← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 179

Sashe 83

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cakumar wuyan rigarshi tayi da hannayenta biyu, ta zazzare mashi manyan gray eyes É—inta Ta jijjiga wuyan rigar tashi, Saboda masu bayyaci yasa ta sassauta muryarta,

"Wai menene alaƙata dakai ne? Ka addabi rayuwata ka hanani sakat, kai nifa bansan ganin wannan mummunar fuskar taka, na tsani ragon namiji irin ka, pls na roƙe ka ka tashi kabar gefen gadona ko na samu inyi bacci" Takai karshen maganar tare da ture shi gefe, ko motsi baiyi ba, kallonta kawai yake yi da lumsassun idanuwanshi,

A hasale tace"idan har bazaka sauko daga saman gadon ba, Ni zan tashi in baka wuri," ganin tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon yasa shi yin saurin damƙar hannunta, wani irin mugun kallo ta jefa mashi"sakar mini hannu na," ba musu ya saki hannun. ta sauko daga saman gadon, Ta dauƙi bargonta da pillow, Ta juya ta nufi tsakiyar ɗakinsu Ta shimfiɗa bargon ta jefa pillown saman shi, Ta haye ta kwanta, duk yana a zaune gefen gadonta yana kallonta,

Lumshe idanuwanta ta yi da niyar bacci ya ɗauketa, kamar daga sama taji an sanya hannu an ɗauketa da ita da bargon da pillown duka ya tattare su ya ɗaga sama Ya nufi gadonta, Yana zuwa ya jefe ta saman gadonta, aɗan tsorace ta ware idanuwanta tare da wurgasu kan fuskarshi Yana atsaye ya kafe ta da ido, Tsabar mamaki ya hana ta furta komai, kamar walƙiya haka Yaje ya daukota,

Cikin nuna jin takaici tace"Nashiga uku! Wai ina ruwanka dani ne? idan na kwana a ƙasa matsalarka ce ko tawa"? Ya bata amsa da cewa"tamu" guntun tsoki taja, bata ƙara furta mashi komai ba, tana jin motsin shi abayanta, haukanshi na matuƙar ɗaure mata kai, Lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, A zaune ya fara gyangyaɗi, A ƙarshe da baccin yafi ƙarfinshi a bayanta ya kwanta saman gadonta, lallai ya taro march,

*ANEELAH*

Wuraren ƙarfe 12 na safe, Tana a ƙudundune Cikin bargonta, Tun bayan sallar asuba data kwanta bacci bata farka ba, wani irin nauyin bacci ne ya ɗauketa, Hada ƙarin maganin muran da tasha a daren Jiya,

Baby junaid ne ya shigo cikin ɗakin yana azaune Cikin motar shi ta wasan yara, Da hannu Yake juya streering wheel ɗin motar, Ba ƙaramin kyau yayi ba, jump suit ne a jikinshi launinsu ɗaya da ƴar motar wasan shi, Army green, da alama ba ƙaramin daɗin motar yake ji ba, daga ya juya steering saita tafi da gudu, agaban gadon Mommynshi Ya tsaya, tare da kai hannu ya danna wani maddani A jikin motar, nan take motar ta soma yin Jiniya, Afirgice aneelerh Ta farka tare da yaye bargon data lullu6a dashi hannunta dafe da ƙirjinta, jallabiya ce a jikinta, Muryarta na kerma take ambaton" Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"

tayi matuƙar tsorata, Duk a tunanin ta ƴan sanda ne suka zo gidan ashe motar wasan junaid ce, Fuskarta a yamutse take kallon shi, ya wage baki yana dariya fararen hakoranshi tar dasu, Dimples ɗinshi biyu sun lotsa sosai, a fusace ta miƙa hannu ta ɗauki pillow ta wurga mashi saman fuskarshi, nan take ya kwa6e fuska zai yi kuka,

Cikin nuna 6acin ranta ta soma Yi mashi magana"Karka kuskura kace zaka yi mini kuka stupid, Wlh nayi regretting dana fidda kuɗina na siya maka motar nan ashe kaina abun zai ƙare!, bazaiyiyu ba ka hanani kwanciyar hankali, zan 6a66alla motar In jefata cikin bola kowa ya huta" Jin wannan maganar yasa shi ƙara sautin kukan nashi, Ganin tana yunƙurin saukowa daga saman gadon yasa jin tsoro, gudun kada ta 6alla mashi motarshi kamar yadda tace, aikuwa da sauri yaja streering Ya juya motar da gudu yajata ya nufu ƙopa, Murmushi ta saki tana bin bayanshi da kallo, aranta tace"Allah kaɗai yasan irin ƙalin sharrin da zaije yayi mini a wurin mami, yau nifa na shiga uku, Wata'ƙil ma yaja a hanani Yin breakfast, " takai karshen maganar tare da saukowa daga saman gadon takai hannu ta ɗauko filon data jefa mashi a ƙasa ta wurgo shi saman gadon, miƙa tayi tare da yin hamma ta wuce toilet, after some minutes ta fito tana tafiya a slow ta nufi gaban mirror ta zauna, wata irin yunwa take ji kamar taci ƴan hanjin cikinta, wayarta ta ɗauka dake ajiye gaban mirror, ta danna power hasken screen ɗin ya kawo, hoton angel ne a matsayin wallpaper ɗinta, ta yi mata hoton ne saman gado tana bacci ta saki baki, Tana matuƙar son angel, Tayi missing ɗinta sosai, duk rana ta Allah idan tafarka daga bacci ta ɗauki wayarta saita sumbaci hoton, Yanzu ma kiss ta manna mashi, aranta tace"I really missed u angel, kamar in yi hauka, Allah ya kare mini ke aduk inda kike, Inaji araina cewa Kina araye kuma kina tunani na, I luv u so much" tuni hawaye sun Cika idonta,

Tana yunƙurin miƙewa daga saman mirror chair ɗin, Sai ga Ana Mai aikin gidansu ta faɗo Cikin ɗakin tana Haki hannunta ruƙe da wayarta, Jikinta sanye da Riga da skirt, Sun matseta, Hankalin aneelerh ba ƙaramin tashi yae ba, Ta cikin mirror ta hangota, da sauri ta ƙarasa Juyawa Baya tana kallonta tace"Ana lafiyarki kuwa? Babu neman excuse kin faɗo mini ɗaki? Kamar wadda tasha ƙwaya"? Tayi maganar tana tunkararta, Duƙar dakai ƙasa ana tayi Muryarta na ɗan rawa tace"Am sorry madam, Wani abune na gani daya bani mamaki, shi ne nazo in nuna maki,"

Matsawa aneelerh tayi kusa da ita, Tare da miƙa hannu ta kar6i wayar Ana, tana ɗaura idanuwanta kan screen ɗin, Ras taji gabanta ya faɗi waro ido waje tayi tana kallonta, mamaki ƙarara akan fuskarta tace"Abun mamaki! ana a ina kika samu hoton nan? Kuma daga gani sabuwar ɗauka ce!" murmushi ana ta ɗan saki kafin tace"Yanzun nan Na ganshi A instagram, shafin twins Na Family ɗin Obinna, Zayn da zaid pravin Obinna, Su ne su ka yi posting ɗin a page ɗinsu na insta, madam i was shocked da naga pic ɗin nan nace ashe matar nan tana araye da ranta da lafiyarta! " jinjina kai aneelerh tayi da alama tayi matuƙar girgiza tace"Wonders shall neva end" kallon Ana tayi tare da cewa"Ki jira ni ina zuwa, dole mami taga hoton nan, amma dai matar nan ta bani mamaki matuƙa" Jiki na rawa aneeleh ta fuce daga Cikin ɗakin, gudu gudu sauri sauri ta nufi bedroom ɗin mami, bayan tafiyarta ana ta fito ta tsaya a falo tana jiran dawowarta,

Aneelerh Na yunƙurin yin sallama a ƙopar ɗakin Mami, sai ga mamin ta fito Jikinta sanye da riga da zani na atampa, Ƙiris Ya rage su bangaji juna ita da aneelerh, Sakin baki mami tayi tana kallonta,

Da sauri aneelerh tace"Am sorry mami, a ruɗe nake ne, wani abun mamaki ne Ana ta gwada mini acikin wayarta, Shi ne na kawo maki kema ki gani" tana inda inda tayi maganar, tare da miƙa ma mami wayar hannunta, tasa hannu ta kar6a, koda mami ta kalli hoton saita ruƙe ha6arta da hannu ɗaya, ta ɗan zaro ido da mamaki akan fuskarta tace"Kai! Wa nake gani kamar BENAZIR"! aneelerh tace"Mami itace, Kalli dakyau ki gani, ba'a jima da yin posting ɗin ba, " Mami tasha ruwan mamaki, Sai ƙarewa hoton kallo take yi, dagaske ɗin dai benazir ce, Daga gani hoton batasan an yi mata shi ba, tana a tsaye, hannunta ɗaya ta dafa murfin danƙareriyar motarta, tsadaddiyar gaske, jikinta na sanye da business suit black colour sunbi shape ɗinta sun zauna mata cuf cuf, kamar don ita aka ƙera kayan, hips ɗinta sun fito sosai, hannunta ruƙe da wayarta ƙirar i phone 15 pro, kanta babu hula ko ɗan kwali, Zallar gashin kanta ne daya sha gyara Har midback dinta, idanuwanta na manne da glass, idan ka ganta a hoton ba zaka ta6a yarda cewa ta ta6a aure ba, Ko tana da ƴa, saboda tsabar haɗuwarta, Jikinta Badai kyau ba, agogon diamond ɗin dake sanye a hannunta, a ƙalla Price ɗinta yakai 100m,

Kallon Juna mami da aneelerh su ka yi kowa Fuskarshi ɗauke da al'ajabi, mami tace"Abun mamaki baya ta6a ƙarewa, Wai dama ƴar nan tana nan da ranta da lafiyarta? Hankalinta kwance tsawon shekara da shekaru bata ta6a waiwayar ƴarta da mijinta ba, Anya kuwa benazir ce aneelerh? Kodai watace me kama da ita? to ae abunne da ɗaure kai wlh, '

Murmushin takaici aneelerh ta saki tare da cewa"wlh mami itace! Babu shakka benazir ce, ae ina ganin hoton ko doubting ban yi ba, na shaida itace, Kinsan dama ita tun fil'azal wayayyiyar macace akwai son gayu, Kuma tafi sha'awar rayuwar ƴanci, " mami tace"Haka fa take, Oh Ni ƴarsu, duniya da abun tsoro take, Anya kuwa Benazir tasan ciwon kanta"? aneelerh tace"Ina fa, ae babu alama, Yanzu haka ko Iyayenta basu da masaniya akan inda take rayuwa, Duk da Naga kamar Ƙasar waje ne, idan kika ƙura ido a jikin Ginin dake a bayan hoton an rubuta Rbc (Royal bank of canada) dake acikin toronto, Kuma ga dukkan alamu mami hoton bada saninta aka ɗauke shi ba, don da ace ta sani da bata bari an ɗauke shi ba, kodan kada asirinta ya tonu agane inda take, tun da ko Iyayenta basu son awace nahiya take zaune ba suma nemanta suke Yi ruwa ajallo,"

Mami tace"Nama rasa me xance, kawai dai Allah ya shiryeta in me shiryuwace, amma dai wannan rayuwar da ta ɗaukarwa kanta bamai 6ullewa bace, Wlh zata yi danasanin mara amfani, kwata kwata benazir bata yi wayau ba, Allah kanta tayi mawa, Ace da ranka da lafiyarka, Ka gudu kabar Jinjira acikin kwamin wanka, da mijinka batare da ka waiwaye su ba almost 4 years, Saboda shafewar basira da rashin hankali, tana can tana yawon biɗiɗi," takarasa maganar tare da jan dogon tsoki Ranta ya 6aci ta miƙe ma aneelerh wayar"kar6i nan nagaji da ganin kayan takaici," kar6ar wayar aneelerh Tayi, Har ta juya zata Bar ƙopar ɗakin mami sai kuma ta ɗan dawo baya tace"mami Baby junaid fa"?
Chapter 83 · 0% Book details