Sashe 24
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wucewarsu keda wuya cikin dajin,Wata kyakkyawar bafullatanar daji, fara tass Jawur da ita, sanye cikin kayansu na al'ada, Ta bayyana hannunta ruƙe da sanda, siririyace Bata da ƙiba ko misƙala zarratin gata doguwa sam6al, Amma akwai dukiyar fulani cike tab da ƙirjinta, ga yalwataccen gashin kai dake gareta mai tsayin gaske, anyi mata kitson kalaba,Wanda yasha ado da duwatsu,wutsiyoyin gashin sun sauka har tsakiyar bayanta, ga wasu da suka zubo ta gefe da gefe na fuskarta,
Tabarakallahu ahsanul khaliqin,Wasu dara daran idanuwa gareta Farare Ƙal kamar fatar farin Cikin kwai, Launin Idon nata Brown Colour ce, tana da kwarin ido sosai,Ga ziraran Eyelashes, Jagirarta tamkar anzanata saboda tsaruwarta, Ga wani dogon hanci da Allah yayi mata, siraran la66anta jawur dasu, Akwai kwalliyar ɗige ɗige asaman fuskarta har goshinta, Wuyanta na sanye da sarkoki, Haka hannunta ma akwai awarwaro,Tana da hujen hanci mai shegen kyau, idan tayi dariya kuwa wayyo Allah madarar kyau, Kai kace gonar audugace, Saboda kyan fararen hakoranta masu tsari, wani ƙarin kyan dimple biyu gareta wanda ko magana take yi, sai sun lotsa,A ƙalla Bazata Wuce shekara Goma sha Shida ba,
Tafiya take Yi a bayan shanayen tana Korasu da sandar hannunta, Wani Lokacin Har rawa take Yi tana jujjuya Jikinta, Da alama ba ƙaramin daɗin yanayin garin take ji ba, ko kusa bata jin Sanyi, Burinta A ruwan sama ya sauka sosai don tayi rawa acikinsa, kamar yadda ta saba,
Fararen kafafuwanta na sanye Cikin takalma, Cikin harshen fulatanci ta soma raira waƙa,
Tana cikin yin waƙar ruwan sama ya soma sauka tamkar da bakin kwarya, Wani irin farin Cikine Ya lullu6eta, Cikin harshen fulatanci tace"Ni ɗin Jinin nasara ce, Mai nema mai samu,Mai nasara mai sa'a, Daga Yin magana Gashi ruwa ya sauka wuhuhu Sai ni DANEJO"
Rawa Tashiga Yi acikin ruwan Yayin da shayenta suka duƙufa Cikin dajin suna kiwo,
Juyi ta dinga yi tana karkaɗa qugu, ruwan saman duk ya jiƙe kayan jikinta sharkaf, sun manne mata,Ƴar rigar jikinta bata rufe Cibinta ba, Sai ɗan zanin data ɗaura, kallabin kuma taci ɗamara dashi,
Tana Cikin Yin rawar nan Cikin rashin sa'a ta ɗaura ƙafarta saman wani dutse dake a bakin Ramin da wannan tafkeken ruwan yake, Gaba ɗaya Dutse ya jirkice, A gigice Ta fasa Uwar ƙara, duk yadda taso Ta hana kanta faɗawa Cikin ramin amma hakan ya faskara, Domin kuwa gaba ɗaya Ta rufza Cikin Ramin, Tsulum Ta nutse Cikin ruwan,
Within Seconds Ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman haki kamar wadda tasha gudu, Gaba ɗaya gangar jikinta tana acikin ruwan, Iya kafaɗarta Ya tsaya, Idanuwanta sunyi luhu luhu dasu, Ƴan hanjin cikinta sun kaɗa, Hankalinta ya ɗunguzuma, Ba ruwan bane damuwarta, don tun tana ƴar ƙarama Baffanta Ya koya mata Ruwa, Babbar damuwarta shine taya za'ae Ta fito daga Cikin Ramin?
Rushewa tayi da kuka cikin harshen fulatanci ta soma Kiraye Kirayen Sunayen Ƴan uwanta donsu kawo mata ɗauki,
 "Inna wuro,Adda!Nanne!bawuro!Wayyo Allah Na babu wani akusa da zai kawo mun ɗauki"? tana Cikin wannan yanayin Shanayen ta Suka Leƙo Cikin Ramin Kamar sunji abunda take cewa, sun kewaye ramin suna ta kuka Emmoh !emmoh!
 Nuna su Tayi da yatsan hannunta"Banga amfaninku ba, Ciyawa kaɗai kuka Iyaci,"cike da takaici tayi maganar,Tana Cikin sambatun nan, Aka kwatsa Tsawa mai sautin gaske a gigice Ta nutsar da kanta Cikin ruwan don ba ƙaramin tsorata tayi ba
sosai ruwan saman Ke safka da ƙarfinshi,
Lokacin da danejo ta nutsa kanta Cikin ruwan a tsorace sakamakon Tsawar da aka kwatsa, Ba zato Ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Kyakkyawar Yarinyar dake kwance saman dutsen dake a ƙasan ruwan mai girma da faɗi, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, rigar Jikinta duk ta nannaɗe ta manne mata, biji biji take iya hangenta saboda ƙasan Ruwane
Waro ido waje daneju tayi a matuƙar tsorace take kallon Yarinyar, Shin mutunce ko aljan, Abunda ta fara sakawa aranta kenan, tunawa da wata tatsuniya da Nannensu ke basu, Akan macen kifi, nan da nan tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, A gaggauce ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman Mayar da numfashi,
Waswasi ta shiga yi acikin zuciyarta,Anya Yarinyar data gani Acikin Ruwan Mutunce? kodai ta macen kifi ce ko ɗan ruwa? ta jima tana wannan zancen Zucin Kafin Ta kuma nutsa kanta Cikin ruwan, Cike da fargaba ta nufi inda Yarinyar take saman dutse har Allah ya kawota Saitin Inda yarinyar take, Hannu biyu tasa Ta ɗaukota, Sama tadinga yi Har ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan, Natsuwa tayi tana kallon kyakkyawar yarinyar, Daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba, Allah kaɗai yasan Tun wani lokaci take kwance a ƙasan ruwan, Cikinta yayi 6ul6ul dashi,Da alama Ta shaƙi ruwa sosai,
Mu haɗu a next Page don jin yadda zata kaya, Jama'a an rasa shaidar da zata bayyana abunda ya faru? taya kenan za'a san meya faru dasu Taj?Su wanene waɗannan Mutanan masu haɗarin gaske? shin danejo zata taimaki angel? Idan ta taimake ta kuna tunanin angel yarinya mai ƙiriniya zata juri zama a hannun fulanin daji? ya zata rayu batare da mahaifinta ba? Duk dai acikin littafin kurkukun ƙaddara zaku samu amsoshin tambayoyinku, Tafiyar ta dabance salon ma na daban ne, a kullun burina in kawo sabon salo wanda ba'a ta6a ganin irin shi ba, Allah dai ya taimaka, Waɗanda suka shirya yin payment na kurkukun ƙaddara 500 ne, Suyi mun magana ta layi na 08103884440.*💋KURKUKUN ƘADDARA💋*
*dedicated to Aunty kubraâ¤*
_Daga alÆ™alamin Boss Batureâœï¸_
*E9*
At first sight da Danejo ta kalli fuskar yarinyar, sai taji tsananin tausayinta, Kuma nan take taji tana son ta taimaki rayuwarta.
Tunda ta ayyana hakan azuciyarta sai taji ta daina Jin tsoron tafkeken ramin Ramin, kodan saboda Yarinyar zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta ceci rayuwarta.
Dabarace ta fado mata aranta, Da sauri ta sanya hannu É—aya, ta Kwance kallabinta data É—aura É—amara dashi, ÆŠayan hannun kuma na dafe da yarinyar,
a saman bayanta ta goyata, kafin a hankali ta cigaba da matsawa cikin ruwan harta ƙaraso jikin gwamagwaman duwatsunan dake kewaye da wurin, jikinsu akwai hudoji, tsaf mutun zai iya daddafawa ya haura sama, Sai dai yana da matuƙar hatsari idan Duwatsunan Jiki suka 6allo, mutun zai iya jin mummunan rauni ga shi ita harda goyo.
Cike da fargaba danejo ta sanya hannayenta, ta dafa jikin dutsen A haka tadin ta tafiya tana bin jikinsu, Har Allah ya taimaketa ta hauro sama, tana faman Mayar da numfashi, da sauri ta sanya hannayen ta tare da warware goyon da tayi mata, ta sauko da ita a hankali ta kwantar da ita saman ciyayin, ɗagowa tayi tare da kallon shanayenta dake ta kuka, Ta wurga masu harara don ba ƙaramin haushin su take ji, daga gani dai akwai ƙuruciya atattare da ita.
Mayar da idanuwanta ta yi akan fuskar yarinyar, ta sanya hannu tana yaye sumar kanta data rufe fuskarta.
Tayi wani irin haske, ƙananun la66anta sunyi pink sosai suka ciza, duk irin kyan danejo saida tayi mamakin Tsantsar kyawun yarinyar data tsinto acikin ruwa.
Hannayenta ta ɗaura Asaman ƙirjinta tashiga dannashi, Nan take ruwa ya sona fesowa Ta bakinta da hancinta, cigaba da dannawa tayi har saida ruwa Ya daina zubowa, natsuwa Tayi tana kallonta, ta yi tunanin zata farka amma sai taga ko motsi ba ta yi ba, Da sauri ta jogana kunnanta saitin Zuciyarta don taji, idan tana harbawa a razane ta ɗago, ranta duk ajagule fargabarta kada ace yarinyar tarasa ranta.
Tunawa tayi da saman dutsen da ta ganta akwance, hannu tasa ta juyo da bayanta, ta cusa yatsun hannunta acikin sumar kanta data cukurkuɗe, har saida ta taddo fatar kanta fara sol, Anan taga Raunin data ji, ashe kantane ya ɗan fashe daga baya, sakamakon buguwa da kanta yayi jikin dutsen, A ruɗe danejo ta miƙe tare da daukarta, ta sa6eta saman kafadarta, Sam ta manta da shanayensu, hankalinta na akan Yarinyar dake Cikin mawuyacin Hali, Watsawa Tayi da gudun gaske tamkar zata tashi sama,
Tana Cikin gudun nan, wani bafullatanin Sanye cikin kayan fulani, da ƴar hularshi, Hannunshi ruƙe da sanda zai gifta, Karaf idanuwan shi sauka sauka a kan danejo dake ta tsala gudu,
Mamaki ne ya kama shi, É—aga murya ya yi tare da kwala mata kira, har cikin kanta tajiyo kiran da ya yi mata, Batare da ta juyo ta kalleshi ba ta amsa mashi da na'am,
Cikin harshen fulatanci Yace inata baro masu shanayen su kuma menene ta dauko a hannunta, tace ma shi suna can suna kiwo, Yaje ya cigaba da kula dasu,"daga haka bata ƙara cewa uffan ba,
Girgiza kai Bawuro yayi a ranshi yace bazata ta6a canzawa ba, daga haka ya nufi Cikin dajin inda shanayen su suke,
Danejo kuwa bata nufi ko'ina ba, Sai wuraren wasu Bukkoki rukuni rukuni a ƙalla sunyi Shida, A gefen ɗaya daga Cikin bukkokin wani tsohone tukuf zaune cikin kayan fulani, daga gefe kuma Wasu Manyan matane, Sun kwan biyu aduniya, Sai sussukar gero sukeyi, ga wasu kuma Ƴan mata su biyu matasa Suna 6arar masara,
Tundaga nesa Tsohon Ya hangota, da ƙarfi ya ambaci sunanta DANEJO, lokaci ɗaya sauran Mutanan suka ɗago suna kallonta, Ganin yadda take ta gudu yasa duk sukayi tunanin ko wani mugun abunne yabiyo ta, aikuwa aguje Suka nufi Cikin bukkokinsu kowa ya ɗauko makaminshi, Shima tsohon ya miƙe yana ɗangyale ƙafa ya shige cikin bukkar gefen shi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da Ma shi, (to fa yaƙi ya ta shi)
Ƙarasowa tayi tana ta faman haki, lokacin da suka lura da abinda ke ruke a hannunta sai kowa ya ajiye makaman yaƙinsa, suka tattara hankulansu akan yarinyar data ɗauko, A saman Shimfiɗar kakansu ta sauke yarinyar, tare da ɗagowa ta kalli kakansu cikin harshen fulatanci tayi mashi bayanin inda ta tsinceta, koda jin hakan Jiki Na rawa Ya koma Cikin bukkarshi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da ƴar jakkar fata, a gefen shimfiɗar ya sauke jakkar, Yace ma danejo ta nuna mashi inda taji ciwon, rubda ciki ta kwantar da ita, tasa hannu ta yaye sumar kanta, nan suka ga raunin da taji, Bude jakar yayi ya curo wasu magunguna nasu na gargajiya, wanda suke Yi ma mutun treatment dasu idan yaji ciwo,