← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 179

Sashe 31

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sambatu take ta faman yi, Cikin fitar hayyaci, tarasa gane inda take, Ko'ina duhu, babu haske ko misƙala Zarratin, jikinta yayi mata wani irin nauyi tamkar an ɗaura mata dutse a samanta, Ko yatsan ta ta gaza ɗagawa, Wani baƙon yanayi da bata ta6a jin kanta acikin shi ba, ga zafi ta ko'ina, numfashin ta kanshi daƙyar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu'a da tazo bakin ta, Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haɗa uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda ƙuncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faɗin"Wai ba kowa ne a kusa, Ku faɗamun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta ya bushe ƙamas, Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta, Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo, tamkar hostel na kwanan ɗalibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je da a ka yi su da Metal(ƙarfe) A ƙalla sun kai goma sha biyar, single bed ne na mutun ɗaya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a ɗaya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta ɗakin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da Katako zubin armchairs guda biyu dake ajiye, agaban kujerun there's a table an ɗaura wasu fitilun kusan uku a saman shi, daga tsakiyar ɗakin akwai shimfiɗaɗɗen red carpet, Saukowa Tayi daga saman gadon Cike da fargaba take kallon baƙon wurin da ta tsinci kanta a cikin shi, juyawa tayi tana kallon bayanta bene ne madaidaici, da alama akwai ƙopa a can saman stairs ɗin, Amma daga inda take tsaye bata iya hangen ƙopar ta yi lungu, Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su akan ƙopar dake a rufe, saman ƙopar taga an rubuta "Toilet" nan take ta gane makewayi ne, ɗakin yana da tagogi both left and right na jikin bango amma an garƙame su, ginin da alama tsohon gini ne aka sabunta shi, A ruɗe take zazzare gray eyes ɗinta da suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, long eye lashes ɗinta duk sun cukurkuɗe, dogon hancinta yayi jawur da shi saboda matsar da ya sha lokacin da take ku ka, heart shaped lips ɗinta sunyi light pink sun bushe ƙamas, gaba ɗaya ta rikice musamman da ta shafa jikin ta, a hautsine ta kalli uniform ɗin da aka sanya mata, launin baƙaƙe zaro ido tayi ganin an canza mata kaya ita a iya saninta kayan fulani ne ajikin ta lokacin da ta gudo daga hannun fulanin daji, hatta kanta kitson kalaba ne da danejo ta yi mata amma yanzu an warware mata kitson an sakar mata gashin ga shi nan a haukace har kusan waist ɗinta ya yi mata tamkar hijabi, uniform ɗin jikinta riga ce me dogon hannu takai mata har guiwarta, sai dogon wando har kasa, a bayan rigar an rubuta no 1, Juyawa ta yi da gudun gaske ta nufi benan nan, a zafafe take tattaka matattakalar har takai bakin ƙopar sai dai a garƙame take an rufe ta, Hankali a matuƙar tashe ta dunga bubbuga ƙopar tuntana yi a hankali tana tambayar bakowa ne anan har takai ga kai ma ƙopar naushi ta ƙafa ta hannu, tamkar ƴar dambe duk ta raunata jikin ta, Saboda ƙopar ta metal ce, Jiri ta fara gani acikin idanuwanta ba arziƙi ta dakata tana fama mayar da numfashi, zufa ta ko'ina a kan fuskarta, Jingina bayanta ta yi a jikin hand rail ɗin benan a galabaice, ga uwar yunwa tana ji kamar tacin ye ƴan hanjin cikinta, Tana cikin wannan yanayin ta jiyo motsin tafiyar mutane can kuma taji alamun ana buɗe ƙopar ɗakin da take ciki, a hanzarce ta wurga eye balls ɗin ta kan ƙopar tana jira taga wata ja'irar ce ko wani ja'irin ne xai shigo, domin kuwa ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wanda ya yi silar ɗauko ta daga saman titi ya kawota wannan wurin mai kama da prison. Cikin ƙanƙanin lokaci aka buɗe ƙopar tare da turo ta, awani slow angel ke kallon ƙafar mutanan da suke ƙoƙarin shigowa ciki, wasu gabza gabza Mutanene masu tsayi da faffaɗan ƙirji, Wata kalar ƙira gare su mai ban tsoro kowannan su na a cikin Shiga ta baƙaƙen kaya long coat har guiwa sai dogon wando, sunyi 6adda kama ta yadda ko akaifar hannunsu baka iya gani, sun sanya mask a fuskokin su, Sun 6oye ainihin halittar su, ƙafafuwansu kuwa Army boots ne suka sanya, kawunansu na sanye da cowboy hat, dai dai da ziririn gashin kansu baka iya gani ko'ina arufe ya ke, motsa lips ɗinta ta soma yi da niyar ta yi magana sai dai kafin ta yi yunƙurin furta wani a bu, idanuwanta suka sauka akan ƙafar matashin saurayin da ke ƙoƙarin shigowa, kalar uniform ɗinta ne ajikinshi baƙaƙe masu ɗauke da No 1 A halitta dogo ne fari sol da shi, kyakkyawan gaske, Droopy eyes ɗin shi farare ƙyal da su, Yana da dogon hanci, full lip ɗinsa red colour ne, yana da dimple ɗaya a gefen fuskar shi wanda ko motsa lips ɗinsa ya yi sai ya lotsa, Yana da yalwatacciyar sumar kai, ta kwanta luf har mid back ɗinsa dark brown saboda tsabar kyanshi sai ka rantse da Allah maca ce ba namiji ba, ta yi tunanin shi kaɗai ne wuce warshi ke da wuya, sai ga wata matashiyar budurwa me sanye da black uniform no 2, itama fara ce sosai doguwa kamar angel tana da manyan idanuwa ga dogon hanci, soft lips ɗinta brownish colour ne, tana da yawan gashi ya cika kanta kamar an kifa mata kwando, tsayin shi ya haura kafadarta, Tana ƙarasa saukowa sai ga wasu matasan ƴan mata masu sanye da red uniform kowanne da numbers a bayan rigar shi, gasu nan kala kala wasu baƙake wasu farare wasu wankan tarwaɗa, kamar yadda angel ke kallonsu haka suma suke binta dana mujiya, A kalla mata sunkai goma acikinsu maxa kuma biyar, sai da suka kammala shigowa tukunna waɗannan GIANTS ɗin su ka fuce daga ɗakin bayan sunyi locking ƙopar, Cikin tashin hankali angel ke bin kowannan su da kallo, can dai tace"wai uban wanene ya kawo ni wannan wurin! Menene alaƙata da ku!"nuna matasan ƴan matan ta yi da yatsan hannunta "ku faɗamun su wanene ku?kuma ina ne wurin nan? kun wani tsare ni da ido kuna kallo na" a harzuƙe ta yi maganar, ɗaya daga cikinsu ce wannan me black uniform no 3 ta soma magana cikin harshen turanci"kamar yadda kika tsinci kanki a cikinsa batare da sanin ki ba, mu ma haka muka tsinci kan mu, abu ɗaya na sani shi ne, kurkukun ƙaddara gida ne na marayu wanda basu da gata,' girgiza kai angel ta yi'ae ni ba marainiya ba ce, iyaye na suna araye wlh bazan zauna acikin kurkukun nan ba, i must find away to leave........" kafin takai ƙarshen xancen nata wata matashiya me ɗauke da uniform jajaye no 4 baƙa siririya tace"ba gidan cutarwa bane, gidan taimakon marayu ne zasu tallafi rayuwarki, dayawa ma anan aka rainesu tunkafin su mallaki hankalinsu, xamu samu kulawa tunda bamu da kowa kurkukun ƙaddara shi ne gidanmu" Uwar harara angel ta wurga mata"prison will neve be a home for me, ba zan ta6a lamunta ba, taya za'a sato mutun akawo shi wani baƙon wuri sannan ace gidan marayu ne? Ta gidan ubanwa aka gaya masu cewa ni marainiya ce, da uwata da ubana kuma da dangina, ba daga sama na faɗo ba," yadda take magana rai a6ace har wani huci ke fita daga cikin bakinta, Takun tafiya suka jiyo daga cikin ɗakin muryar wata tsohuwa tukuf suka jiyo tana faɗin"Ina Magana"da hanzari dukansu suka sauka daga saman benan xuwa cikin ɗakin hada angel, Tsayawa su kayi idanuwansu akan tsohuwar, a tsaye take jikinta na sanye da doguwar riga mai gashi gashi ajikinta, launin ja hannunta na ruƙe da sanda fara ce tass ta tsufa tukuf idanuwanta duk sun zurma, fuskarta ta yi uban tamoji tamoji, kanta babu gashi ko ɗaya da yake baƙi, gaba ɗaya uwar hurhurace hatta jagirarta hurhura duk ta kamata, hada gemu gare ta fari fatt yadda kasan namiji, ga wani katon hanci dake gare ta, uban gi6in dake abakinta yadda kasan ƙogon dutse, haƙora huɗu kaɗai suka rage abakinta na sama dana ƙasa, can cikin kursurwar bakinta, dogayen haƙora ne ko ta rufe baki sai na saman sun leƙo waje, hannayenta kuwa xaƙo zaƙon akaifu ne haka ƙafafuwanta wasu tsoffin takalma ne launi rigarta jajaye, kunnuwanta falo falo an manna masu bari ma, Mamaki ne ƙarara akan fuskan angel, ta ya akai tsohuwar ta shigo cikin ɗakin batare da ta biyo ta ainihin ƙopar shigowa cikinsa ba? To kodai ta saman rufi ta duro ne ?ko kuwa bango ta tsaga ta shigo? Kamar daga sama angel ta ji tsohuwar tace"ko ɗaya! ta ƙopa na shigo ciki" ta yi maganar tare da juyawa tana nuna mata wata ƙopa dake a ɗaya daga cikin kusurwowin ɗakin, "Nan ɗaki na ya ke, Ni tamkar uwa nake awurin ku, dayawa sunsan wacece ni saboda na shayar da wasun ku, wasu kuma na rainesu kamar DANISH da
Chapter 31 · 0% Book details