← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 179

Sashe 136

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Meyasa ki ke mirmishi"? Muryar shi ce ta katse mata tunanin nata, har lokacin bai janye rigar tashi da ya ke miƙo mata ba.

Maƙe mashi kafaɗa tai tare da cewa"ae babu kyau, bazan goge maka ba, sai mun yi aure" maimaita kalmar aure yai"what does that mean"? Jujjuya eye balls ɗinta ta yi, tare da sauke su kan fuskar shi tace"Zan faɗa maka amma ba yanzu ba, sai mun fita daga cikin kurkukun nan," ta ƙarasa maganar tare da fashewa da dariya, tabi ta gefen shi, ta fuce daga cikin toilet ɗin, bin bayanta da kallo yai har ta 6ace ma ganin shi, ta tafi tabar shi da aikin maimaita kalmar Aure, tunawa da Gabriel dake acikin ɗakin, yasa shi yin saurin bin bayanta.

Tana shiga ɗakin ta samu su azeeza zazzaune saman dining carpet ɗinsu kamar masu cin abinci, Alhalin nan kuwa fira suke yi a tsakanin su, gwanin ban sha'awa, Gabriel Na ganin ta yae saurin yunƙurawa zai miƙe daga zaunan da yake a gefen gadon shi, suna haɗa ido da ita, Sai ga Danish Ya faɗo ɗakin, da sauri Gabriel Ya koma ya zauna fuskarshi babu walwala, bai ta6a ganin ɗan takura irin Danish ba.

A bayan angel ya tsaya tare da yi mata magana"muje ki kwanta" ba tare da ta kalle shi ba tace"bacci a yanzu? A'a gaskiya, Ni sai dare yayi zan kwanta, Zanje wurin su hanna mu yi fira ne, " yace mata"Okey, my eyes on u," yana faÉ—in hakan ya nufi akwatin kayan su, ya buÉ—e ya ajiye rigarshi, ya É—auko red vest É—insa ya zura ta a jikin shi.

Su hanna na ganin Angel, suka soma sakar mata murmushi suna faÉ—in Ga Masoyiya angel nan, Ku bata wuri ta zauna, mayar musu da martanin murmushin ta yi, taji daÉ—in sunan da suka kira ta dashi Masoyiya Angel.

A tsakankanin Jamima da azeeza ta zauna, tana fuskantar Hanna da parveen, kowannansu yai zaman cin tuwo kamar É—aliban makaranta allo.

"Ku fada min akan me ku ke tattaunawa ne"? Tai tambayar tana kallon fuskar kowannan su,
Sarah ce ta fara magana"Labari su ke bamu akan abubuwan da ki ke koya musu, Lokacin da bamu nan" Parveen tace"Namanta ban faÉ—a maki ba, lokacin da ki na yin bacci kamar jiya ne, Gabriel ya tambaye mu, wai mu bashi labarin ki sannan mu faÉ—a mashi abubuwan da kika koya mana, kuma duk mun faÉ—a mashi" a tsanake ta ke sauraron su, yayin da idanuwanta ke a kan la66an masu yin maganar.

"Yau har training É—in rawa ya bamu, duk mun gaji, shiyasa muka zauna muna É—an zantawa" acewar Hannah.

"Pls Angel, ki koya mana abunda ki ka koya musu muna so" Jamimah ce tai maganar, Hibba tace"damuwa tasa kin daina koya mana karatu," numfasawa tayi kafin ta soma magana

"In sha Allah zamu cigaba da yin karatu, nima ban ji dadi ba, dana daina koya ma ku, yanzu dai kowa ya faÉ—i abunda yake so mu dinga yi, don mu sanya junan mu farin ciki"

Duk wani a bu da suke tattaunawa akan kunnan Danish, da ke a zaune saman gadon shi, nan ya zauna bayan ya sanya vest dinsa, idon shi akan la66an Angel da ke cikin yin magana tana kora masu parveen jawabi akan abubuwan da zasu dinga kullum.

Ko ƙyaftawa baiyi, Gabriel kam Idon shi na akan Danish, lamarin ya ɗaure mashi kai, ganin irin kallon ƙurullan da ya ke yi ma Angel, kamar zai lashe ta,

Firgit! ya yi jin saukar hannun mutun saman kafaÉ—ar shi, da sauri yakai idonshi kan wanda ya ta6a shi, Haris ne ya zauna gefen shi.

"Da alama ka manta da É—an uwan ka, na lura kwanakin nan hankalin ka gaba É—aya yana akan Angel tun da ku ka shirya da ita, wai menene a tsakanin ku ne? Tell me É—azu ma mu na kallon ku ni da Deeja, Angel ta shiga toilet ka bi bayanta, tsawon lokaci ba ku fito ba, sai daga bisani mu ka ga ta fito, kai ma ka biyo bayanta kamar ma wanka ka yi" tun da haris ya soma magana Danish Ya baza kunnuwanshi yana sauraron shi, sai dai har yanzu bai janye idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba saboda tsabar jaraba.

Da mamaki akan fuskar Haris yace"kai magana fa nake maka? Ko kallo ban ishe ka ba kenan," motsi yae da la66ansa wurin furta mashi"Am all ears," haris yace"ae nasan kana ji, saboda ka maidani shashasha ina magana idon ka na akan Angel, wai me ka ke kallon akan fuskarta ne"? Yai tambayar yana leƙen fuskarshi, da buɗar bakin Danish sai cewa yai"kyau nake kallo, ko ba ka gani ba" sakin baki haris yai,"Dama kyau yana kallon kyau"? ɗaga mashi kai ya yi alamar Eh.

"Bari na tashi na baka wuri, ka gama kallon kyan, don na lura gaba ɗaya bata ni ka ke ba," kafin haris ya miƙe Danish yai saurin ruƙe hannun shi yace"Hankalina akan yake, idanuwana ne kawai basu atare da kai, amma ina sauraronka" Guntun toki haris yaja"dalla ni sakar min hannu na, ɗan rainin wayau," Ƙin sakin hannun nashi yai, ya damƙe shi acikin nashi, su naufal dake zaune saman beds ɗinsu, gaba ɗaya hankalinsu na akan Danish da haris, Mubeen yace"ku tashi muje wurin su mu ma muyi fira, tun da suma matan sun haɗa kansu" Kamar dama jira su ke yi yai maganar, kowannan su ya sauko daga saman nashi gadon su ka nufi Danish, gefe da gefen mattress ɗin suka zazzauna.

Javed yace"me kuke tattaunawa ne? Shi ne baza a kira mu ayi zantawar damu ba," Haris yace"kun ga alamun muna tattaunawa ne? tun da nazo na zauna gefen shi, bai juyo ya kalle ni ba, idanuwanshi na akan Angel, na rasa gane me yake kallo akan face ɗinta, ya dai ce min kyau yake kallo" dariya su ka saki gaba ɗayan su, naufal yace"abun mamaki, kyau na kallon kyau," Ba tare da Danish ya kawar da idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba ya bashi amsa da cewa"ba abun mamaki ba ne, ni nasan me nake kallo" mubeen yace"ban yarda ba, sai dai wani abun na daban, idan kyau ka ke son kallo, ka ɗauki mirror ka kalli fuskarka mana," shiru bai tanka mashi ba, don ba ƙaramin takura shi su ka yi ba, Gabriel da ke zaune gefen gadon shi, a takure, yaso ace angel tana fuskantar inda yake ne don ya ji daɗin faɗa mata inda ya ajiye mata wasiƙar, sai dai ta juya mashi baya.

"Tun da baka son mu zauna a kusa da kai, ku tashi mu je wurin ƴan uwan mu mata, su yi firar tare da mu," haris na faɗin hakan kowannan su ya miƙe su ka nufi Dining carpet ɗin su, inda su Angel su ke zazzaune kowannan su Ya samu wuri ya zauna, cikin sa'a Naufal ya zuƙunna bayan Hannah da ke fuskantar Angel, da ya ke dogo ne shima tubar kalla, gaba ɗaya ya kare ma Danish Fuskar Angel, baya iya ganinta da kyau, takaicin duniya ya ishe shi, sai ya mayar da kallon shi ga Gabriel, su ka haɗa ido da juna, Jira ya ke yaga in gabriel zai miƙe da niyar yaje wurin su, kamar Gabriel yasan me ya ke ayyanawa acikin zuciyar shi, da gangan ya miƙe zai nufi wurinsu, a hanzarce Danish ya miƙe, komawa Gabriel yai ya zauna gefen gadon shi, sai gashi shima Danish ɗin ya koma nashi gadon ya zauna, Ikon Allah.

Su biyu ne basu je wurin ƴan uwan nasu da ke yin fira ba, hatta Majnun yana a tsakankanin Deeja da Rubina, Ya natsu kamar mutumin arziƙi, duk wanda yai magana acikinsu haka zai ƙurawa la66ansa ido har sai ya gama magana, wani lokacin sai ya tintsire da dariya, ko ba abun dariya aka faɗi ba.

"Tun da yanzu mun ƙara yawa, A faɗa mana waya fi kyau a cikin mu"? Acewar Yasmin, hibbe tace"wa zai faɗi? Sai dai ko Angel,' girgiza kai angel tai
" a'a, a samu wanda yafi kowa hankali a cikin mu ya faÉ—a mana wanda yafi kyau,' ta yi maganar tana nuna musu majnun da idonta, dariya su ka saki gaba É—ayan su, Deeja tace da shi"Chinonso faÉ—a mana waya fi kowa kyau a cikin mu, yau zamu tabbatar da idan kana da cikakken hankali"

murmushi suka ga ya saki yana murmura idanuwanshi, hada ƙoƙarin miƙewa tsaye yana kallon fuskokin su, tsawon lokaci sun kasa kunne suna sauraron shi, yadda kasan me nazarin wani abu, har wani leƙa fuskarsu yake yi, a ƙarshe yace"Haris" shiru su ka yi, haris ko sai tiƙar dariya yake yi, itama Deeja murmushi ta saki,

Jamima tace"Ƙarya kake yi, ba haris bane yafi kyau, ba ka ga shi baƙi bane,"

Harara chinonso ya watsa mata, tare da ruƙe qugunshi, ya turo ciki gaba yana faɗin"ke ne kike ƙarya, harisu ba baƙi bane, Fari ne fat," waro ido su kai gaba ɗayan su suna kallon shi, Angel tace"Anya kuwa Majnun Ƙwaƙwalwarka tana aiki dai dai? Haris ɗin ne yafi kowa kyau kuma fari ne" jinjina mata kai yai fuskarshi a ɗaure yace"Eh mana, yafi kowa haske aciki ku, shi ne yafi kowa kyau" Mubeen na murmishi yace"anya haris ba wani abu ka yi mishi ba? Ko dai ka yi mishi ƙyafcen ido ne"? Haris na dariya ya ce"Ka tambaye shi mana sai ka ji idan ni ne nasa shi ya faɗi hakan"

Miƙewa mubeen yai tare da komawa gefen chinonso da ke a tsaye, ya duƙo yadda tsawon su zai dai dai ta"faɗa min wata irin barazana haris yai maka"? Ta6e baki majnun yai, ni bai min komai ba, gaskiya na faɗi yafi kowa kyau acikin ku, shine fari" fuskarshi a ɗaure yai maganar babu alamun wasa don shi har ga Allah gaskiyar shi ya ke gaya musu.

"Yau naga ikon Allah, wai dole sai ya ƙaryata abunda ya faɗi? Nifa na sani dama, haris yafi kowa kyau a cikin ku"! acewar Deeja, haris ya kar6e da cewa faɗa mu su dai, Ni ɗin kyakkyawa ne, da alama kishi su ke yi dani, '
Chapter 136 · 0% Book details