Sashe 6
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kanta ta daina shan nono, hakan yasa inna kuluwa ta yaye ta, a washe garin ranar da ta yaye ta, ta sanar da taj maganar komawarta ƙauyen su, ya yi mamakin jin zata tafi duk da irin rayuwar hutun da take yi agidan, Ba don yaso ba ya sallameta, kuma Yayi mata alheri sosai baiwar Allah ita kanta ba don taso ba, tabar gidan sai don zargin wani abu da take yi, Game da Ƴarshi to fah
Bayan tafiyarta kamar an ƙarama yarinyar rashin ji, har tsoro take ba taj saboda ƙarfin halinta, a kwai wani lokaci da ta addabe shi da 6arna, Sai ya dinga ɗaurata Saman Freezer dake ajiye A falo, sam ba ta so Yana ɗaura ta a sama, tun tana mashi kuka a karshe Sai gashi Idan ya daura ta da zarar Ya bar wurin sai ta faɗo kasa, Taci gaba da 6arna Abun Ya ɗaure mashi kai Yarinya sai kace aljana ranar da ta ƙure shi Keji yasa akayi mashi mai girma hada mukullin rufewa Ya sakata acikin kejin Yasa mukulli Ya rufe A tsakar falo ya ajiyeta, shi kuma Ya koma saman Sofa ya kwanta yana kallonta ranta Ya 6aci sosai tun tana gwarancin ta har takai ga fashe mashi da kuka, tausayinta Ya kamashi har baisan lokacin daya fiddo da ita daga cikin kejin ba, Ya rungumeta yana lallashin ta har ya samu tayi bacci, A daren ranar daga zuwa Yin sallar isha'e, Ya dawo ya taras Ta 6alla mashi Laptop dinshi da yake aiki da ita, idanuwan shi sukayi jawur ga shi bai iya koda yi mata tsawa ne balle aje ga bugu, A fusace ya ɗauke ta ya nufi gidan su aneelerh da ita ya kai ma Su, Yace ya basu kyauta su ruƙe ta awurin su,ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba, hannu biyu suka kar6eta ashe xaune bata ƙare ba A tunanin shi Ya samu hutu Daren Ranar bayan yayi wanka ya zura kayan baccin shi Ya kwanta cike da farin Cikin Yau zaiyi bacci hada minshari,
Wuraren ƙarfe 12:30 na dare, Can Cikin bacci Ya dinga Jin mutsu mutsun mutun ajikinshi, hakan yasa shi farkawa daga bacci, Yakai hannu ya kunna fitilar gefen gadon,
Kamar ance Ya dago karaf idanuwan shi suka sauka akan baby Angel dake kwance ajikin shi ta ƙanƙameshi, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, a firgice Yake kallonta Har wani murmu shi take sakar mashi, yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniya ba, Abun yayi mugun ɗaure mashi kai taya akai har ta yi wayon da zata iya Kamo hanya daga gidan Taj dake a jikin gidan shi ta dawo gida ƙarfe 12 da rabi na dare batare da jin tsoro ba,
Jiki a sanyaye Ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata asaman kanta, Wai koda shaidanun aljanune suka shafe ta, sae faman lumshe ido takeyi alamar bacci zata Yi,
Babu yadda ya iya haka ya ƙanƙame ta a kirjinshi Yana shafa sumar kanta, Sae gashi bacci Ya ɗauketa bada jima wa ba shima bacci Yayi awon gaba dashi.
Wuraren Sallar asuba, Uzair da aneelarh suka buga uban sammako, Hankalinsu atashe Yarinya ta 6ace, Duk sun ruɗe Suna shiga falon Gidan Suka ci karo da Taj tare da Angel zaune saman Dining Chairs Hannun shi ruƙe da Kofin tea yana bata abaki tana sha,
A ruÉ—e suka kalli Juna, saboda tsabar mamaki kafin ma Taj yayi masu bayani Uxair Ya rufe shi da faÉ—a yana cewa 'Don me zaije Ya É—auki yarinya batare daya faÉ—a masu ba, Yasa duk sun tashi hankalinsu,'sai da ya Kammala zazzaga mashi masifa,
 Tukunna Taj yace"Wlh bani na daukota ba,dakanta ta dawo,
A sukwane Aneelarh tace"Wai dagske ita tadawo da kanta"?
Kafin taj ya basu amsa angel tariga shi cewa"Eh da ƙafafuna na dawo, kuma ma baba maigadi bashi ya buɗe mun ƙopa ba, ni na buɗe dakaina" tana magana tana cije le6e kamar ƴar daba,
Tashin hankalin da ba'a sama shi date! cike da tsantsar mamaki suke kallonta, Taya akai har ta iya buɗe ƙopar da ake rufewa da key?
 Girgiza kai Taj yay "Lamarin Baby sai addu'a, Ina kwance jiya wuraren karfe sha biyu da rabi na dare naji motsin mutun ajikina a she itace ta dawo Ba ƙaramin tsorata Nayi ba"
Tabbas sun fara zargin Yarinyar tana da aljanu shiru kawai sukayi batare da sun sanar ma Taj abunda suke hasashe ba,
A daren Ranar Alhaji Ubaid Ya ƙara kawo masu ziraya, Kamar yadda ya saba duk in yana ƙasar sai ya zo, kuma duk in yazo sai ya kashe ma angel kuɗi kamar hauka kafin ya tafi,
A washe garin ranar da safe Ba zato ba tsammani Sai ga text message an tura mashi da baƙuwar Number, Benazir ce tayi saƙon Bakomai ta rubuta ba face Tana neman Saki a wurin Taj, kuma kada yayi tunanin zata dawo ta tafi kenan har abada abunda yasa ya yi farin Ciki da saƙon sanin cewa tana araye, Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba, Har bibiyar Number da ta tura saƙon yayi amma a kashe ya sameta, Yaji takaici sosai tun yana sa ran dawowar benazir cikin rayuwar shi harya fidda rai, ba don yaso ba ya tura mata da text ta number yasan wata rana dole ta buɗe ta gani, Saki ɗaya yayi mata acikin saƙon daya rubuta mata....,......
A ranar Uncle abdallah ya dawo Nigeria, Uzair ne da kan shi ya ɗaukosu a Airport zuwa gidansu, tsabar farin Ciki a wurinsu bakinsu kasa rufuwa ya yi musamman Taj, hajiya adama tayi murnar ganin su Cikin ƙoshin lafiya Ranar yini tayi da angel awurinta, tun dawowar su Angel awurun su take kwana, Bakomai yafi ba Taj mamaki ba face irin yadda yarinyar take natsuwa agaban mutane, Amma idan shi da itane tadinga 6arna kenan kamar 6eran gida,
****Boss Bature******
A kwana atashi. Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea, Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya, duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure rabuwa da ita, Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi, Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki, ko 6ari bata ta6a yi ba a bun ya dame ta sosai, Shi kan shi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa, har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu, Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi, Lokacine baiyi ba ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalin su harya basu Labarin Iyayen shi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa, Tunda suka ji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu,
A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji, Ashe Yanzu wasan Ya fara,
Tun tana da shekara Uku Ya sanyata nursery, hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata, rana ta farko da ta fara zuwa makaranta, ta samu Æ´a'Æ´an mutane ta dinga gartsa masu Cizo, Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta, saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta Saboda baza su Iya Control É—inta ba, ga shi ya hana a dukar mashi Æ´a ko tsawa Baiso Ayi mata sai dai bayan idonshi.
Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa'ƴan mutane, tun da yayi mata faɗa abunda bai ta6a Yi mata ba a ranar har fushi tayi taƙi cin abinci, daƙyar Ya lallashe ta ya samu suka shirya da ita,
Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece, tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado, a tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba, bayan fitarshi Da rabin awa ta farka tana Jin yunwa gashi Sam bata da juriyar Yunwa,
Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar ÆŠaura girki, Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din, Dama tasan Yadda yake kunneshi Saboda wasu lokuttan a tare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki, To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta.
Yana Wurin aiki Aka kira shi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi, Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan.
Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi, Duk yabi ya ruɗe babban tashin hankalin shi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta, da gudun gaske Ya fada Ciki gidan, Su uzair suka bi bayan shi dama sunzo hada aneelarh, A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo, Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi,
Sai da suka gama shan wahalar nemanta, Ba zato ba tsammani suka same ta a cikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha.
Da gudu suka nufe ta gaba É—aya suka rungumeta, kowa ya na faman sauke ajiyar Zuciya,
Abunda Ya faru a she bayan ta kunna gass, ta sauko daga saman Chair ɗin, Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha, Sam ta manta da tabar gass a kunne, duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita ba ta ji ba, Baba maigadi ne Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Ciki don yaga me ke faruwa, koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi, Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman a gaji,
Angel tasha fada awurin Taj kuma duk da laifin da tayi ma shi ko dungurin ta bai yi ba, kadan daga Cikin munanan halin angel shine, Bata barinbshi yayi bacci muddin ta farka, to shima dole ya farka baccinshi Ya qare, Idan suka fita Yawan shakatawa komai ta gani tana so, koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi idan ba haka ba hmmm xa'aga tashin Hankali, Bayan wannan Ta iya jan faÉ—a idan suka Je anguwa, komai ta gani saita dauka ta jefar, Ayita nema tana ji bata faÉ—in ita ta dauka.