Sashe 44
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk ba wannan ba, tambayoyi da yawa da take neman amsarsu WACECE TSOHUWA? SU WANENE GIANTS DAKE ZUWA KAWO MA SU ABINCI? A INA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA YAKE? TA FARA HASASHEN GIDAN KURKUKUN BA'A CIKIN NIGERIA YAKE BA, ZAIYI WUYA MA ACE ACIKIN GARI YAKE, SHIN SU KAƊAI NE ACIKIN GIDAN KURKUKUN KO KUWA AKWAI WASU MUTANAN? MEYASA AKA HANASU SHIGA CIKIN SHI"?
ta yi zurfi a cikin tunaninta muryar batool ta katse ta da cewa"Angel har yanzu baki yi bacci ba"! Firgigit tayi tare da kallon batool dake a zaune gefen gadonta hannun ruƙe da fitila, tsananin mamaki ne ya kamata, ganin duk sunyi bacci, ita kaɗaice zaune saman gadonta, batasan tsawon lokacin da ta ɗauka ba, Sai da batool ta fargar da ita, ashe dare ya yi har sun kwanta, ita a yadda tabarsu suna akan danish dake ta fasa ƙara, Yanzu ga danish ɗin nan kwance cikin bargonshi sai bacci yake yi, su azeeza ma duk sun kwanta,
"Yansu na farka zan shiga toilet shine na hango ki a zaune, nayi mamaki" murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa"Bana jin bacci ne, ya jikin danish"?
"Ya ji sauƙi, baki ga ma har yayi bacci ba" tayi maganar tana haska gadon danish ,
GyaÉ—a kai angel tayi"Nima yanzu zan kwanta, kije ki shiga toilet É—in,"
Batool tace"ae har na shiga na fito, zan wuce ne na lura dake a zaune"
Shiru angel ta É—anyi, ganin kamar tana acikin damuwa yasa batool tace,"Baki da lafiya ne? Ko wani abu na damunki"?
da sauri angel tace"bakomai, kawai ina tunanin rayuwar duniya ne"
"Yau da kika samu motsa jiki, ga6o6in jikina sai ciwo suke yi mun, amma yanzu dana ta shi daga bacci sai naji daÉ—in jiki na,"
Angel tace"idan kuka saba kullum zaku ji dadin jikin ku, zai saki sosai ba'a son mutun daga yaci abinci ya kwanta, anfi son kadan motsa jikinka, "bayani tayi mata dangane da amfanin motsa jiki, batool tace"Daga yanzu duk in muka ci, abinci zamu dinga yi, bari naje na kwanta" tana kokarin miƙewa angel ta yi saurin ruƙo hannunta, kallonta batool tayi tare da cewa"Lafiya"?
"So nake na tambaye ki, A gidan kurkukun nan Ana kiwon kaji ne"? Cikin rashin fahimtar zancanta, batool tace"Kiwon Kaji kuma? Meye ma'anar hakan"
Dafe kai angel tayi"Ina Nufin kaji da ake kawo mana muna ci kusan kullum, Ana kiwonsu ne a gidan nan ne? Still batool bata fahimci zancenta ba, ta dai san kaza da ake kawo masu a soye suci, amma batasan ma'anar kiwon ba,
"Shikenan tunda baki sani, Amma kin ta6a shiga cikin kurkukun nan? Naga ranar da aka kawo ni, Ni kaÉ—ai nafarka acikin É—akin nan, Ku kuma daga waje kuka shigo Ciki, Ina kuka je ne"? Ta yi tambayar tana kallonta"
"Bazan iya tuna komai ba," cike da takaici angel tace"Komai baki sani ba ke, to faÉ—a mun a gidan kurkukun nan ku kaÉ—ai ne kuke rayuwa a cikinsa"?
Girgiza kai tayi"A'a bamu kaɗai bane, Kinga wannan numbobin na bayan rigunan mu, akwai me 400," waro ido waje angel tayi muryarta har shaƙewa take yi wurun cewa"Are u serious"? Ɗaga mata kai batool tayi alamar Eh, taci gaba da cewa"idan zan iya tunawa kafin zuwanki, Munyi rayuwa acikin wasu Prisoners ɗin waɗanda Ke rayuwa a killace cikin kurkukun nan, bamu kaɗai bane, muna da yawa," mamaki ƙarara akan fuskar angel ta kuma cewa"Amma ku meyasa aka ware ku daga Cikinsu"? Batool tace"nima bansani ba,"
"Yanzu faÉ—a mun, duk wani abu da kika sani game da kurkukun nan,"
"Bansan komai ba"
"Ke dai ki tuna" shiru batool tayi tana kokarin tunano abunda ta sani, tsawon lokaci kafin ta soma magana
"Idan aka ɗauki mutun ba'a dawo wa da shi, idan muka tambayi tsohuwa ina ƴan uwanmu suke waɗanda aka ɗauka daga Cikinmu, sai tace mana mu kwantar da hankalin mu, Suna nan cikin ƙoshin lafiya wata rana zasu da....." bata kai karshen maganarba, ta miƙe da sauri ta dauki fitilarta, ko kallon angel ba ta yi ba ta wuce saman gadonta ta kwanta,
Zuba mata ido angel tayi Cike da mamakin yadda ta miƙe zumbur ta tafi batare da ta ƙarasa maganarta ba, kodai itama an zungureta ne? Ta yi tambayar a cikin Zuciyarta,
Kafin ta yi Shirin kwanciya, kamar kullum ta ɗaga hannayenta sama tana yi masu addu'o'i, Hada daddynta kullum ne bata mantawa da shi, Yana acikin ranta..........🥺
*ANEELERH*
Mami ce zaune gefen gadonta har ta yi shirin kwanciya, jikinta na sanye da Sleeping gown, ta ƙura wa screen ɗin wayarta ido,
fitowa abie Yayi daga Cikin toilet yana gyara wuyan jallabiyar jikin shi,
gyaran murya yayi mata ta É—ago tana kallon shi, fuskarta da alamun damuwa tace"Ina ta kiran aneelerh bata É—aga ba, "
"Bansan meyasa kika tashi hankalin ki ba, sai kace wadda ta tafi wata uwa duniya,"
"Dole na damuwa, saboda ni bata faÉ—amun cewa a can xata kwana ba, kuma na kira layin Uncle bash É—in tana ta ringing bai É—aga ba, itama dr Aisha na kira layinta bata É—aga ba, idan acan zata kwana ae yakamata su kira su sanar dani,"
Murmushi abie ya saki"Na lura ba ƙaramin ji kike da ƴar nan taki ba, Ko da yake nasan saboda wa kika hana idonki bacci,"
"Bai wuci kace saboda baby junaid ba, ae dole na damu da jika na, shi kaÉ—ai fa nake da shi kwallin kwal an tafin mu da shi, sai da nace tabarmun shi a wurina, amma ta kafe akan saita je can da shi,"
"In banda abunki, taya zata tafi tabar maki shi, bayan ba'a yaye shi ba, idan ya yi kuka ya zakiyi da shi"?
"Nima ae macace, Kaima kasan ina da abunda zan bashi" Dariya abie yayi a lokacin ya dawo gefenta ya zauna,
"Yanzu dai ki kwanta kiyi bacci, zuwa gobe da safe, zasu dawo kiga jikanki,"
Ba don taso ba, ta ajiye wayar Suka kwanta bacci atare,
A 6angaren Aneelerh Kuwa, tun Bayan magbrib suka baro gidan Uncle bash, Drivern gidansu Musa ne ke yin driving É—inta, Tana a zaune Cikin back seat na motar, Jikinta na sanye da Arab gown ta yafa mayafi akanta, Baby junaid na rungume saman kirjinta, Yasha kayan sanyi ajikin shi,
"Ba gida zamuje ba, Gidana nake so ka kaini akwai wasu kaya da zan É—auka"musa dake driving yace"Amma Ba mu yi da Alhaji cewa zan kaiki gidanki ba,"
"Eh na manta ban faÉ—a ma shi ba, ka kaini ba matsala," acewar aneelerh,
Shi dai hankalin shi bai kwanta da su je gidan nan ba, ganin dare yayi kuma gidan yana a karkashin Binciken Æ´an sanda bai son wani abu ya faru,
"Amm hajiya naga dare yayi yanzu, me xai hana mu bari sai gobe da safe in kaiki gidan'?
ɗaure fuska aneelerh tayi sam batasan gaddama"meyasa ka ke yi mun magana sai kace wata ƙaramar yarinya? Bani nace ka kaini ba? Ae ba jimawa zanyi ba, akwai abunda nake so in dauko ne Ko minti biyar bazan yi acikin gidan ba,'
Muryar shi na inda inda yace"Zan kai ki mana kawai dai naga dare yayi ga kuma yaro ahannunki,'
"Muje kawai nidai" Amsa mata yayi da toh, ya juya sitiyarin motar ya haura saman titin da zai sada shi da unguwarsu Uzair,
Lokacin da suka ƙaraso unguwar tsit babu hayaniya ko gifcin mutun baka gani, kowa ya shige gidanshi, akwai hasken street light ta ko'ina,
A bakin gate É—in Gidan, Musa yayi parking É—in motar, ya fito da sauri ya buÉ—e ma aneelerh murfin motar, Fitowa tayi hannunta rungume da junaid, Key É—in gidan yana a hannunta, Dama biyu gare su É—aya na uzair É—aya nata, wanda ke a hannun jami'an dake bincike na Uzair ne,
"Madam kodai in bi ki mu shiga Ciki"? Kallon shi tayi ganin duk ya tsorata"Motar fa wa zaka barma gadinta"? Muryarshi a sanyaye yace"hakane kuma bari na koma Ciki na jira ki, dan Allah Aunty kiyi sauri" murmushi tasaki jin ya canza mata suna, ya kirata da madam ya kuma kirata da aunty, Maimakon sunan da yake kiranta da shi Hajiya,
Wuce wa ta yi zuwa bakin ƙopar dake a jikin gate ɗin gidan, ta sanya key ta buɗe ta, ta shiga daga Ciki, duk akan idon musa dake a tsaye ya jingina bayan shi jikin motar,
A tsanake take tafiya Cikin Gidan wani irin yanayi take ji atattare da ita, Ko'ina ta shiga bi da kallo, tun daga kan inda suke ajiye motocinsu har zuwa ƙopar shiga falonsu, Bakomai take tunawa ba face rayuwarsu da Uzair, tuni taji hawaye sun wanke mata fuskarta, yau tsawon shekara biyu da watanni kenan, babu su babu alamarsu,
Hasken electric bulbs ne Ya gauraye gidan, tamkar da rana,
Lokacin da tazo bakin ƙopar falon, ta sanya key ta buɗe ƙopar ta shiga daga Ciki, Ko'ina a gyare yadda kasan mutane na rayuwa acikin gidan,
A saman Sofa ta kwantar da baby junaid dake ta bacci, ita kuma ta shige Cikin bedroom É—insu, tsayawa tayi tana bin É—akin nasu da kallo, sai ta dinga ganin kamar fuskar uzair yana sakar mata murmushi,
Girgiza kai kawai ta yi yayin da hawaye ke cigaba da sauka saman fuskarta, Hotonsu na aure dake manne jikin bango ta ƙurawa ido, Sunyi matuƙar yin kyau, kusan minti biyar kafin ta Hau saman gadonsu ta kwanta tana shessheƙar kuka,
Dama babu abunda ya kawota Cikin gidan tazo ne kawai don ta ƙare mashi kallo saboda kewar Mijinta da tayi,,
Bubbuga mattress din ta dinga yi da hannunta tana kuka tana faɗin Wai ina kaje uzair? Meyasa ka tafi kabarni cikin maraicin rashinka, bayan kasan bana iya rayuwa da wani ɗa namiji idan ba kai ba, dan Allah mijina ka dawo gareni wlh ban gaji dakai ba, ina matuƙar ƙaunarka, kazo kaga Babynmu kyakkyawa da shi, so kake ya taso amatsayin maraya wanda bai da uba? Why uzair? Wata amsa kake so na bashi idan ya tambaye ni dangane da Mahaifinsa? Sai sambatu take yi ita kaɗai tana kuka, sam ta manta da Musa driver dake jiranta, ga kuma Yaro da ta bari a palour shi kadai saman Sofa yana bacci,
Kusan awa ɗaya aneeelerh bata motsa ba, wani irin yanayi mara misaltuwa take jin kanta a ciki, sai faman shessheƙar kuka take yi,