← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 179

Sashe 117

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

yana jin wata irin natsuwa mai kwantar da tarzoma acikin zuciya, Dariya haris yae tare da cewa"Danish fa suman kwance yae, Da alama Mun kashe mashi baki, Parveen ɗauko musu Madubi Su kalli fuskarsu atare, Ki haɗo mishi Da Naman kazar shi da bai ci ba, xamu tasa shi gaba sai angel ta bashi abaki Yaci, Ko yana so ko baya ehe" gaba ɗaya suka haɗa baki wurin cewa"Dolen shi ne ma, Idan yasa taurin kai Mu tarar masa, kamar yadda mu ka yi a yanzu," jiki na rawa parveen ta nufi akwatin da madubin yake, A jiye ƙarƙashin table ɗinsu, Nan suka kwantar dasu, ɗaya saman ɗaya, ta janyo akwatin Ta buɗe shi, daga sama Mirror ɗin yake, Ta sanya hannu ta ruƙo handle ɗin shi, da gudu taje ta miƙa ma Haris Ya sanya hannu ya kar6a, kafin Ta juya ta nufi gadon Batool, Allah sarki, Har yanzu a ƙarƙashin gadonta suke Ajiye kingin abincin da suka rage, Zuƙunnawa tae tare da tura hannu ta janyo basket ɗin, maimakon taje ta kai musu, sai da ta fara Kai naman baki ta ɗan 6alla, tukunna ta miƙe da sauri taje ta miƙa ma Haris kwandon, yace da azeeza ta kar6a ta ruƙe, tun da shi madubi ne a hannun shi, Bayan azeeza ta kar6a suka ɗan dakata suna jiran Danish Ya miƙe daga Jikin Angel, sai dai basu ga alamun xai ɗago ba, don ya tsare ta da waɗannan fararen eyes ɗin nashi, sun ƙurawa juna ido, kamar ranar suka fara ganin juna, muryarta ƙasa ƙasa tace"Ka ɗaga ni, na fara jin nauyi," da alama bai ji me tace ba, Xaro mashi gray eyes ɗinta tae gwanin ban tsoro ta kuma cewa"Am talking to u my man, Alƙawari ne dai ya karye, ko kana so ko baka so," Bata yi tsammanin zai tanka mata ba, in a smoky voice ya furta"kin shammace ni," murmushi ne ya bayyana akan face ɗinta,

"Bani na shammace ka ba, sune suka shammace ka, Kuma taimakon ka su ka yi, ko ba haka ba"? Tae maganar tana ɗan jifar shi da harara, martanin mirmishin ya mayar mata, kafin ya daure ya yunƙura ya ɗaga jikinta, ya koma daga gefe ya gyara zaman shi sama mattress din, ya jingina bayan shi jikin bango, Itama ta miƙe ta jera kafaɗa dashi suka xauna, Yayin da suke fuskantar ƴan uwansu, dake a kewaye dasu, Sai murmushi suke sakar musu, musamman azeeza hada wani kashe musu ido.

Matsawa haris yai daga gefen gadon Ya miƙa ma Angel madubin, Tasa hannu ta kar6a, tun kafin ta saita shi saitin fuskar Danish yae saurin shutting eyes ɗinshi, muryar shi tae low wurin furta"Pls angel, ki janye shi bana son ganin shi," sosai ya datse idanuwanshi, naufal yace"Why? Its just a mirror, face ɗin ka zaka gani ba wani abu ba, muna so ne kawai kaga irin kyan da ka yi acikin Sabon Uniform ɗinka, ko ba haka ba guys"? Atare su haɗa baki wurin cewa"Yeah"! Kallon shi Angel tae ganin har jikin shi ya fara kakarwa, Mamaki ya kama su, ko meyasa baisan Kallon madubi, wannan itace tambayar da suke yi ma kansu.

"Idan ma tsoron kallon shi ka ke ji, remember that am with u by ur side, u can hold me,"

jin wannan maganar ta Angel, yasa shi yin saurin xagayo da hannun shi ta bayanta zuwa saman kafaÉ—arta ta hagu, Ya É—an kwantar da kanshi saman right shoulder É—inta, Har ga Allah bai son kallon Mirror, Ba yadda zai yi ne don sun matsa mi shi, kuma a yanzu yana son farin cikin su shiyasa ya amince musu,

Kanga madubin ta yi saitin Fuskarshi tare da cewa"Ka buÉ—e idanuwanka a hankali," bin umarnin ta yae wurin buÉ—e eyes É—inshi slowly ya ware su akan Round mirror É—in, har wani lumshe su yake yi, Murmushi angel ta saki ganin yana kallonta ta cikin madubin tace"Bani xaka kalla ba, Fuskarka zaka kalla" ta6e mata lips dinshi yae irin an takura shi É—in nan,

Su haris sai dariya suke tiƙa, sun samu Abun kallo, hada ƙoƙarin zuƙunnawa bakin gadonsu, saboda sun gaji da tsayuwa, duk yadda ta so Danish Ya kalli fuskarshi acikin mirror yaƙiya sai dai ya kalli fuskarta, Javed yace"its okey, Hakan ma ya wadatas, Yanzu A ajiye madubin gefe, Ga chicken leg ɗinsa nan ki bashi ya ci, idan ya kammala da kazar sai ki ba shi fruit ɗin shi" Amsa mashi tae da toh tana murmushi ta miƙa ma parveen madubin ta sanya hannu biyu ta kar6e shi, ta juya ta nufi box ta ajiye shi, ta dawo ta zuƙunna gefen su hanna, Duk fa wannan budurin da suke Yi basu san cewa Dare Yayi ba, don tuni Hasken Fitilun ceilling ɗinsu Ya ɗauke, Na floor lamps ne Ya Haskaka Room ɗin nasu, ba tare da sun ankara ba, Wasu irin fitilune Da zarar duhu yayi da kansu suke kunna kansu, Kamar dai na saman ceiling ɗinsu, banbancin shi ne, da zarar dare yae suke ɗauke wa su kuma na ƙasan sai in duhu yayi suke kunna kansu, Kuma haskensu baida banbanci, da alama babu mai jin bacci acikinsu, sakamakon baccin da suka sha ɗazu da marece, hada ƙarin hakan yasa suka gaza gane cewa Dare ya yi.

Azeeza ce ta miƙa ma Angel Kwandon Tasa hannu biyu ta kar6a ta ɗaura shi saman Laps ɗinta, kafin ta zura hannun ta na dama ta ruƙo cinyar kazar ta ɗago da ita, saitin bakin shi ta kanga mashi ita, Sai gashi Ya xaƙe dai ci ya ke yi su mubeen suna ta yi mishi clapping, sai da ya Cinye rabi Ya janye bakin shi, ta tambaye shi ko ya ƙoshi ne? yace mata eh, zata iya cin sauran, parveen kamar zatai kuka tace mufa,' Dariya angel tae tare da miƙa ma azeeza Naman kazar maimakon parveen tace"Saboda rashin tsoron Allah Parveen Nafa ga wurin da kika yaga, hada sahun haƙoran ki, a jikin cinyar kazar, ko an gaya maki ban lura ba ne," Yatsina fuska parveen tayi, Hada murguɗa baki, Azeexa kuwa ta kar6a cinyar kazar daga hannun Angel, ta ɗan gutsira ta miƙa ma hanna itama ta yaga, ɗaya bayan ɗaya saida kowa Ya Ci naman, A ƙarshe suka miƙa ma parveen Ƙashi, su ka ce Ta gwaigwaye shi, Hada ƴar ƙwallarta saboda tsabar baƙin ciki, kuma hakan baisa taƙi kar6ar ƙashin ba,.

Apples ta curo kusan Uku da suka rage mashi, Yace mata shi ɗaya ya ishe shi, sauran ta basu su ci, tace mashi hada sauran fruit din? Don akwai ayaba guda uku, Yace mata Ta ajiye mashi ayaba ɗaya ta basu sauran su ci, Sai daɗi suke Ji, Ta miƙa ma haris Apples biyu da ayaba Biyu Yasa hannu ya kar6a, Shi ya rarraba musu, tare da miƙa ma kowannan su, suka kar6a suna ci.

Abaki angel taci gaba da bashi apple ɗin yana Ci, sai da ya ci rabi, yasa hannu ya kar6a, Ya koma yana bata abaki tana ci, Ayabar ma shi ya 6are 6awon Ya zura mata a baki, taci kusan rabi kafin ya ƙarasa cinye sauran, bayan sun kammala suka sha ruwan su dake acikin bottle,

Haris ne ya kawar da kwandon Ya maida shi a ma ajiyarsa, Parveen kuma ta kwashe 6awon Ayabar da su ka 6are ta nufi toilet ta zubda su cikin trash can, Daga bisani ne suka gane cewa dare ya nutsa, Angel tace su jira tayi musu addu'a kafin su kwanta, Suka amsa mata da toh, Saukowa tae daga saman gadonta, tabar Danish zaune yana kallonsu, Cikin harshen larabci ta shiga karanto musu addu'o'in tana tottofa masu, suna amsa mata da ameen, bayan ta kammala, Hannah ce ta basu shawarar su Cire sabbin Uniform É—insu, Su sanya tsoffin gudun kada su yi squeezing,

In yaso gobe da safe sai su maida sabbin, Angel tace kin kawo shawara mai kyau, daga yanzu old uniforms É—inmu sun zama sleeping dress É—inmu, Kowa Ya ji daÉ—in wannan shawarar, without wasting time suka sauya Kayan jikinsu, Kowa Ya ninke nashi ya tura a cikin akwati, Suka É—auko Tsaffin suka sanya ajikinsu, daga bisani Kowannan su Ya nufi gadon shi ya kwanta Suka ja bargunansu, in a short time bacci yae awon gaba dasu, É—akin yae tsit ba ka jin hayaniyar komai, Mutun biyu ya rage angel da Danish, babu alamun zasu runtsa, Ae yau suna cikin farin Ciki,

Ya yi tsammanin zata dawo ta kwanta saman gadonta, sai kuma yaga ta nufi ƙopar shiga sashen toilet dinsu, har sai da ta shige, kafin ya sauko daga saman gadon yabi bayan ta, A bakin ƙopar toilet din ya la6e yana kallonta,

A yayin da take zuƙunne gaban tukunyar flowers din nan, kamar mai ta6in hankali, haka ta zauna tana ba furen Batul labarin abunda Ya faru Yau, hada ƴar ƙwallarta tace"Naso ace kina atare damu, a ka yi wannan shagalin, nasan zaki yi farin ciki sosai, saboda burin ki ne, kiga mun haɗa kan mu, Ina matuƙar ƙaunarki ƴar uwata rabin raina..." kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon hawayen da suka wanke mata fuskarta.
Chapter 117 · 0% Book details