Sashe 38
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
*DANISH* ne a tsaye hannun shi ruƙe da rigar shi, tun daga ƙasa har sama take kallon shi, kamar wani bugagge sai faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, shafaffan cikin shi tamkar wanda bai ta6a cin abinci ba, ranta a matuƙar 6ace ta miƙe saboda tsabar fusata bata ɗauki rigarta ta sanya ba, ta rufe shi da faɗa" kai wani irin jaki ne ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko?
Tunda ta soma balbale shi da masifa bai yi yunƙirin tanka mata ba, kuma bai motsa ba ya dai yi kasaƙe yana kallonta, sai da takai ƙarshen maganar tana haƙi cikin sanyin murya yace"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."kafin ya kai ƙarshen maganar, ta sunkucin bokitin ruwan da ta tarba, gaba ɗaya ta sheƙa mashi ruwan a jikin shi, sharkaf ta jiƙa shi,
Runtse idanuwan shi ya ɗanyi saboda ruwan daya shiga ciki, long eye lashes ɗinshi sun jiƙe sharkaf, hannu ya sanya tare da share ruwan dake akan fuskarshi, kafin ya buɗe idanuwan shi, ta yi saurin ɗaukar rigarta da ke a saman igiyar ta zurata a jikinta,
Tana huci ta ci gaba da kallon shi tana fadin"Zaka fita ko saina ƙara watsa maka wani ruwan? Ƙaton banza kawai matsalar ace mutun baida addini kenan, ko dabba tafi shi kan gado,"
A lokacin ya ƙarasa buɗe idanuwan shi, jinjina kan shi ya yi still bai tanka mata ba, ya juya ya fita daga cikin toilet ɗin,
Lamarin ya ɗaure mata kai, har ta soma tunanin kodai yana da ta6in hankali ne? In ba haka ba taya zai faɗo mata bagatatan Cikin toilet batare da ya tambayi ko akwai mutun aciki ba, idan ma ya yi tunanin babu kowa ne why bazai yi knocking ba? Guntun tsoki taja, aranta tace"Amma dai wannan anyi sullu6iyo, Shashasha sauna, next time idan ya kuskura ya ƙara faɗo mun irin haka, saina koya ma shi hankali," takai ƙarshen maganar tare da nufar ƙopar toilet ɗin da nufin ta rufe, hannunta ta ɗaura saman handle ɗin ƙopar, shiru ta ɗanyi jin alamun bai tafi ba, zurfi tunani ta shiga lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin ta manta bata yi locking ɗinta ba, kodai ya yi tunanin babu mutun ne shiyasa ya faɗo ciki? Don ta lura Haka suke yi idan suka ga ƙopa ba a datse ba, shi ne babu mutun a ciki, idan kuma suka ganta a datse to shi ne ke da akwai mutun, kenan itace ta yi ba dai dai ba? Da ace ta rufe ƙopar danish bazai iya shigowa ciki ba,
Ta6e baki ta yi, ta tura ƙopar ta rufe, ta koma ciki domin yin wanka,
Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin wankan, ta mayar da kayan jikinta, ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, tana buɗe ƙopar ta same shi a tsaye ya jingina bayan shi jikin bangon toilet ɗin, da alama jira yake ta fito ya shiga,
Wuce shi tayi zuwa cikin É—akin,
A tsaitsaye ta same su, banda mutun biyu Batool da Aziza,
"angel" hannah ce ta kira sunanta, ƙarasawa ta yi kusa da ita ta tsaya,
Fuskarta É—auke da murmushi tace"kin fito kenan, nima wankan nake so inyi ina jira su batool su fito sai in shiga,"
"Idan ku kayi wanka babu wani abu da ku ke shafa ma jikin ku"? Angel ce ta yi mata tambayar,
girgiza mata kai ta yi tare da cewa babu, mu ma haka muke zama duk in mu ka yi wanka,
"Comb fa? Ina so in taje gashin kaina",
"Guda É—aya ne muke da shi, kuma yana a wurin danish, da shi muke amfani in kina so sai in aro maki," da sauri tace"a'a na fasa" aranta kuma tace komai danish danish sai na koya mashi hankali, sullu6uyo kawai,
Tafiya ta yi zuwa gefen gadonta, ta zauna tana bin kowannan su da kallo,
Motsi buɗe ƙopa su ka jiyo daga can kusurwar da benan ya ke,
Nan fa su Hannah suka fara murna sunsan abinci ne za'a kawo masu,
Takun tafiyarsu tamkar na dawakai, saukowa su kayi daga saman matattakalar benan, Giants ne
Hannayen su É—auke da farantai, shiga ciki su ka yi a dai dai saitin carpet É—in nan suka É—aura sauke tray É—in,
Kafin su ka ja baya tare da goya hannayen su saman ƙirjin su,
Fuska a É—aure angel ke kallonsu, ko gunki bazai nuna masu iya tsayuwa ba, abun na ci mata tuwo a kwarya, wai su waÉ—annan mutanan su wanene? Basa ji basa magana, kullum kuma cikin shiga iri É—aya kuma sun 6oye ainihin suffar su,
Jin jina kai ta É—an yi aranta tace"A sannu zan gano ko su wanene ku,"
"Angel ki taso mu ci" Hibba ce ta kirata ganin ta yi zugudum saman gadon,
Saukowa ta yi tare da tunkarar inda suke zaune itama ta zauna gaban farantan, ta lanƙwashe ƙafafunta, mutun uku suka rage basu ƙaraso ba,
Javed yace"wai ina danish ya ke ne? da su batool, wani yaje ya yi masu magana su zo mu ci," yunƙurawa haris ya yi da niyar yaje ya kirasu sai gasu sun fito daga cikin ƙopar shiga toilet ɗin a tare, komawa ya yi ya zauna, gefen angel batool da aziza su ka zauna, danish kuma ya zauna gefen javed, yana fuskantar angel tun da suka haɗa ido, ta wurga mashi harara tare da murguɗa ma shi small mouth ɗinta,
Bin ta ido kawai ya yi, don baima san menene ta ke yi ba, haushin shi take ji ta ƙara jin tsanar shi saboda sharrin da yayi mata, da ya ce ƙirjinta kamar bangon ɗakin su, tsohuwa ma tafi ta abun kirki, kalaman nan sun baƙanta mata rai, kuma taci alwashin sai ya ɗanɗani kuɗar shi,
Batool ce ta ya ye jan ƙyallen da aka rufe saman trays ɗin, Hamburger suka samu tare da chicken legs na ƙosassun kaji anyi masu jar suya har wani maiƙo suke yi, kowa zai samu burger ɗaya da kuma Chicken leg ɗaya, a tray na biyu Tea pot ne sai jerin wooden Cups, faranti na ƙarshe basket ne mai ɗauke da kayan marmari, a gefe ɗaya kuma bottle waters ne' fuskar kowannan su awashe, baƙaramin daɗi suka ji ba, duk da sau ɗaya ake a basu abinci arana, Amma suna Ci su ƙoshi wani lokacin ne ba'a basu abun da zai ƙosar dasu, amma yau kam ba laifi, kowannan su Tunanin wanda zai rage yaci da anjima yake yi,
Batool ce ta zuzzuba masu kakkauran tea a kowani Cup, ta miƙa masu ɗaya bayan ɗaya, kusan atare suka kai baki suna sha, Idonta idon danish Sun hana juna sakat, gani take kamar wani abun yake ayyanawa aranshi tun da ya ganta babu riga a jikinta, nan take ta murtuƙe fuska, a ƙule tace"Stop looking at me"
"Ae bani ke kallon ki ba, ke kike kallona," amsar daya bata kenan, daga haka ya É—auke idonshi daga kanta, ya kai hannu ya É—auki burger É—inshi yana ci,
Yunƙurawa tayi tare da miƙewa, kowa yabi ta ido, batool tace"Har kin ƙoshi"? Fuskarta a hautsine tace"Zan ajiye ne da anjima inci" takai ƙarshen maganar tare da kai hannu ta ɗauki Chiken leg ɗinta, ta ɗibi fruits, ta kuma ɗaukar bottle water ɗaya,' duk fa don saboda danish tabar wurin, Saman gadonta ta koma ta zauna, kuma still bata daina kallon shi ba, lamarin ya ɗaure ma shi kai, shi dai baisan zunubin daya aikata mata ba, sam ta tsani ganin shi, abunda bata sani ba danish mugun shakkarta yake ji, shifa har yanzu kallon monster yake yi mata, bai yarda cewa itama mutun ce kamar su, saukowa ta yi daga saman gadon ta nufi gadon batool, ta zuƙunna bakin gadon ta zura hannu a ƙarƙashi ta janyo kwandon da batool ke ajiye ragowar abincin ta, a ciki itama ta ajiye Fruits ɗinta, apple uku sai ayaba guda biyu, ta raba cinyar kazar biyu ta tura rabi aciki, rabin kuma anan zuƙunne ta cinye ta, tana kammala ci ta buɗe murfin robar ruwan tasha rabi, bayan ta gama ta rufe kwandon, ta tura shi Ciki, kafin ta miƙe hannunta ruƙe da bottle water ɗinta, ta koma saman gadonta, daga ƙasa ta ajiye bottle ɗin,
a lokacin suma sun kammala cin nasu abincin, wasu sun rage cinyar kazarsu, wasu kayan marmari suka rage, kowa dai ya É—auki robar ruwanshi don ya ajiye zuwa anjima,
Tattara kayan abincin giants su kayi, A jere suka fuce daga cikin ɗakin, prisoners kowa Ya koma saman gadon shi, Anci an ƙoshi saura bacci, aikin su kenan Abun ba ƙaramin ɗaure wa angel kai yake yi ba, wai su kwata-kwata basa gajiya da rayuwar kulle? Daga ɗaki sai toilet, daga anci abinci kuma sai hawa gado ayi bacci, anya kuwa suna da lafiyar kwakwalwa?
Ganin da gaske bacci za suyi yasa tayi saurin cewa""Wai ku baku tunanin fita daga cikin kurkukun nan? Ko baku da ra'ayin yin rayuwar Æ´an ci ne, Cikin mutane?
"Ta ya zamu sanyawa ranmu fita daga cikinsa, bayan tsohuwa ta faɗa mana cewa mutanan dake awajen kurkukun nan baza su ta6a ƙaunar mu ba, wahala zamu sha tunda bamu da kowa a ƙarshe ma akashe mu da ranmu," yasmin ce ta bata amsa,
Rubina tace" bamu da kowa tsohuwa itace gatan mu, taya zamu yi tunanin barin kurkuku bayan babu ƙofar fita daga cikin shi? idan mun fita wurin wa zamu je"?
Guntun tsoki angel taja"daga anyi magana sai kuce tsohuwa, bansan me ta jiƙa ta baku kuka sha ba, wanda har ya gusar maku da tunanin ku, Amma ni inada tabbacin ba hakanan aka ƙyale ku ba, saboda babu mutumin da zai juri a kulle shi, tamkar yadda ake kulle dabba,"