← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 179

Sashe 61

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jingina bayan shi Yayi a jikin Sofa ɗin da yake zaune, Har ga Allah Shi kanshi yana acikin matsanaciyar damuwa na rashin ya'yan shi da ya yi, Yaji raɗaɗi sosai, sai dai ba yadda zai yi, daure wa kawai ya ke yi, A duk lokacin daya tuna rashin Da yayi, Na ɗan uwansa, Kuma yayansa Malam zahiru, da mahafiyarsu deeja, Sai ya dinga Jin kanshi tamkar marayan da baida mafaɗi aduniya, Dama wake gaya mashi gaskiya idan yay badai dai ba? malam zahiru ne, tun yana yaro shi yake zaunar dashi yayi mashi nasiha game da rayuwar duniyar nan, kalmar da yafi faɗa mashi itace "ABDALLAH KAJI TSORON ALLAH, ' tuna wannan yasa shi kai hannu ya dafe goshinsa, Idanuwanshi suka Cicciko tab da kwalla, haƙika yaji mutuwarsu, Hatta yahana su Mahaifiyar Tajuddeen, Yaji mutuwarta sosai, Mutanan kirkiki, Mutane masu ƙima da daraja,

Ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanuwanshi, Bakomai yake tunawa ba face Tajudeen lokacin da zai raba shi da iyayenshi, Suna kuka yana kuka saboda basu son rabuwa da juna, Suna matuƙar ƙaunar ɗansu, Amma saboda son zuciya yabi ta ƙarfi da yaji don yana da arziƙi, ya ba mahaifiyarsu Cin hanci, aka damƙa mashi yaro, tun da yake bai ta6a danasanin raba tajudeen da iyayenshi ba, Sai bayan rasuwarsu, tsawon shekaru basu yi tozali da dansu ba, har sun koma ga mahaliccin su, Shi ma kuma ɗan nasu An neme shi ƙasa ko sama babu shi, Wannan wata irin ƙaddarar rayuwace? Yanzu idan Allah yasa aka ga su tajudden Taya zai Iya Sanar dashi game da mutuwar Iyayenshi!!? innallahi wa'inna ilaihirraji'un............

Tun ɗazu Hajiya adama ta fito daga cikin kitchen, hannunta ruƙe da plate mai ɗauke da glass cup na ruwa mai sanyi tare da snacks, ta jima a tsaye tana kallon Mijinta nata da ya yi zurfin Cikin tunani, Hawaye ta gani kwance a cikin idanuwanshi, Da alamun damuwa attare da shi ba kamar yadda ya shigo mata ba, A saman C table ta ɗaura plate ɗin dake hannunta,

Kwala mashi kira Tayi A firgice yakai idanuwanshi akanta yana kallonta

"wai lafiya dear, Ina ta kiran sunanka Amma hankalinka sam baya atare dakai, Meya faru ne? Yanzu fa nabarka fuskarka asake, amma kuma na dawo na taras dakai cikin damuwa" tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki Cup ɗin ruwan ta miƙa mashi,

Hannu yasa ya kar6a, tare da kaishi saitin bakinshi yana sha, Zama hajiya adama tayi tana fuskantar shi, Jira take yi ya gama sha yayi mata bayanin dalilin shiga damuwarshi,

A hankali ya sauke Cup É—in saman table, ya zura hannu Cikin trouser pocket É—inshi ya zaro hanky ya goge fuskarshi, sai da ya daidaita natsuwar shi tukunna ya kalle ta, gaba É—aya hankalinta na akanshi, sam baison ya faÉ—a mata dalilin shiga damuwar tashi, don yasan halitta, Yanzu ta kama yi mashi kuka, shiyasa ko zancen su Taj bai cika son yi mata ba, Rauni ne da ita,

Gudun kada ta ƙara tambayar shi meke damunshi, yasa shi yin saurin canza zancen ta hanyar cewa"Yawwa, Yanzu wani shirye shirye yakamata muyi na komawa Ƙasar mu? Naji kince zaki yi siyayyar kayan tsaraba da zaki yi ma mutanan gida,"

Jinjina kai Hajiya adama tayi tare da cewa"eh, idan ya rage kamar saura 4 weeks Mu tafi, Inaso zamuje Shopping mall atare, Akwai kayayyakin da nake so Na Siyawa ƙanne na, kasan su mayun kallon korean drama ne, suna san suturarsu ba ƙaramin burgesu yake yi ba, inaso na siya masu, hada Jikana zan siyawa kayan wasan yara, da kayansu na al'ada suna burgeni, ita Fatima ma hada cewa in yi masu tsarabar abincinsu, In banda shiririyata, zan dai siya masu chocolates ɗinsu kalar wanda bamu dasu a gida, " magana take yi mashi amma hankalin shi gaba ɗaya baya akanta, har saida Tace"Kai fa? Me zaka yi tsaraba da shi
Murmushin yaƙe ya yi mata, muryarshi a karye yace"Wa nake da shi da zanyi ma tsaraba? Dama ƴa'ƴana ne, yanzu kuma babu su, amma duk da haka zan siyawa Angel kalar suturarsu, a ƙiyashin da nayi yanzu takai 15years a duniya, Zan yi mata siyayya sosai in ajiye mata, hada bags and shoes da teddys, komai ma zan siya mata, duk ranar da Allah ya bayyanar dasu, sai in damƙa mata abunta,' yakai ƙarshen maganar, tare da duƙar da kanshi ƙasa, Shi kanshi baisan yayi waɗannan Zantuttukan ba, Saboda su ne aranshi shiyasa yayi maganar, Shessheƙar Kukan Hajiya adama yajiyo acikin kunnanshi, Kafin ya ɗago da kanshi tuni ta miƙe da sauri ta wuce zuwa bedroom ɗinsu, Binta yayi da kallo har saida ta 6ace ma ganinshi,

Girgiza kai kawai yayi, kafin ya miƙe ya nufi ɗakin, Don ya samu yayi wanka Ya canza kayan jikinshi,

*Back To Prison🥺*

Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta ke yi, eye lashes ɗinta sun manne ma juna, daƙyar ta samu ta ware idanuwanta basu sauka akan kowa ba, sai akan fine face ɗin Danish dake ta sharar bacci, kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke a yayin da take kallon shi cikin natsuwa, kamar wani baby ya naɗe Jikinshi cikin bargo, fuskarshi kaɗai ce awaje, tun daga kan yadda yake fitar da numfashin shi, zaka shaida yana acikin kwanciyar hankali, baƙaramin daɗi taji ba, tana fatan Allah ya yaye mashi lalurar dake damunshi,

Almost 15 mins tana kallon shimfiɗarshi, kafin ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta a jikin bango, gadajensu batool tabi da kallo, Tayi mamakin ganin basu farka ba, Kamar wasu matattu sai sharar bacci suke yi, kowa ya kudundune jikinshi cikin bargo, sunyi matuƙar burgeta sai ta dinga jin inama ace Acikin Gidan Mahaifinta suke ba'a Cikin Gidan Kurkukun ba, da sun more rayuwarsu, tasan cewa Danginta zasu kar6esu hannu bibbiyu, musamman aunty aneelerh, da hajiya adama suna son yara sosai, taci alwashin idan Allah ya bata Ikon musuluntar dasu, Zata nema masu hanyar da zasu gudu daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Sai dai babban abunda take yi ma fargaba shine, Taya za'ae Su fita daga Cikin kurkukun da ransu da lafiyarsu? Idan Allah yasa sun samu ƙopar fita kenan, Bayan wannan abunda take matuƙar jimawa Anya kuwa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA A cikin ƙasar Nigeria yake!? idan har ba'a Nigeria yake to kuwa dai suna acikin tsaka mai wuya! Fatanta Allah yasa ba awani ƙurmin dajin ginin yake ba, Don kuwa akan hanyar guduwa ma wata dabbatar na iya kai masu hari ta Cinye Naman Jikinsu......."

Tana Cikin yin wannan Zancen Zucin nata, Karaf idanuwanta suka sauka akan danish dake ƙoƙarin faɗowa daga saman gadonshi, Cikin magagin bacci, A hanzarce ta duro daga saman gadonta tayi gaggawar tarbe shi, ƙiris Ya rage ya tiƙo ƙasa, ba don Allah yasa tayi saurin zuwa ba, da kanshi yayi mugun buguwa,

Nannaɗeshi tayi tare da turashi saman gadon, Ya koma yadda yake, Ajiyar zuciya ta sauke yayin da take kallonshi, Soft red lips ɗinsa ta gani suna motsi, alamar yana sambatu, miƙewa tayi ta hau saman gadon, ta duƙar da kanta saitin la66ansa, ta natsu tana sauraron me yake cewa,

_the sounds is soothing me, I can't stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_

Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, jin sambatun da danish yake yi, duk akan Karatun kur'anin da tayi mashi jiya ne, ta fahimci cewa ba ƙaramin daɗi yaji ba, shiyasa ma har yake sambatu acikin Baccinsa,

Whispering tayi mashi acikin ear ɗin nashi tace"Kana so In koya maka"? sam batayi tunanin zai amsa bata, sai ji tayi yace"yeah," da sauri ta kalle fuskarshi, Abun mamaki Bacci yake yi bai farka ba, amma yana magana, ƙumshe dariya tayi kafin ta ƙara cewa"Dame zaka biya ni idan na koya maka"? Tayi tambayar Tana sauraron amsar da zai bata,

Cikin muryar bacci yace"I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want" Cikin nishaÉ—i angel take dariya, A maganar da yayi mata idan har zata fassarata a matsayinta na wadda tayi rayuwa awajen kurkuku, Tamkar kalaman soyayya ne, Amma shi awurin shi bakomai bane, ya faÉ—i mata hakan ne saboda baida abunda zai iya biyanta da shi, idan ba kan nashi ba,

"does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?"
Amsa mata yayi"yeah" koda wankin Uniform É—ina ne? Tayi tambayar tana kallon fuskarshi, idanuwanshi na arufe gam, wannan karan bai bata amsar tambayarta ba, da alama ya kuma yin nisa Cikin baccin sa,

Ruƙo bargon shi ta yi tare da ƙara janshi ta rufe mashi har zuwa saman fuskarshi, Tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon danish, Ta ji yo motsin buɗe ƙopa, da alama giants ne suka ƙaraso, Yau Abinci ya riga masu Cin shi, ƙarasowa,

Ƙarasa saukowa tayi daga kan gadon nashi, ta tsaya a tsaye tana Jiran su ƙarasa shigowa Ciki, Takun tafiyarsu ta soma jiyowa, kafin su bayyana su ukun nan hannayensu a ruƙe da wooden trays, mai ɗauke da kayan Kalacinsu,

Akan idonta suka wuce zuwa saman dining carpet ɗinsu, Kowa ya sauke Farantin dake a hannunshi, Ja da baya su kayi atare suka ƙame kamar yadda suka saba, tunani ta shiga yi Kowanene acikinsu Ya damƙeta aranar nan har yayi wurgi da ita, bazata ta6a manta azabar da tasha ba, Ta tsani giants a rayuwarta, ko son ganinsu bata yi, Saboda basu da Imani, Ga ƙarfi kamar na dawakai, ta jima tana kokwanto akansu Anya kuwa Cikakkun mutanene? Kodai half jins ne?

Ta yi zurfi Acikin tunaninta, taji motsinsu, Ras taji gabanta ya faÉ—i ganin suna tattara kayan abincin da suka ajiye masu, aruÉ—e tace" ina zaku tafi da abincin mu? Bayan bamu Ci ba" babu alamun suna sauraronta,

"Magana fa nake Yi maku, idan saboda suna yin bacci ne yanzu zan tashe su, pls kada ku tafi" ko waiwaye wannan basuyi mata ba, Tana ji tana gani suka haura saman bene da abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Tana Jiyo sautin garkame ƙopa da su kayi,

"Ya salam" ta ambaci hakan tare da dafe kanta, muryar batool ce ta katse ta da cewa"Angel lafiya naji kina sambatu ke kaÉ—ai"? Da sauri angel ta juya baya tana kallon batool dake kwance saman gadonta, farkawarta kenan daga bacci,
Chapter 61 · 0% Book details