafara sanya naci tana yin karatun tunkafin ma yace mata ta yi take yi, wani lokacin ko bacci take yi ta dinga sambatu kenan tana Bitar karatun da a ka koya mata, Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yi mashi ba, Uzair da aneelerh ba ƙaramar rawa suka taka ba, wurin taimaka ma taj akan angel, dama sun ɗauketa tamkar ƴar su, Allah ya bata kaifin basira,wani irin ƙoƙari gare ne ita duka boko da islamiyya ko'ina yabon ta su ke yi, Kowa sonta yake yi, duk wani Competition da za'ayi Tsakanin makarantu, ita ke ciyo ma school ɗinsu, shiyasa su kansu malaman Ji su ke da ita, duk in tayi fashi bata zo school ba, Sai sun kira taj a waya sunji dalili, sometimes har gidan suke zuwa ganinta,

A kwana a tashi ba wuya wurin Allah Angel ta shiga Cikin shekarata Goma, a wannan Lokacin suka Shirya Mata Party na taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tun ana saura kwana biyu, Aneelerh ta kai ta wurin Saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyan gaske, tare da ƙunshi na jan lalle, da ya rage saura kwana ɗaya birthday ɗin nata, gaba ɗaya suka shirya don zuwa yi mata siyayya A shopping Mall,

Kaya sosai suka siya mata a kasuwar, sai da suka gama kashe mata kuɗi, Tasa masu rigima akan Tana son a siya mata Piano da kuma drawing materials, A lokacin sunyi ƙarƙaf, sun gama kashe ƴan canjin da suka rage masu, Lallashinta su ka soma yi akan tayi haƙuri next time idan suka ta shi dawowa zasu siya mata, Ƙin yadda ta yi a ƙarshe ma ta rushe masu da kuka tana fadin ita dai su siya mata su take so, ko kuma amaida sauran kayan da aka siya mata don kuɗin su isa a siya mata Piano, sosai Angel ta sanya masu rigima, tun mutane basu lura ba, har hankalin kowa ya dawo kansu, Ganin Yadda yarinyar take ta ruskar kuka, Aneelerh taso ta siya mata, Taj ne ya hanata saboda yasan ba isassun kuɗi gareta ba.

A haka suka koma gida, Sosai ya yi mata faɗa akan ta daina yi ma shi rigima Cikin mutane, tunda yace mata ba shi da kuɗi meyasa zata takura shi, so take ta kunya ta shi a idon jama'a, daga ƙarshe yace mata ta yi hakuri idan ya samu kuɗi zai siya mata komai take so, shi kan shi baiji dadin yadda ya gaza siya mata Abubuwan da takeso ba, Don ta ƙwallafa rai a kan su sosai,

A washe garin ranar ya kasance Juma'a, ranar birthday ɗin ta, Gagarumin party suka haɗa mata, tun bayan sallar asuba aka soma shagali don a wannan lokacin ne Angel tazo duniya, Ƴan uwa da a bokan arziƙi duk sun hallara don tayata murnar birthday ɗinta, Kaya kala Uku ta sanya aranar, aneelerh ce ta shiryata ta yi mata kwalliya, Musamman aka ɗauko photographers, Su ka yi masu hotuna, taro yayi albarka Anyi kulu washrabu hani'an, Kowa ya shaida ya nishanɗantu

Angel ta samu Kyaututtuka masu yawan gaske daga wurin a bokanan aikin shi, Wasu gifts ɗinma baisan su wanene suka aiko mata dasu ba, baba mai gadi ake aikowa daga waje,ya kawo mata su cikin gidan, bakomai ya fi Ba shi mamaki ba, face wata kyuatar bazata da a kayi ma angel, Abun ya ɗaure mashi kai, Abunda angel ta kwallafa rai akan shi ne Aka samu wani ya siya mata su, piano da kuma kayan zane da ta sa masu rigima a shopping mall, Ya yi mamaki sosai har baba mai gadi ya tambaya waye ya aiko mata da gift ɗin don shi ya miƙo su Cikin gidan, Baba maigadi yace ma shi bazai Iya shaida fuskar wanda ya kawo ba, Matashin saurayi ne dai kuma ya sanya facemask a fuskar shi, Sannan kuma Acikin mota ya zo, har tambayar baba maigadi ya yi kobya lura da kofato a ƙafar mutumin daya kawo su? Baba gadi ya yi dariya Tare da cewa Bazai iya tantance ƙafafune ko kofato ba,tunda ya sanya takalma,

jikin taj dai yayi sanyi sosai, ko angel bai bari taga kayan ba, Ya 6oye su a É—aya daga Cikin É—akunnan gidan, Kafin a kammala shagalin sun ke6e da Uxair ya sanar da shi game da kayan da aka siya ma angel, shima ya yi mamakin jin hakan, Amma sai yace mashi Ya kwantar da hankalin shi, Shi yafi tunanin Cikin mutanan dake kallonsu A mall É—inne lokacin da angel tasa rigima akan su siya mata kayan, Shine aka samu wani na Allah ya siya mata su, don haka ya cire damuwa aranshi Ya bata kayanta, kada ya hanata yin amfani da su, Iya ka ci dai kafin tafara amfani da su, Ya tofe su da addu'a, kuma kada Ya dinga barinta tana yawan yin kiÉ—a, ko Æ´an zane zane sai ya dinga lura, Sosai Uzair ya ba shi shawara, Har saida yaga hankalin shi Ya kwanta,

Bayan kwana ɗaya da yin Birthday ɗin nata, Sai ga ɗan saƙo an aiko daga wurin Alhaji ubaid, Gift ne Ya aikoma jikarshi, danƙareriyar waya ƙirar i phone tare da Laptop, Bayan ya kar6esu daga hannun ɗan saƙon,Yakaisu ɗakinshi ba zato ba tsammani Sai ga alert na 1.5m ya shigo wayarshi, again daga alhaji ubaid, Ba ƙaramin farin Ciki ya yi ba, Yana ƙara Jin ƙaunar mutumin kodan saboda kyautatawar da yake yi ma ƴar shi, shi kaɗai ya damu da ita duk cikin family ɗin benazir babu wanda ya ta6a tuntu6ar shi koda a waya ne ya tambayi ya angel ta kwana, duk da yasan halin su ko lokacin auran shi da benazir dayawansu basu so ya aure ta ba, saboda arziƙin shi bai kai ya mallake ta ba, shiyasa sam babu ruwansu da abun da ya shafi tajudden, Alhaji ubaid ɗin kaɗai ne ya damu da su, kusan kullum sai ya kira don yaji ya lafiyar jikar shi,

har uzair ya tuntu6a Don su yi shawara da shi game da Kuɗin da alhaji ubaid Ya turo mashi,Yace mashi Yayi amfani da su,Wurin Gyara mata bedroom ɗinta, Inda zata koma da kwana, ya sanya mata kayan wasanni da zasu dinga ɗebe mata kewa, Sauran kuɗin Kuma Akwai hidindimu masu Zuwa, ya ajiye mata su, Duk yadda taj yaso ya ɗauki wani a bu daga Cikin kuɗin yaƙi kar6a, Sai da ƙyar ya samu ya kar6i dubu ɗari,

a tare da aneelerh suka tsara mata komai na bedroom dinta, Wani haɗaɗɗen gado suka sanya mata, Headboard ɗinshi Sak Jikin butterfly ne, Komai na bedroom ɗinta Pink Colour ne, Ba abunda ba'a sanya mata ba, Yaci wahala kafin ya samu angel ta koma kwana dakinta,Saboda sabon da su ka yi da juna, sai ya bari bacci ya ɗauketa tukunna yake kaita ɗakin ta, idan tafarka ko ƙarfe nawa ne na dare saita sauko daga Upstairs ta dawo ɗakinshi da yake ya dawo downstairs bayan sun raba daki, Sai dai kawai yaji ta Kwance ajikin shi,
Chapter 14 · 0% Book details