← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 179

Sashe 107

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Atare suka nufi dining carpet É—insu suka zazzauna, Kowa ya natsu zasu fara Cin abinci,

Duk wannan abun dake faruwa angel da danish suna kishingiɗe saman gadajensu, sun Juyawa juna baya babu mai fuskantar wani, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi, ita dai damuwarta batool ɗinta, ko awani hali take ciki? Fatanta Allah yasa maganar da danish ya faɗa mata akan furen nan ta zama gaskiya,

Bayan su parveeen sun kammala Cin abinci. Sauran da suka rage ma angel da danish, Haris yace su je su É—auko kwandon batool a kwashe musu nasu aciki, Nan fa duk jikinsu yae sanyi tunawa da batool É—insu, duk da dama tana acikin ransu ba yadda za su yi ne, tsakaninsu da ita addu'a ce kawai.

Hanna ce taje ta ɗauko kwandon batool dake a kusa da gadon danish Kifin da suka ajiye mishi tun jiya duk ya bushe jikinshi, hada ƴar rabin gwandar da baici ba, nuna musu kwandon tai tare da cewa"Fried fish din ma ya lalace bari naje na zubar dashi, in wanko basket din sai asanya musu abincin aciki....." tunkan ta ƙarasa maganar parveen tai wuf ta sanya hannu ta kar6e kwandon tana faɗin"Inji wa yace maki ya lalace, bani nan ki gani, yanzu nan zan sanya shi a hanya..." Murmushi suka saki gaba ɗayan su yayin da suke kallonta, A ƙasa ta zuƙunna ta ajiye kwandon tare da kai hannu Ciki tana tatta6a Jikin kifin, azeeza tace"amma parveen baki da hankali, tun jiya fa yake a buɗe cututtuka duk sun hau jikin shi a haka zaki ce? Salon Cikin ki ya 6aci," Harara parveen ta watsa mata tare da cewa"Bai shafe ki ba ae cikina ne ba na ki ba" duk yadda suka so su hanata Cin fried fish din nan taƙi ji, tai kunnan uwar shegu dasu, Zama tayi na musamman tacinye shi tass bayan ta gama da kanta taje toilet ta wanko kwandon tass ta shigo dashi Cikin ɗakin ta miƙa ma Hanna kwandon, tasa hannu ta kar6a ta zuƙunna gaban farantin da niyar ta ɗibar musu wanda suka rage musu, Muryar Angel ta dakatar da ita,

"Kada ki haÉ—a mini abinci dashi, Ki ware mini nawa daban" idanuwanta arufe tai maganar, batare data motsa daga kwancen da take asaman gadonta ba, Haris yace ki É—ibar mata nata ki je ki taimaka mata taci, Ni kuma zan kaima Danish nashi, ta amsa mashi da toh,

Kafin marece yayi saida suka shiga cikin kowani toilet suka dudduba sabbin kayan da aka sanya musu, bakomai yafi burgesu ba face Hair gel kodan sabo da gashin kansu, sun samu na gyara shi, basu fara amfani dasu aranar ba, saboda sunfi so sai angel ta samu sauƙi ta taimaka masu wurin gyarawa.

A daren ranar Saman Sababbin gadajen nan kowannansu ya kwanta, in ka cire mutun biyun nan, Angel da kuma danish suna asaman gadajen su, jiki duk ba daɗi da ga ita har shi, ko wanka sun kasa tashi su yi, room ɗinsu yayi wani irin haske tamkar da rana saboda sabbin fitilun nan da suka kunna hasken su ya gauraye ko'ina gwanin ban sha'awa, Cikin nishaɗi suke ta wasa da pillows, Idan wannan ya jefa ma wannan sai shima yaɗauko pillow Ya jefa ma na kusa dashi, yadda kasan basu da wata damuwa bayin Allah, Angel tana jiyo hayaniyar su suna yin fira bayan sun gama wasa da pillown deeja tace"Nifa gani nake kamar zamu dawwama acikin kurkukun nan, tunda ga wasu ma za'a ƙaro mana" Parveen tace"ai kwara su zo suma su ɗanɗani irin zaman da muke yi, su ji in akwai daɗi," Azeeza tace muguwa parveen yanzu har wasu kike yi ma fatan suyi irin rayuwar da muke yi"? Parveen tana dariya tace"Nifa na faɗi hakanne kodan mu samu a ƙyale mu adaina ɗaukarmu mu tsaffin prisoners, su kuma sabbin sai acigaba da ɗaukarsu, Kunga mun hutu ko ba haka ba,'

Murmushi angel ta ɗan saki, yayin da idanuwanta suke fuskantar ceilling, ta ɗan ɗaga murya tana faɗin"parveen maganar da ki kayi sam ba ta yi mini daɗi ba bai kamata kina yi musu mummunan fata ba, tun kafin zuwansu ma, Ni tausayinsu ma nake ji, su da basu san komai ba, wlh ko maƙiyina bana yi mishi fatan shiga wannan kurkukun ƙaddarar, ballanta su da za'a kawo mana, musamman in ya kasance daga waje za'a kawo su, Ba ƴan asalin cikin kurkukun bane"

jin wannan magnar ta angel yasa parveen tace"patient Ashe baki yi bacci ba, da ace nasan idonki biyu da ban furtata ba," dariya su kayi gaba ɗayansu, Angel tace"Oh, wato ni sarkin yin wa'azi ko? Kiji tsoron Allah parveen, Nidai komai na faɗi inayi ne don in taimaka muku wurin gyara rayuwarku," hanna tace"ai kina ƙoƙari kuma muna jin dadi sosai, muna fatan Allah yabarmu tare dake har bada, har mu shiga aljanna," murmushi angel ta ɗan saki, tare da yunƙurawa ta miƙe zaune saman gadonta ta jingina bayanta jikin bango, ta wutsiyar idonta take satar kallon danish, Ya rungume pillow sai bacci yake yi, aranta tace shi ko tsamin jikinshi baiji, " can kuma ta ta6e baki tana faɗin to ni meye ruwana dashi, " ta ambaci hakan tare da jan tsoki, Muryar Javed ta jiyo daga inda take fuskantarsu Yana ta yi musu faɗa akan su yi musu shiru sun hanasu runtsawa, su kuma sun dage sai zuba suke yi kamar kanyar da bata da daɗi,

kasa kunne ta yi tana sauraron firar da suke Yi, sai taji akan gidan daddynta su ke magana, lamarin ya É—an bata mamaki, jin parveen tana faÉ—in ai wlh idan suka gudu daga Cikin kurkukun suka koma gidansu angel ita acikin kitchen zata dinga kwana, ko dan ta dinga dafa abunda take so"

Sakin baki angel tai tana sauraron ikon Allah, aranta tace wato ita parveen burinta na duniya shine abinci, taci abinci bata gajiya, mai iya rainonta sai manomi, amma wannan in baka da ƙarfin jari saita naƙasa ka," bata kammala zancen zucin nata ba, ta jiyo muryar azeeza tana faɗin"Ni dai ba ruwana da wani abinci, Idan Allah yasa muka bar kurkukun nan muka koma gidansu angel, A ɗakin daddynta zan dinga kwanta, nima ya rungumeni kamar yadda yake yi ma angel suna kwana tare," Haris yace"Sannu uwar son banza, menene alaƙarki dashi da har xaki kwana a ɗakinshi Ya rungume ki," zum6ura baki tae ashagwa6e ta bashi amsa da cewa"Ae ta faɗa mana cewa, Daddynta yana son ƴa'ƴa, Kaga kenan muma zamu zama kamar angel awurinshi" naufal yace"Kuna yaudarar kan ku dayawa, ku ɗan sarara mana, kada wata rana zuciyarku ta karaya, a garin sanyawa rai abunda bazai ta6a yiyuwa ba,"

Kafin wani ya kuma cewa wani abu angel tace"Inji wa ya faɗa maka cewa bazai ta6a yiwuwa ba? Ƙarancin imanin ku shine zaisa mu dawwama acikin kurkukun nan, bai kamata kuna sage musu gwiwa ba, Idan Allah yaso a yau ɗin nan zamu iya barin kurkukun nan wannan ba abun mamaki bane, amma nasan zaiyi wuya ku yarda da maganata har sai ranar da Allah yasa muka ku6uta inda rai da lafiya, tukunna zaku tuna da wannan maganar dana faɗa maku!!!"

Haris yace"kada ki damu, Ni zan tuna maki, wannan ba wani abu bane" yana magana yana dariya kamar wani zautacce, Ya raina maganarta, ba ƙaramin haushi taji ba, tadai yi shiru ne ta ƙyale shi saboda sanin irin jahilcin dake ɗawainiya dashi.

Lokacin da bacci yai awon gaba dasu ita kaɗai ta rage bata kwanta ba, kamar yadda tai alƙawarin xata dinga raba dare biyu domin ta samu damar yin addu'o'inta, tana Cikin yin addu'oin hawaye ta ko'ina akan fuskarta, danish ya farka ya ɗan miƙe xaune saman gadonshi yana kallonta, ganin tana ƙoƙarin juyowa ta kalli inda yake yasa shi yin saurin kawar da kanshi gefe, gudun kada ya sa6a alƙawarin daya ɗaukar mata, saukowa yai daga saman bed din shi Ya janyo bargonshi Ya nufi Cikin toilet dashi, Tana ta bin bayan shi da kallo Cike da mamakin me zai yi a irin wannan lokacin, tsawon mintuna sai gashi ya shigo ɗakin chest ɗin shi ɗaure da bargon, Alamar ya wanke uniform ɗin, Sun ishe shi da tsami, Sai lokacin ta tuna da yadda jikinta yake, ta dage tana ta yin addu'o'i batare data tsarkake shi ba, Yanke shawarar zuwa toilet din tayi don ta wanke kayanta ta samu tayi wanka, tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon ƙasusuwan jikinta suka rurruƙe har wani sauti suke badawa ƙas! ƙaƙas!! wani irin raɗaɗi taji ajikinta, ta ɗan cije la66anta tana faman ambaton wash Allah na, duk akan kunnan danish dake zaune saman gadonshi, Ya lumshe idanuwanshi, Tun da yai wanka sai yaji daɗin jikinshi, wata irin ni'ima ta saukar mishi, yaso ace suna shiri da juna daya taimaka mata wurin yin tafiya don ya fahimci cewa so take itama ta yi wankan,

Ba yadda ta iya dole ta haƙura da yin wankan tayi zamanta tsakiyar gadon, a haka baccin yai awon gaba dasu,
Chapter 107 · 0% Book details