← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 179

Sashe 132

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuciyarshi a hautsine Ya ƙarasa gefen gadon shi ya zauna, Ya rasa wa zai tunkara game da zancen haura war shi taga, so yake ya sami wanda zai faɗa mawa, ko don su je su ɗauko yarinyar nan da ya gani, tabbas yana ji aranshi cewa mutun ce ita ba Aljana ba, shiyasa abun ya tsaya masa aranshi, gani yake kamar bai kyauta mata ba, yanzu da ace sister ɗin shi ce, acikin wannan mawuyacin halin bazai ta6a ƙyale ta ba, duk runtsi duk wuya sai ya taimake ta, but why ya gaza taimakon ita wannan yarinyar, girgiza kai ya ɗanyi kamar wanda aka zunguri bayanshi ya miƙe Ya cigaba da yin zarya cikin ɗakin nasu, Ji ya ke kamar ya je ya faɗa ma Danish sai dai yana matuƙar kokwanto a kan shi, Kuma yana ji aranshi zaiyi wuya ya bashi haɗin kai don su shiga cikin kurkukun.

To waye zai iya faɗa ma zancen nan? Nutsawa yae cikin tunaninshi, nan take zuciyarshi ta Amabaci sunan ANGEL, tunawa yai da lokacin data watsa ma Giants ruwa a jikin su tana zazzaga musu masifa, hakan yasa shi yarda cewa Yarinyar ba ƙaramar jaruma ba ce, bata da tsoro kuma tana da ƙwarin gwiwa, dama tun ranar da aka kawo su ya lura da yadda take tafiyar da rayuwarta da kuma ta ƴan uwanta tamkar itace ta haife su, ta zama jagora acikin su, kuma ya fahimci cewa yarinya ce ita bata kai shekarunsu Hanna ba, amma tafi su wayau da hankali.

Tun da ya fara zarya acikin ɗakin, su parveen su ke ta kallon shi, hatta Danish ya ankara dashi, kamar akwai wani abu dake damun shi, sam bai lura da kallon na shi da suke yi ba, A ƙarshe zuciyarshi ta saƙa mishi cewa

_Ita kaÉ—ai ce zata Iya taimaka maka wurin nemo Æ´ar uwarka, tun da itama tana neman tasu Æ´ar uwar da aka É—auke, Idan ku ka haÉ—a hannu da ita, za ku iya cimma nasara, don haka karka kuskura ka faÉ—ama kowa, Ita kaÉ—ai zaka sanar mawa_

Muryar Azeeza ce ta katse mishi zancen zucin mashi ta hanyar yi mishi magana

"Ɗan uwa, me ka ke tunani ne? Tun ɗazu na lura da kai sai zarya ka ke yi mana acikin ɗaki, nace anya lafiya kuwa" Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi tare da juyar da kanshi Ya fuskanci inda azeeza take zaune ita da parveen. Kamar wasu tagwaye

"Ina tunanin rawar da zan koya ma ku ne ko ba ku so"? Ya faÉ—i hakan ne don kar su yi tunanin wani abun ne na daban ke damunsa.

Har suna haÉ—a baki wurin cewa"Muna so mana, dama zuciyar mu duk ba daÉ—i wlh, kwanakin nan mun rasa farin cikin mu"

"Kada ku ta6a bari damuwa ta hana ku jin daÉ—in rayuwar ku, saboda kowa yana da damar da zai sanya kan shi farin ciki, yawan zama kuna tunanin zai iya haddasa muku matsala, just ku yi abunda ranku ke so, zaku samu farin ciki" acewar Gabriel

Parveen tace"Angel tana koya mana yadda zamu motsa jiki, da karatu sannan tana bamu tarihi da labarin gidan daddynta, har ma ce mata tayi wata rana zata yi ƙoƙari don mu fita daga cikin kurkukun nan........." natsuwa gabriel yai a yayin da yake sauraran maganar parveen, da alama ya ƙara samun wani abu da yake son ji agame da angel, da sauri ya nufi gefen gadon dasu azeeza suke zaune, shima ya zauna.

"Inaso ku bani duk wani labari da angel ta baku agame da rayuwar ta, da kuma abubuwan da ta koya maku" Buɗe ido sosai Danish yai daga can saman gadon shi yake kallon bayan Gabriel dake zaune gefen su parveen, Mamaki ne ya kama shi for what reason Gabriel zai dinga yi musu tambayoyi kan angel! Menene alaƙar shi da ita? Why yake son ji"? Miƙewa zaune Danish yai saman mattress ɗin, ya jingina bayanshi jikin bango, ya tsare su da ido, Tabbas da ace yasan dalilin da yasa gabriel ya tambayi su azeeza su bashi labarin angel da ya dakatar shi.

Parveen ce ta labarta mishi komai game da angel, tun zuwanta kurkukun da irin É—awainiyar da ta yi masu, har zuwa ranar da aka kawo su Gabriel cikin kurkukun.

Jinjina kai gabriel yai alamar ya gamsu da labarin da parveen ta bashi na angel,

Azeeza tace"mu taso ka koya mana rawar? Idon shi akan fuskarta yace"nafi so mu yi tare da angel, mu bari ta farka," su ka ce mi shi toh, zasu jira ta farka, Miƙewa Gabriel yae daga gefen gadon parveen, yana juyawa suka haɗa ido da Danish, ya ɗaure fuska, ta6e baki Gabriel yae tare da wuce wa Ya nufi nashi gadon ya zauna yana jiran farkawar Angel.

Lokacin da marece ya nutsa, suna zaune, Unaiza tafarka jikinta nata kerma hannayenta dafe da Cikinta, saukowa tai daga saman gadonta, da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, bayan ta shiga toilet ɗin agaban magudaji ta zuƙunna tana ƙwara amai, tamkar ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago, temperature ɗin jikinta ya yi zafi sosai, tana acikin mawuyacin hali, an rasa me zuwa wurinta ya taimake ta.

Tun daga cikin sashen toilet ɗinsu har izuwa cikin ɗakin su, Sautin kakarin amanta ne Ya karaɗe ko'ina, Ya addabi kunnuwansu, ganin sunƙi motsawa suje su taimake ta, yasa azeeza ta sauko daga saman gadonta, parveen hada cewa"Zuwa za ki yi? Baki ji abunda angel tace mana akanta ba? Salon saita shanye maki jinin ki ko"? abunda suke jima tsoro kenan shiyasa suka ƙi zuwa su taimake ta, shi kuma Danish abunda ya hana shi zuwa wurinta gudun kada yabar ɗakin Gabriel ya samu damar zuwa wurin angel, saboda ya fahimci cewa so yake yayi magana da angel.

"Ai bata da lafiya, ba zata iya shan jini ba, ni dai zanje na taimake ta ne, kada ta mutu" azeeza ce tai maganar tare da kama hanya ta nufi sashen toilet dinsu, Cikin toilet ɗin da take jin sautin shesheƙar kukan Unaiza, ta buɗe ƙoparshi tasa kai ta shiga, A zuƙunne ta same ta, Baiwar Allah taji jiki, Cikinta ya ɗame dama bata ci abincinta ba, jikinta sai kerma yake yi.

Ƙarasawa gabanta Azeeza tayi fuskarta da alamun tausayinta ta zuƙunna suna fuskantar juna, bata ta6a tunanin wani daga cikinsu zaiji tausayinta ba har yazo wurinta sai ga azeeza tazo, daƙyar take kallonta saboda nauyin da idanuwanta su ka yi mata, sunyi luhu luhu da su kamar ƙwayar cikinsu zasu faɗo ƙasa launin idon nata ya ciza, la66anta sun yi suntum, sai nishi take yi tana matse cikinta.

"Sannu sister, baki da lafiya ne"? Bata samu damar amsa mata ba, azeeza ta kuma cewa"Pls talk to me, I wanna help you." Ganin taƙi tanka mata yasa azeeza ta Miƙewa tare da nufar inda bucket ɗinsu yake, ta tarba shi bakin fanfo ta kunna ruwa ya soma sauka acikinsa, Sai da yai rabi ta ja bokitin tana nishi don ba ƙaramin nauyi yayi mata ba, gefen unaiza ta ajiye bokitin, kafin ta karkatar dashi ruwan cikin ya kora aman da tayi dukan shi, Sauran da ya rage, ta taimaka mata wurin wanke fuskarta, ita kanta azeeza sai da gabanta ya faɗi jin irin zafin da jikin unaiza yae, lokacin da ta ke wanke mata fuskar da hannunta, kwata kwata babu ƙoshin lafiya atattare da ita, hada baki ta kuskure mata.

"Mu koma É—aki, kinji" a wahalce ta É—ago da ido tana kallon azeeza ta É—an girgiza mata kai, yayin da take cizon lower lip É—inta, wani irin raÉ—aÉ—in azaba take ji.

"Pls ki yi min magana mana, ni inaso na taimake ki ne" runtse ido unaiza tayi na É—an wani lokaci, azeeza har ta gaji da tsayuwa, ba dan tana jin tausayinta ba da tuni ta jima da komawa dakin su,

Tana so ta yi ma azeeza magana sai dai ta kasa motsa la66anta, jini har ya fara bleeding ta hancinta, ganin hakan yasa hankalin azeeza ya tashi, da gudu ta nufi cikin ɗakin su, a sukwane ta faɗo Ciki, Hankalinsu Naufal ya dawo kanta, muryarta har tana shaƙewa wurin faɗin"Ƴar gidan daddy bata da lafiya, Hancin ta yana bleeding, dan Allah ku zo ku taimake ta" Shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata, duk da sun tsorata da jin abunda ta faɗi,

Ran azeeza ba ƙaramin 6aci yae ba, hawaye har sun fara wanke fuskarta, cikin ƙunar rai tace"wai ba zaku zo ku taimake ta ba"? Kamar kurame sai dai suka bi ta da ido, fuskarta a hautsine ta nufi gadon angel, tana bubbuga ƙafarta tana ambaton sunanta

"Angel wake up, ga ƴar gidan daddy can bata da lafiya, ina ta roƙon su akan su zo mu taimake ta amma sun ƙi saurarana"

tana kuka tana magana, Daƙyar ta samu Angel ta farka, tana faman yamutsa fuskarta da tayi jawur, saboda kukan da tasha, A hankali ta tsayar da idanuwanta kan fuskar azeeza dake ta kuka, Muryarta adisashe ta furta"meya faru ne"? Cikin shessheƙar kuka azeeza tace"Ƴar gidan daddy ce, tana acikin toilet bata da lafiya hada jini a hancinta, ina ta roƙonsu akan su zu su taimaketa amma sunƙi su saurare ni"

Ɗaya bayan ɗaya angel tabi kowannansu da kallo, ita Sarah bacci ne ya ɗauketa bayan ta gama yankar akaifar, amma sauran idonsu biyu, lokaci ɗaya ta fahimci dalilin dayasa suka ƙi zuwa su taimake ta, saboda tace musu ita mayyace, zata iya shanye musu jini, duk da ita ta yi hakan ne don ta sanya musu tsoronta acikin zuciyar su, gudun kada ta lalata musu rayuwa.
Chapter 132 · 0% Book details