← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 179

Sashe 11

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameen mutumina"
Shiru suka É—anyi,yana so ya tambaye shi aneelerh amma ya kasa,
"Muyi video call mana"acewar uzair,
Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call, A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu, ya dan tada kan shi saman pillow, jikin shi na sanye da kayan Bacci,
"Show me her face" murmushi taj ya yi tare da haska mashi fuskar angel, ta sa ki baki da hanci tana ta sharar bacci,
Dariya uzair yayi"waya ga mashasha, wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a, a haka zata zama surukar mu,"
Fuskar Uzair É—auke da murmu shi yace"cin mutuncin ya isa haka aminina, kai ka sani Wlh angel koda kuÉ—in mutun saida rabon shi, koda rabon shi sai in Allah ya nufa"
Jinjina kai Uzair Yayi tare da É—an yatsina fuska yace"Virus É—in"?
Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani, adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet, Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya, Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakin shi baya, wanda hakan yasa har Taj ya iya hango fitowarta,

Baisan ya a kai ba Ya tsinci kanshi da satar kallonta, Ya bar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daÉ—i, gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel,

"Me kake tunani ne"? a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair, muryar shi na inda inda yace"Bakomai zan kwanta mutumina, Sae Allah yakaimu," da sauri ya yi rejecting kiran tunkafin ma uzair ya yi mashi sallama,

Lumshe idanuwan shi ya yi zuciyar shi a cunkushe, duk yadda yaso Ya hana kan shi tunanin abunda ya faru tsakanin shi da aneelerh abun ya faskara, daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba da shi,

Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba, koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakanin su, mutu ka raba takalmin kaza, tabbas Angel taba kowa mamaki, irin yadda take son mahaifinta, tarairayarshi take yi, biyayya take yi mashi sau da ƙafa, Xaman Lafiya ya wanzu a tsakanin su.

A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki, dawowar shi ke nan daga masallaci, ya ɗan tsaya sauraron wa'azi, jikin shi na a sanye da jallabiya ash colour, da sauri ya nufi bedroom ɗinsa, Da sallama a bakin shi ya shiga, tunkafin ya ƙarasa shiga ya same ta a kwance tsakiyar gado tana ta sharar baccin ta hada minshari, Agogo ya kalla shida ta kusa, ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin ya yi a gefen gadon ya zauna, tare da ɗan juyo wa yana kallonta, tayi ɗai ɗai a saman gadon, Kayan baccin da ya sanya mata jiya sune a jikinta riga da wando blue sky, curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe,

a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancin ta, yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba,
"Wake up My lovely daughter" Cikin kunne yayi mata raÉ—a,
BuÉ—e gray eyes É—inta ta É—anyi slowly tana kallon fuskar shi biji biji,
"Nauyin bacci ko? Oya wake up, kada muyi late, ki tashi inyi maki wanka, in girka maki abinci mu ci mu ƙoshi, kafin na sauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina

Jin tayi shiru ba ta ce komai ba, yasa shi fara Yi mata cakulkulo, lokaci guda ta 6a66ake da dariya, white teeth É—inta kamar gonar auduga, saboda tsabar kyau, kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda hasken su,

Sosai ya sanya ta nishaɗi, a ƙarshe Ya ɗauke ta saman kafadar shi Ya nufi toilet da ita, almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayan shi, Ya ɗaura mata towel ajikinta,

A saman mirror chair ya zaunar da ita, Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin, Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu, runtse ido tayi tana dariya mirmishi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura, zura hannun shi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da gashin, Bayan Ya kammala ya kashe dryer din, ya mayar da ita inda ya ɗaukota, ya kuma ɗauko Comb,Ya shiga sharce mata gashin, Sai faman sakin murmushi take yi, A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci?

ta cikin mirror taj ke kallonta, ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu ta ke tunani, Man gashin ta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata, Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta da ke a jiye gaban mirror din, Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta, Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse, Yawan gashi ne da ita ga tsayi, don a yanzu gashin ta ya kai mid back ɗinta, sai da taj yayi da gaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi,

"Daddy ni da kai wa ya fi kyau" ta yi tambayar tana sakar ma mirmishi
Dungurin kanta yayi"Kinfi kowa sani ae" ya yi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu, Hannu yasa ya buɗe murfin, Jerin kayan sawan shi ne da kayanta, Uniform ɗinta Ya ɗauko mata riga fara sai mini skirt red colour, Abaya fara ƴar short, a yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta, ga wayau da Allah ya yi mata uwa dila agari,

bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare, Ya zaunar da ita gefen gado"Am coming now" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta, madara ce me sanyi Acikin roba, tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips,
Ajiye mata yayi a gefen gadon, Shaf shaf ya shige toilet Yayi wanka, Ya fito sanye da short, zuba mashi ido ta yi tana kallon shi,.
Harara ya É—an jefa mata"Zansa kaya"
ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi, tamkar bata ji me yace ba,
Gyaran murya yayi mata"Can't u hear me? Ki koma Falo inaso zan shirya".
Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace"Amma ae ni har wanka ka ke yi mun, kuma kana ganina ba kaya, Amma ni kullum sai ka kore ni in zaka sanya kaya'

Tashin Sense, zaro ido waje ya yi yana kallon ta Cike da mamaki, Ya ma rasa gane wai me take nufi, sai lokacin ya gane kuskuran sa na rashin É—aukar mai aikin da zata dinga kular ma shi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin,

"Angel don't waste my time, Oya hold ur basket, ki jira ni a falo,"
Ganin ya É—aure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket É—inta ta fuce falo, Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa, Bayan ya kammala shiryawa cikin suit, Ya fito daga É—akin Ya nufe ta, Hannunta ya kama suka fito daga falon,

Baba maigadi ya samu, A harabar ajiye motocinshi, Yana goge ma shi motar da zai fita da ita,

Tunkafin su ƙarasa baba maigadi ke ta faman washe ma angel baki, ita kuwa ta tsuke fuska, Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san ta yi kyau, Daƙyar ta ke ma mutane magana,

Suna ƙarasowa bakin motar, Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa, kafin Ya kalli angel"Ƴan mata makaranta za'a tafi"?
ÆŠaga mashi kai tayi alamar eh"
"Allah ya bada sa'a Angelata"maƙe mashi kafaɗa ta yi"Ni ta daddy ce"dariya su ka yi gaba ɗayansu,

Taj yace"Bari mu wuce kada mu makara" baba maigadi yace "Allah ya tsare adawo lpy" ya amsa ma shi da ameen kafin ya buÉ—e mata motar ta shiga ciki, ya zagaya ta left hand, ya buÉ—e ya zauna a driver seat,

A tsanake Yayi ma motar key, tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin, da sauri baba mai gadi Ya riga shi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin, Ya fuce daga gidan,

A hankali yake driving, Ta wutsiyar idonshi ya kalleta, Ta natsu ta kame kanta,
"Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa"
"Ba bacci nake ba,Ina tunani ne"
"Daddy wlh ni banaso mu rabu, dama ka dinga tafiya dani wurin aikin ku"
Murmushi ya ɗan saki"Karatun naki fa"?y ayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana,
Shiru bata amsa mashi ba,
"Ni inaso ki yi karatu angel, sai da ilmi ita kanta rayuwa ta ke yin kyau, ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane za su yi alfahari dake"?

"Inaso" ta amshi amsa a takaice,
"To faÉ—amun me kikeso ki zama"?
Da buÉ—ar bakin ta sai cewa tayi"house wife" ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba, zuba ma shi ido ta yi tana kallonshi, fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske ta yi maganar,
"Daddy why are u laughing? did i say something wrong"?
Girgiza kai yayi"a'a,May be u did'nt understand my question, Ina nufin wani aiki ki ke son Yi idan kika girma, a aikin gomnati? ya yi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar, Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin, A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar,
Chapter 11 · 0% Book details