Sashe 86
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Pls danish, mu koma ɗaki, " magiya ta dinga yi mashi amma yaƙi tanka mata, har ta fara tunanin ko ya yi bacci ne jin shiru, matsawa ta yi sosai kusa dashi, ta ɗan kwanto saman jikin shi tana leƙen fuskarshi, ya rufe eyes ɗinshi, kamar ya fara bacci, yanke shawarar ɗaukar shi ta yi kamar yarda ya ɗauketa jiya da ta yi fushi ta kwanta a ƙasa tsakiyar ɗakin su, Murmushi ta saki yayin da take nannaɗe hannun rigarta, tana kammalawa, ta soma kiciniyar ɗaukar shi, duk yana jin motsin hannayenta a bayanshi, wani irin nauyi ne dashi yadda kasan dutse, Ta tattara Iya ƙarfinta na ƙarshe ta ɗaɗɗago dashi, ta samu ta raba shi da saman bargon, tana ƙoƙarin Juyawa don ta nufi ɗaki dashi, wani irin nauyi Ya fisgeta, ba arziƙi ta sake shi ta rubza saman jikinshi, tana faman haki hana nishi kamar wadda tayi uban gudu, bawan Allah, kanshi ya bugu sosai, ba yadda ya iya, Jarabar angel tafi ƙarfin shi, har time ɗin bai buɗe idanuwanshi ba, bai kuma motsa ba, saboda nauyin jikinta dake asaman nashi, Babu alamun zata ɗaga shi, ta kifa kanta saman kirjinshi, sumar kanta duk ta tarwatse, slowly ya ɗan ware idanuwan shi, ya ɗaurasu akan sumar kanta, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta""An..gel" Ƙasa ƙasa ya furta sunan, bata amsa mashi ba. Kuma bata ɗago ba, ranshi ne ya bashi cewar kodai tayi bacci ne
Zagayo da hannayen shi yae saman bayanta, a wannan yanayin bacci ya yi awon gaba su, manne da juna,
A washe gari
Haris ne ya fara farkawa daga Bacci, Cikin buƙatar zuwa toilet, Saukowa Ya yi daga saman gadonshi ya nufi toilet yana hamma tare da yin miƙa duk a lokaci ɗaya, Zura ƙafar shi keda wuya ya yi arba da su angel dake a kwance saman bargon danish, sun ƙanƙame juna suna bacci, Yadda kasan tip da tyre, Tsabar mamaki ne ya kama dashi, har wani leƙen su yake yi don ya gane ma idonshi da kyau, hada sanya hannu ya ruƙe ha6arshi, can kuma sai ya saki murmushi, Mutumin da ke jin fitsari maimakon ya shiga toilet, Sai ya juya saboda gulmar data ciyo shi, Jikin shi har rawa yake Yi, wurin komawa cikin ɗakin, agaban gadajensu Javed, Yaje yana tashin su daga bacci, ɗaya baya ɗaya ya dinga tada su, Kowa Ya mike yana miƙa da hamma tare da tambayar shi lafiya? Yace musu Su zo suga wani abun ban mamaki, Koda jin haka jiki na rawa, Kusan atare suka sauko daga saman beds ɗinsu, lokacin da su batool suka shiga, Suna Yin arba dasu Danish manne da juna, Kowa Ya buɗe baki haɗi da zare ido, Kamar sun samu tv, A kewaye da shimfidar Suka zuƙunna suna kallonsu, Yayin da su masu baccin basu san wainar da ake toya ba,
Angel ce ta fara farkawa, A hankali ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, ras taji gaban ta ya faɗi ganinta ajikin danish, sam ta manta meya faru jiya, waro ido ta ɗanyi tare da sanya tafin hannunta ta rufe bakinta, Gyaran miryar Da haris yai mata ne yasa tayi wuff ta sauka daga saman jikin danish ta koma gefe ɗaya, Ta yi tunanin zata ga haris shi kaɗai amma sai ta gansu kaf ɗinsu kewaye dasu, Tawaga guda, sun baza na mazurinsu suna kallon Ikon Allah, Muryarta na in ina tace"Am..kun..gane..jiya..um" bata ƙarasa maganar ba, Batool tace"Ai mun riga mun gane komai ba sai kin yi mana bayani ba," azeeza tace"ƙwarai kuwa, Aljanu ne suka kawo ku nan, koba haka ba"? Ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu Hannah, har suna haɗa baki wurin cewa eh, wani kallon rainin wayau taga suna Yi mata, Kafin ta ƙara furta wani abu, danish ya farka yana kokarin buɗe idanuwanshi, Biji biji yake iya ganinsu, Haris yakai hannu ya bugi ƙafarshi"tashi ka yi mana bayani, meya faru a daren jiya," gaba ɗaya jikin shi kasala yake Ji, Yunƙurawa Yayi tare da miƙe wa zaune, a lokacin idanuwan nashi sun washe yana ganinsu, One by one ya dinga binsu da kallo, sai wani sakin murmushi suke Yi kamar sabbin mahaukata, ɗauke eyes ɗinshi yae daga kan fuskokinsu, Ya mayar dasu kan angel da tayi wuƙi wuƙi da ido, Suna haɗa ido dashi, ta fara zazzaga mashi masifa"Duk kai kaja mini ina zaman zaman lafiyata, Tun farko basai da nace Ka koma ɗaki ka kwanta ba amma saboda kafiya irin naka kaƙi jin maganata, Ka nace saika kwana anan, Ni banma yarda dakai ba, kaine ka janyo ni jikinka, har bacci ya ɗauke ni, saboda rashin tsoron Allah, gashi kaja min zunubi," tun da tafara faɗa suka zuba mata ido suna kallonta, Ita fa gani take kamar suna zargin wani abu, yayin da su kuma basu kawo komai aransu ba, saboda ilminsu bai kai nan ba, Abun ma burgesu Yayi, don su a wurinsu ba wani bane don mace ta haɗa jikinta dana namiji, sun saba ba tun yanzu ba, saboda haka suka taso suna rungumar junansu, abu ɗaya ne basu yi neman junansu, shima saboda basu da shauƙin sha'awa kwata kwata, an cire masu shi, amma fa suna ƙaunar junansu sosai, sai ma mutun ya yi tsammanin akwai soyayya asakaninsu, Alhalin nan kowa babu wannan aransu, Kawai ƙaunar juna ce,
"Angel ki daina ƴan kame kame, Mun riga mun san komai," harara ta jefa ma hanna da ta yi maganar tace"Me kuka sani? Idan ma wani abu ku ke zargi to shine ke da laifi ku tambaye shi ku ji,"a ƙule tayi maganar, shi dai baice komai ba, idonshi na akan fuskarta,
Parveen tace"danish ka faÉ—a mana gaskiyar abunda ya faru? Dagaske ne Kaine silar komai? ÆŠaga mata kai yayi alamar eh, saboda gudun jarabar angel,
Javed yace"Ni ban yarda ba, Nafi zargin Angel, Cos danish bazai ta6a kawo ki nan ba, sai dai ko kece kika biyo shi, wama ya sani ko faɗa ne ya haɗa ku, " miƙewa tsaye angel tayi"Ni kun ga tafiya, Ina da abun yi" Takai karshen maganar tare da Juyawa ta Nufi toilet ta buɗe ta shige, Jamlock ta sanya ta datse ƙopar, kafin ta le6e tana sauraron me suke cewa,
"Danish faɗa mana gaskiya, Meya faru daren Jiya a tsakaninku? Ya akai kuka baro ɗaki kuka dawo nan"? Batool ce ta jera mashi tambayoyin, angel dake la6e ta yatsina fuska aranta tace"Wannan batool ɗin sai kace ƴar jarida, ko ina ruwansu da abunda ya faru adaren jiya in ban da gulma da son jin kwakwaf mtsww"taja tsaki daga ƙarshe,
Tana Jinsu suna ta tambayarshi ya faɗa musu, Amma yaƙi basu amsa sai dai ce musu ya yi, ya manta komai, bazai iya tunawa ba, dole suka haƙura da tambayarshi, Ajiyar zuciya angel ta sauke, a fili tace yayi ma kanshi ƙiyamul laili, dama Bata son ya faɗi ne don kada ajinta ya zube, su ji cewa itace ta biyo shi don ta ba shi haƙuri,
Bata fito daga Cikin toilet ɗin ba, sai da ta yi wanka, A waje ta samu Su haris suna Jiran Na cikin toilets ɗin su fito su ma su shiga ko sun samu su yi wanka, Wuce su ta yi zuwa Cikin ɗakin, Babu kowa duk suna a can sai ita kaɗai, daga gefen gadonta ta zauna, bakomai ya faɗo mata acikin ranta ba face Deeja, Ko awani hali take ciki yanzu Allah wa'alamu, ɗaga hannayenta sama tayi cikin harshen labarabci ta soma jero addu'o'i tana karanto da niyar Allah ya tsare musu ƴar uwarsu, tana Cikin Yin addu'ar taji yo motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, da sauri takarasa shafa addu'ar, Ta juya tana kallon ƙopar, tsohuwa ta fito daga cikin ɗakin, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a harmutse baka Iya gane awani yanayi take, haɗa ido su ka yi da angel, da buɗar bakinta sai cewa ta yi"Ba zaki zo ki gaishe ni ba"? Murguɗa mata baki angel ta yi tare da cewa"Mutanan kirki nake gaisarwa, ba masu matattar zuciya ba" bazawarin murmushi tsohuwa tasaki, haɗi da girgixa kai tace"kin tsane ni kamar mutuwarki" angel tace"fiye da haka" dariya tsohuwa tayi,
"Idan ba ki son ganina to ki kwantar da hankalinki, nan badajimwa ba, Zaku daina gani na," babu yabo ba fallasa angel tace"Da munji daɗi wlh, kwara mu daina ganinki, tun da dama babu amfanin da kike yi mana, sai sai kawai kullum ki leƙo da ƴar sanda a hannu," wannan maganar ta angel ba ƙaramar dariya ta bata ba, Musamman data kwatanta yadda tsohuwa ke leƙo wa da kanta,
"Ba zaki yi kewata ba"? Ta jefa mata tambaya, angel tace"Kin ta6a ganin anyi kewar maƙiyi? To idan ma ana yi ni bansani ba, Ni dai burina shine ki fita arayuwar mu, saboda baki da amfani, " hannu takai ta ɗauki pillow Ta ɗago dashi tana nuna ma tsohuwa tace"Kinga wannan matashin kan na hannu na? wlh yafi ki amfani yafi ki daraja da ƙima a wurin mu, ai ke dake da waccan tukunyar fulawar ta Cikin toilet ɗin mu baku da banbanci,"
Tuntsirewa tsohuwa ta yi da wata irin mahaukaciyar dariya hhhhhhhh, da gudu su Hannah suka shigo cikin ɗakin sakamon Jin sautin dariyar tsohuwa wanda yajawo hankalinsu, A tsakiyar ɗakin suka tsaitsaya suna Kallonta, Ɗauke ido tsohuwa tayi daga kan angel ta mayar dasu kansu Batool tace"Kuma bazaku gaishe ni ba"? Maimakon su gaishe ta, Sai suka juya suna kallon angel, Tsohuwa tace"ba shakka, Uwarku kuke Jira ta baku Umarni kenan"? Shiru suka Yi basu ce mata komai ba, Still idonsu na akan angel data maƙe musu kafaɗa alamar kada su gaishe da ta ita, Shigowa cikin ɗakin mazan su ka yi gaba ɗayansu duk sun yi wanka, Suna ƙarasowa inda tsohuwa take, cikin girmamawa Danish Ya ɗan russuna tare da gaishe da ita, hakan ba ƙaramin fusata Angel yayi ba, har saida taja dogon tsoki,