Sashe 96
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryar azeeza cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah batool ki yafe ni wlh bada son raina na gartsa maki cizo ba, ke ce kika shaƙe mini wuyan rigata har naji zafi na cije ki," wani irin jiri batool take gani acikin idanuwanta, biji biji take bin kowannan su da kallo, Angel tace"Batool meke damunki? Wai baza ku faɗa mana me ya haɗa ku ba? Meyasa ku ke yin kuka? Ga zufa duk ta wanke jikin ku," matsawa batool ta yi kusa da angel ta kwantar da kanta saman kafaɗarta, da sauri angel ta sanya hannayenta biyu ta rungumeta sosai ajikinta, cikin muryar kuka batool ta zayyane musu abunda ke faruwa, Hankalinsu yayi matuƙar tashi, deeja dake a gefen haris ta fashe da kuka tana faɗin"mun shiga uku, abunda nake gudu sai da ya faru, wannan wace irin masiface? Fuskarta a yamutse takai kai ƙarshen maganar, haris yace"gaskiya bazaiyiyuwa ba, nidai bazan bari atafi da wani daga Cikin ku ba, sai dai a haɗa dani," cigaba da magana deeja tayi yayin da hawaye ke bin fuskarta tace"Dan Allah mu hada kanmu, wannan karan kada mu bari atafi da ƴan uwan mu, ina matuƙar tausayin azeeza da batool, bazan so su ɗanɗani irin raɗaɗin azabar da muka sha ba, musamman azeeza zamu iya rasata," maganar deeja ba ƙaramin tsorata azeeza ta yi ba, jikinta ya hau 6ari, haƙoranta har kakarwa suke yi kamar wadda sanyi ya kamata, da sauri javed ya janyota jikinshi, kamar jira take yi dama ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka, lallashinta ya shiga yi, yana ɗan bubbuga bayanta da hannun shi,
Zuciyoyinsu duk sun karaya, Fuskar Rubina É—auke da matsananciyar damuwa tace"Wai shin Jinin wanene acikin su? Ta ya zamu iya ganewa? É—agowa azeeza ta yi daga jikin javed tana faÉ—in"I just know it's not my blood, wlh ba jini na ba ne, sai da na faÉ—a ma batool cewa banawa bane, Saboda ni ko da na shiga toilet É—in ban kai ga cire wandona ba, na yi tozali da shi"
cikin shessheƙar kuka batool tace"Nima banawa bane, ba daga jikina yake ba, har na shiga na fito daga Cikin toilet ɗin ban ganshi ba" koda batool tae maganar bata raba jikinta daga na angel ba, ta ƙanƙameta, ji take kamar in ta raba jikinta daga nata za'a zo arabasu ne,
Hawaye ne masu É—umi suka wanke fuskar angel. Har cikin zuciyarta tana jin wani irin mummunan faÉ—uwar gaba, muryar na É—an rawa ta ambaci sunayensu Batool azeeza, "duk suka natsu, suna jiran jin me zata ce musu,
"Since we were all confused, we couldn't figure out whose blood was in the toilet, abunda yakamata muyi zamu shiga toilet ɗin mu duba jinin da kyau, idan muka tabbatar jini ne, Azeeza da batool kowannan ku zai shiga cikin toilet ya bincika jikin shi, ta hakanne kaɗai zamu Iya gane daga jikin wa jinin ya ɗigo" gaba ɗaya kowa yayi amanna da maganar angel, koda suka shiga toilet ɗin suka duba dakyau, jini suka gani har ya ɗan bushe a ƙasa, Hankalinsu ya ƙara tashi, angel tace abunda ya rage yanzu, su shiga su duba jikinsu, Batare da 6ata lokaci ba, azeeza da batool suka shiga cikin toilet, kusan atare suka fito daga Ciki, Har suna haɗa baki wurin faɗi "Ba daga jiki na yake ba" Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, To wai jinin wanene toh? dole dai acikinsu ne wani ya zubar dashi, kuma azeeza ta tabbatar musu da cewa sabon Jini ne, domin kuwa lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin, da ruwa ruwa jikinshi, kafin yakai ga bushewa,
Kowannan su ya shiga ruɗani, in a low voice danish yace"ku daina wahalar da kanku, Idan ma dagaske jinin ne, Giants ne zasu banbance wanene acikin su," harara angel ta watsa mashi tare da cewa"danish har fata kake yi azo a ɗauke su"? duƙar da kanshi ƙasa yai batare daya bata amsa ba, haris yace"yanzu duk ba wannan ba, ku zo mu koma ɗaki mu jira mu gani me zai biyo baya" muryar azeeza a rauna ce take fadin"Ni wlh bazan fita daga nan ba, ku rufa mana asiri mu yi zaman mu acikin toilet mu datse ƙopar, ta yadda ba zasu Iya shigo wa su ɗauke mu ba" la66anta har shaking suke yi saboda tsabar firgici.
Tsananin tausayin su ne ya kama ƴan uwansu, haris yace"Azeeza ta kawo shawara mai kyau, mu rufe su kawai acikin toilet, kun ga shikenan munyi maganin Giants ba zasu Iya shiga su ɗauke su ba" Jinjina kai angel ta ɗanyi alamar gamsuwa da bayanin Haris, ta ƙara da cewa"Ni zan zauna a atare dasu cikin toilet ɗin"
Girgiza kai danish yayi yana binsu da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa yace"that cannot be possible, if you say you will stop the giant from taking her you'll bite off more than u can chew........." daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da suke watsa mashi asaman fuskarshi, Tsabar takaici ya hana Haris furta komai, Sai angel ce tai ƙoƙarin cewa"Kome zamu yi be shafe ka ba danish, u should stay away from us, tun da ba ka supporting ɗin mu that's mean baka da amfani awurin mu, ka koma saman gado ka kwanta zai fi maka kwanciyar hankali. If not wlh zan yi maka abunda baka tsammani," angel na rufe baki deeja tace"Danish baya atare damu, na fara zargin cewa Yana atare dasu, shiyasa ko jiya da aka dawo dani duk irin baƙar wahala dana sha, Kowa Yana yi mini sannu duk da bata maganin ciwo amma ina ji daɗi, atlease ƴan uwana sun nuna sun damu dani sun yi kewata, amma danish ko kusa dani baizo ba, sai kace wata maƙiyiyar shi.
hawaye na bin fuskar deeja takarasa maganar, Ran haris ya 6aci sosai, a fusace ya kai hannun shi ya damƙi damtsen hannun danish ya fusgo shi ya ja shi da ƙarfi ya fitar dashi daga cikin sashen toilet din. har cikin ɗakin su bakin gadon shi ya kawo shi, anan ya dakata Ya ɗago suna kallon juna ido cikin ido shi da danish,
"Ba ka da amfani a wurin mu, duk da haka bawai ina gudun ka bane, ko Ina fushi dakai a'a ko ɗaya, har yanzu kana nan a yadda kake cikin zuciyata, sai dai bama buƙatar ka a halin da muke ciki yanzu, Gado shi ne ya dace dakai ka hau ka kwanta" ya ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki, kafin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin. Jikin danish ya yi sanyi, slowly ya ɗan juya baya yana kallon haris dake ta sauri har sai da ya shiga ƙopar tukunna danish ya ɗauke idonshi daga kallon bayan nashi da yake yi,
Kamar yadda suka ce ya hau saman gado, aikuwa gadon ya haye ya kwantar da kanshi saman pillow, shi kaÉ—ai yasan irin raÉ—aÉ—in da yake ji acikin zuciyarshi, ganin yadda Æ´an uwanshi suke nuna rashin amfanin shi acikin su, abun yana mishi ciwo acikin zuciyarshi. Daurewa kawai yake yi dan ba yadda zaiyi,
Bayan haris Ya koma cikin toilet É—in, atare da angel suka tsara yadda zasu shirya ma Giants don su hana atafi da Æ´an uwansu, Bayin Allah sun damu da Æ´an uwansu sosai, babu mai tunanin abinci acikinsu ba don basu jin yunwa ba, sai dan damuwar da suka shiga, na fargabar kada azo a É—aukar musu Æ´an uwansu,
Haris ne yace da angel ta shiga Cikin toilet ita da batool su datse ƙopar ta yadda giant ba zasu Iya shiga Ciki ba. ita kuma azeeza a ƙarƙashin gado zasu 6oye ta, hanna tace ae zasu Iya gano azeeza tunda suna kallon komai suke Yi, amma ita a ganinta, abar azeeza ta shiga cikin toilet ɗin tare dasu angel, Haris yace su yi hakan kawai, toilet ɗin ƙarshe suka buɗe angel da su azeeza suka shiga Ciki, kafin su rufe ƙofa haris yace"su kwantar da hankalin su, idan an kawo abinci zasu kawo musu nasu su ci," suka amsa mashi da toh, daga bisani angel ta datse ƙopar da Jam lock,
Kallon juna suka shiga yi atsakaninta dasu azeeza dake a tsaitsaye, fuskokinsu sharkaf da hawaye, sam babu kwanciyar hankali atare dasu,
Tsananin tausayinsu ne ya kamata, gaba É—aya ta sanya hannayenta biyu ta rungumesu ajikinta, Cikin sigar lallashi take Yi musu magana,
"In sha Allah giants bazasu raba mu da ku ba, bazan bari a cutar mini da ku ba, ina ji ina gani, wlh sai inda ƙarfi na ya ƙare, koda kuwa zan rasa raina ne, amma wannan karan ashirye nake dana fuskanci kowani irin tashin hankali ne" with Confidence angel tayi maganar, babu wasa akan fuskarta.
Hankalin su batool ya ɗan kwanta, saboda jin abunda tace, ɗagowa batool tayi daga jikin angel, idanuwanta sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, cikin sanyin murya tace"Angel, bana so wani ya cutu acikin ku ta dalilin mu, idan har giants sun zo zasu tafi damu, kada kuce zaku shiga huruminsu, " girgiza kai angel ta ɗanyi tare da cewa"ki daina faɗin hakan, batool da ace kinsan me suke Yi maku idan suka ɗauke ku, da baki ce haka ba, ke kanki bazaki so atafi dake ba, mutanan nan basu da imani basu da tausayi, kashe mana rayuwa suke son yi ta yadda ba zamu ta6a amfanuwa ba, burinsu shine su ƙarar damu," tamkar zata fashe da kuka ta kai ƙarshen maganar, azeeza dake kwance jikin angel, taƙi ɗagowa baiwar Allah, Jikinta sai kerma yake yi, ta ƙanƙameta tamkar zata koma cikin cikinta, wani irin faɗuwar gaba take ji, ita kanta angel tana iya jiyo sautin bugun zuciyar azeeza, fargabatar kada tsoro yasa zuciyar azeeza ta buga harta mace kafin ma su ƙaraso,
"Mu samu wuri mu zauna, nasan kun gaji da tsayuwa" daga jikin bango suka zauna, still azeeza bata saki jikin angel ba, hannu bibbiyu ta ƙanƙameta koda suka zauna, itama batool ta ɗan kwantar da kanta saman kafaɗar angel, toilet ɗin yai tsit ba ka jin hayaniyar komai, tsawon lokaci kafin angel ta fara faɗa musu addu'o'in da zasu karanta na neman tsari, saboda tsaro,