← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 179

Sashe 141

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rashin fahimtar zancenta su ke kallonta, A lokacin tafara dawowa cikin hayyacinta jin sautin muryoyinsu akanta, Wani irin matsanancin ciwon kai ta ke ji, Hannunta ɗaya dafe da goshin ta, da taimakonsu Hanna Ta miƙe zaune tana faman yin shessheƙar kuka, Idanuwanta har sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, daƙyar ta buɗe su, sunyi jawur dasu, awani irin galabaice take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya............'

"Angel ki yi mana bayani meya faru daku ne? Meyasa aka tafi da Danish! Jinin menene Agaban rigarki? Da wuyanki'? Kamar Æ´an jarida haka suka tsareta da tambayoyi.

"Dan Allah ki fidda mu daga cikin ruɗanin da mu ke, mun ga ɗazu kun fito toilet Jini duk ya wanke fuskar Danish, ba mu gasgata abunda idanuwanmu suka nuna mana ba, Kafin mu yi wani yunƙurin Giant Yazo ya tafi Dashi" Naufal ne yai magana maganar,

Cikin muryar kuka parveen ta soma magana"wlh muna acikin matsanancin tashin hankali Angel, Mun rasa gane meya faru ne! Pls ki yi mana bayani, " Sai da ta gama sauraransu ɗaya bayan ɗaya, Muryarta a raunace ta furta sunan gabriel ba tare da ta ƙarasa maganar ba, Sai nishi take yi,

Harsuna haɗa baki wurin cewa"Me Gabriel yai masa? Shi ne Ya kashe mishi idon"? Haris yace"idan ma shine Ya ta6a shi, gashi can kwance ƙasa a sume mun yi mashi bugun tsiya"

Zafafan hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskarta, Ko ƙarnin jinin jikinta basa ji, don bashi bane agabansu, Magiya suka dinga yi mata akan ta faɗa musu abunda ya faru, Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana faman lumshe idanuwanta kafin daƙyar ta motsa la66anta.

"Bazan iya tuna komai ba, dan Allah Na roƙe ku, Ku ƙyale ni, kaina ciwo ya ke min," Ba don sunso ba, suka rabu da ida, babu wanda ya ƙara tambayarta, duk da sun fahimci kaɗan daga cikin abunda ya faru tsakanin Gabriel da Danish, sai dai basu san menene ya jawo da har faɗa ya kaure a tsakaninsu, kwantawa ƙasa angel tayi idanuwanta na fuskantar ceilling, Jikin ta duk ba dadi, bakomai take tariyowa ba face abubuwan da faru kafin zuwa lokacin daya rasa idonshi, Bawan Allah ya dinga bibiyarta duk don kada Gabriel ya samu damar Yin magana da ita, ashe tsautsayine ke bin shi. Sosai ta fashe da ku ka.

"Angel kina ƙara jefa mu cikin damuwa, tun da ba za ki faɗa mana abunda ya faru ba, Zamu jira har zuwa lokacin da za'a dawo mana da ɗan uwan mu wlh idan har ya tabbatar mana da abunda muke hasashe to kuwa tabbas Ba zamu ƙyale Gabriel ba, dole ya fuskanci hukunci dai dai da abunda ya akaita ma Danish ɗin mu! sai ya yi danasanin zuwan shi cikin kurkukun nan!" Naufal ne yai maganar yana fitar da huci, Haris yace"Ae basai mun tsaya jiran Danish Ya dawo cikin mu ba, Idan har Angel taƙi faɗa mana gaskiyar abunda ya faru dashi, Zamu tsare Gabriel ne ta ƙarfi sai ya faɗa mana abunda ya aikata mashi, "

"Wannan wata irin rayuwace! Muna cikin jimamin rashin Æ´ar uwarmu batul, ga wata masifa ta kunno kai, Ni bansan meya haÉ—a Gabriel da Danish ba, Shi da babu ruwanshi da shiga sabgar da bata shi ba, bana tunanin Danish ne ya fara tsokanar shi, Gabriel shine mai laifin'!! Deeja ce tai maganar fuskarta a yamutse,

"Bawan Allah Hakanan An naƙasa mishi rayuwarshi, wlh ba zamu ƙyale Gabriel ba, dama can ni bai kwanta min araina ba, don kawai yaga yana da ƙirar ƙarfi saboda tsabar mugunta yake neman lahanta mana ɗan uwanmu" Acewar Javed, kowa sai tofa Albarkacin bakinsa yake yi, Sai faman tada jijiyoyin wuyansu suke yi, dole ne su damu bayin Allah, Suna matuƙar ƙaunar shi, duk da irin halin ko'in kulan da ya ke nuna musu wani lokacin, hakan bai canza ƙaunar da suke yi mashi ba, ga yunwa suna ji amma damuwa tahana su fahimci hakan, don bata cikin su suke yi ba.

Babu wanda ya lura da chinonsu da ya farka daga bacci, Idon shi bai sauka akan komai ba, Sai kan kayan abincin da aka kawo mu su, Saukowa yai daga saman gadon shi, Yaje ya samu wuri saman dining carpet É—in su ya zauna, Ya dunga kwasar abinci yana cusawa abaki Yana ci yana satar kallon su, kamar munafuki,

Parveen ce ta lura da abunda ya ke yi, aikuwa rai amatuƙar 6ace ta nufi inda ya ke, tana ƙarasawa ta ɗauki Burger ta kifa mashi ita saman fuskarshi, ta dagargaje ta tare da cunkusa mashi har cikin hancinshi tana faɗin"munafuki Kanaganin muna kukan rashin ɗan uwanmu amma kai ta abinci ka ke yi," Tsabar mugunta sai da ta 6ata mashi fuskarshi yai ta kuka yana buge hannunta, kamar zata kashe shi, daƙyar ya samu ta ƙyale shi ta koma wurinsu Haris ta tsaya tana hangen Majnun da ke ta yin birgima a kasa.

"Azeeza ɗauki ruwan nan ki watsa ma wancan ƙaton a saman fuskarshi," Haris ne yai maganar, Dama kamar jira take yi don ba ƙaramin damuwa tayi da Gabriel ba, Allah yayita da tausayi, Hannu biyu tasa ta kimkimi bokitin zuwa gaban gabriel, A saman fuskarshi ta yayyafe mashi ruwan, nan take yaja dogon numfashi tare da saukr ajiyar zuciya,

"Sannu Gabriel," muryar azeeza ce tasa shi yunƙurin buɗe idanuwanshi, zuƙunnawa ta yi saman gwiwowinta agaban shi, tare da kai hannayenta saman kanshi ta ɗago da shi ta kwantar saman cinyoyinta, Ganin ya farka yasa su haris Tunkarar shi Da niyar su takurasa akan ya faɗi masu me ya yi ma Danish, Idan yaƙi faɗa musu zasu ninka mashi bugun da su ka yi mashi ne, sai dai kafin su kaiga ƙarasawa inda ya ke muryar Angel ta katse masu hanzarin su.

"Haris kada ku ce zaku buge shi, saboda ba laifin shi bane abunda ya faru, shima bada son ranshi ya akaita mashi hakan ba........" daƙyar take magana duk don kada su bugi gabriel yasa take Ƙoƙarin faɗa masu abunda ya faru, duk da ta 6oye musu Ainihin dalilin faruwar hakan, ta dai ce musu tsautsayi ne da ƙaddara suka ja har Gabriel ya naushi idon shi, ba tare daya sani ba, sun ɗan samu sa6ani ne akanta, haris yace taya zasu yarda da maganarta? Wani irin tsautsayine wannan da har danish zai rasa idonshi ɗaya? Kawai saboda da ita zasu kama yin faɗa? Shifa bai fahinci zancen ba! Anya kuwa taga uban jinin da ya wanke toilet ɗinsu, Ga shi nan har a jikinta, Ya ƙara da cewa bazasu yarda ba, dole shima Gabriel su cire mashi idon shi ɗaya, in yaso Giant sunzo su ɗauke shi shima akaishi treatment room ɗin don ayi jinyarsu atare!! ganin dagaske haris ya ke yi Ne yasa tai saurin cewa"Danish bai rasa idonshi ba, da kanshi ya faɗa min cewa lafiyar shi ƙalau, babu abunda ya sami idon shi, kada ku yi gaggawar yanke hukunci, ku jira har zuwa time da za'a dawo da shi.

Angel taci wahala kafin ta samu ta shawo kansu, ba don sun haƙura ba, sun dai jira ne zuwa lokacin da za'a dawo musu dashi don suga idan idon nashi yana nan ko ya naƙasa. Yinin ranar babu daɗi su ka yi shi, sai wuraren marece Ne suka ɗan motsa, Da taimakon mazan suka gyara toilet ɗin daya 6aci da jini tass suka wanke shi, kamar wani abu bai ta6a faruwa ba acikinsa, Har wajen shi zuwa bakin ƙopar shiga sashen duk suka wanke, Bayan sun gama suka gyara cikin ɗakin nasu, Ko'ina ya dawo fes sai dai zuciyoyinsu a ƙuntace su ke, ƙarfin hali kawai suke yi babu wani mai lafiya a Cikinsu, sai da marece ya nutsa tukunna su ka ci abincin su, banda Angel da mazan cikin su, ko kallo abincin bai ishe su ba.

Hannah ta yi fama da Angel akan taje ta yi wanka ta wanke uniform ɗinta idan ma bazata iya ba, ita zata wanke mata uniform ɗin da kanta, Amma ta maƙe kafaɗa, gani take kamar inta wanke jinin Danish dake ajikin Uniform ɗinta shikenan bazata ƙara ganin shi, shiyasa taƙi zuwa tai wanka.

idan mu ka koma 6angaren Gabriel, Bawan Allah azeeza ce kaÉ—ai ta damu dashi, ganinta ya ke kamar Æ´ar uwarsa daya rasa, saboda mutuncin da ta yi mashi, Ita ta wanke mashi tsoffin uniform É—inshi da suka 6aci da jinin Danish, tun bayan da yayi wanka, Ya cire su ya bata, Ya maida tsoffin a jikinsa.

Saman Gado ya koma ya kwanta yanata juyi kanshi na sara mashi, Har sai da ya samu bacci ya ɗauke shi tukunna ya ji sauƙin ciwon nashi, A taƙaice Cikin kwanakin Nan Jin daɗin su Ya zama ragagge, me faranta musu rai Angel babu lafiya, Gashi taƙi zuwa ta yi wanka ta cire kayan Jikinta, Ta zama ƙazamar ƙarfi da yaji, duk akan Danish, kwana ɗaya da faruwar abun ko ruwa bai gifta ta maƙoshinta ba, ta haranta ma kanta duk wani jin daɗi ta ƙuntata sosai, A daren ranar da aka tafi dashi, gefen gadon shi ta kwana a zaune kamar gunki,

A cikin kwana na biyu ne su Deeja suka tasa ƙeyarta gaba akan taje tayi wanka idan ba haka zasu yi mata, Su kan su tsananin tausayinta su ke ji, Ba irin lallashin da basu yi mata ba, amma taki sakewa, hatta Haris daya fi kowa Kusanci da Danish Ya haƙura yabarwa Allah tun da ba yadda za su yi, babban abunda yafi damunsu shine awani hali ya ke aciki? Ya idon shi ya ke? jikin shi da sauƙi ko akasin hakan?
Chapter 141 · 0% Book details