← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 179

Sashe 175

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cigaba da magana yayi "Nasan har yanzu baki fahimci inda zancena ya dosa ba, " dafe bangon da ta jingina dashi yayi da tafin hannun shi,

"Tun kafin zuwan ki kurkukun nan munsan komai dangane da rayuwar ki! kaifin basirar ki da hankalin ki shiyasa muka kwaɗaitu da son zuwan ki tun da labari yazo gare mu na cewa kece ƙaddarar Prison! ," gaba ɗaya Ya gama ruɗar da ita, Duk tabi ta kakkame Jikinta.

"Ma'anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! Kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba nida mahaifiyata TSOHUWA TAMIRA!!!!" ƙara zare idanuwan ta tayi akan mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, Al'ajabi ne ya kamata Jin ya ambaci sunan tsohuwa tamira a matsayin mahafiyar shi!

"Ƙaddara kala Biyu ce, Mai kyau da mara kyau, A hasashen matsafa Idan suka killace ki a hannun su zaki zamar masu kyakkyawar ƙaddara, Amma idan suka bar ki a cikin Jama'a kina yawo shine zaki zamar masu ƙaddara mara kyau......." Kasa haƙura ta yi hakan yasa ta katse mashi maganar shi da cewa "Taya akai na zama ƙaddarar su"? Ta jefa mashi tambayar tana kallon shi da zararrun idanu.

"Kin manta me na faɗa maki?" Ko da ya ke halin ki ne Iya tambaya kamar ƴar jarida shiyasa kika gaza haƙura har saida kika katse mini magana ta" muryarta a dabarbarce tace "Bazan ƙara ba"

Gyaɗa kai Ya yi kafin ya ɗaura da cewa "rayuwarku tana a cikin haɗari mai munin gaske, musamman ɗan uwanki Danish"! Gabanta ne ya faɗi jin ya ambaci sunan Abun ƙaunar ta.

"Kasancewar shi garkuwar kurkukun ƙaddara, Matsafa sun ƙwallafa rai akan shi, Saboda shi ɗin tamkar wata nasara ce agare su, idan dashi baza a ta6a Iya rushe Ginin kurkukun ƙaddara ba, su kansu matsafan baza a iya cin nasara akan su ba, shiyasa suka bashi babban matsayi Na Prison Shield! A halin yanzu da na ke yi maki Magana, Ɗan uwanki Danish Ba cikakken Mutun bane, He's a dangerous Giant! Sun riga da sun bashi horon zama Giant duk wani zunubi da kika sani mai girma a duniyar nan na rashin imani da tausayi sun koya mashi, sun riga sun yi Transforming ɗin shi into a Giant, Horo Ne wanda ba mutane zalla suke basu shi ba harda baƙaƙen shaiɗanun aljanu, Harshe na bazai Iya furta maki abubuwan da su ka yi mashi ba da kuma wanda su ka sashi ya aikata kafin su tabbatar da komawar shi Giant........" Bai ƙarasa maganar ba ganin ta sulale daga jikin bangon zuwa ƙasa, zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, bakomai take hangowa ba face fuskar Danish ɗinta! Yanzu shikenan Sun canza shi zuwa Giant, Sun 6ata mashi rayuwar shi sun gur6ata mashi tunanin shi.

Zuƙunnawa Salsabeel Yayi agabanta Saman ƙafafuwan shi,

"Lokaci Yana tafiya, agurguje Zan faɗa maki yadda za ku Yi don ku gano ƙofar nan da zata fitar daku daga Cikin kurkukun nan, shine abu mafi muhimmanci agare ku!

Cikin shessheƙar kuka tace mashi "Idan dagaske ne Zaku iya taimaka mana mu fita zanji dadi sosai, sai dai Ni bazan Iya barin kurkukun nan ba tare da Danish ba, Dole in tafi dashi, in ba haka ba, Ni zan tsaya in yaso sauran ƴan uwan mu su ku6uta," sosai ta fashe mashi da kuka.

"Ni kaina bazan bari ku tafi ba tare da Danish ba! Domin kuwa shi ba iya garkuwar kurkuku bane, Ku kanku garkuwa ne agare ku! Fita prison ba abu bane mai sauƙi, Shi kaɗai ne zai Iya taimaka maku don ku gudu cikin sauƙi, dalilin da yasa nace haka saboda ginin kurkukun nan a cikin ƙurmin Daji ya ke, Idan har Allah yasa kuka samu damar fita zaku faɗa cikin Daji ne mai hatsarin gaske mai ɗauke da mugayen namun dawa, Sannan tafiya ce wadda ƙafa bazata ta6a iya yin ta ba, amma in dai Garkuwa Yana a tare daku bazai bari wata dabba ta cutar daku ba, Koda kuwa Zaki ne ko Kura zai Iya rikiɗa ya koma irin suffar su don yayi faɗa dasu harma yayi nasara akan su......." dakatawa ya ɗanyi da yin jawabin, Itama Angel tuni ta dakata da yin kukan tana kallon shi, Zuciyarta cike da mamaki haɗi da rudanin maganganun shi, Kuma daga gani ba ƙaramin mutun bane.

"Bana so ku ƙara Wata ɗaya a gidan kurkukun nan saboda muna gab da shiga watan da za'a gabatar da Black Night, taro ne na matsafan duniya da zasu halarta a gidan kurkukun nan daga ƙasashe daban daban zasu zo, ranar gwada rashin Imani, ranar zubda jinin prisoners, Idan muka bari ranar ta riske ku a cikin kurkukun nan, bana tunanin ɗaya daga Cikin ku zai Rayu! Dalilin da yasa suka daina zuwa ɗaukar ku saboda sun dakatar maku da Jinin al'adar ku na mata saboda tanadin da su ke yima wannan ranar, tsawon watannin da kuka ɗauka ba ku yi Jini ba, a ranar zasu yi maku sihirin da zaisa ya dawo maku gadan gadan don su gwada rashin imani akan ku......" Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yayi ba, Idanuwanta azazzare ta ke kallon mask ɗin fuskar shi, tsigar jikin ta duk ta tashi haiƙam jin abunda yace,

"Lokaci Yana ƙure mini, Yanzu Zaki Iya yi mini duk wata tambaya dake a cikin zuciyar ki" Numfasawa tayi kafin ta soma jera mashi tambayoyi akan abubuwan da suka cunkushe mata kwakwalwar ta.

"Ka ce mini kai ɗan tsohuwa Tamira ne! Dama tana da ɗa? Da farko ta ta6a faɗin cewa da ace ta ta6a yin aure da tuni ta yi jika dani, daga bisani kuma ta gaya min cewa Itama prisoner ce kamar mu tun tana ƙarama aka kawota gidan kurkukun ƙaddarar harta girma ta yi aure harta haifi ya'ya da jikoki, kaina ya ɗaure, Kuma meyasa ku ke son ɗaukar Fansa? Sannan taya za'ai mu iya ganin ƙofar da zata fitar damu daga Cikin kurkukun, Bayan haka inaso insan ta yadda zamu taimaki ɗan uwanmu Danish Ya dawo Cikin hayyacin shi, menene dililin dayasa ake kira na da Ƙaddarar Kurkuku? Itama ƴar uwata Batul Akwai sunan da aka sanya mata a bayan rigarta Heart beat of prison, na jima inason sanin meyasa aka banbanta mana uniform ɗinmu dana sauran Ƴan uwanmu? Suwane ne keda gidan kurkukun nan? Waye ya sadaukar dani?" tun da ta fara jera mashi tambayoyi bai katse ta ba, har sai da takai ƙarshe tukunna ya soma magana a tsanake.

"Kamar yarda na faɗa maki da farko haka zan maimaita maki a yanzu, Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira! Ni kaɗai ne ɗa da ta haifa, wata'ƙil ta gaya maku hakan ne gudun kada asirinta ya toni a fahimci cewa Kamar tana son kusan wani abu dangane da rayuwar ta ne, wanda Yin hakan Babban matsala ce agare ta, Shiyasa ta ke yi maku ƙarya a kalamanta, Dalilin daya sa muke son ɗaukar fansa Saboda mahaifi na da su ka yi silar mutuwar shi, Babban malami ne wanda duniya tasan da zaman shi ana kiran shi da Habibullah, Yana ɗaya daga cikin manyan Malamai na duniya masu zagaye ƙasashe domin yin da'awa, Allah yayi mashi baiwar ilimi, ɗan ƙasar Nigeria ne, Tun da ya ke bai ta6a yin aure ba, a zamanin shi baida burin daya wuce Yayi koyi da manzo SAW wurin karkato da hankulan waɗanda basuyi imani da Allah ba don Ya Musuluntar dasu, Ita kuma mahaifiyata tsohuwa Tamira Ƴar Ƙasar America ce ba musulma bace bata da addini, Farkon haɗuwar su da mahaifiya ta yaje ƙasar Dubai domin gudanar da gasar Musabaƙa ta karatun alƙur'ani ta duniya da aka gayyace su tare da manyan malamai na sauran ƙasashen duniya A babban birnin Dubai wato Abu dhabi, A can Allah ya haɗasu itama lokacin taje ƙasar Gudanar da harkokin kasuwancin ta, kamar yarda ya bani labari tun da yake bai taba sanyawa ran shi zai so wata ƴa' mace har takai su ga yin aure ba, sai gashi ƙaddara ta haɗa shi da auran Baturiya ƴar ƙasar america, bakomai ne yasa shi amincewa da tayin soyayyar da tayi mashi ba, face don ta nuna tana so ta musulunta in har ya amince zai aureta, kinji dalilin daya sa har ya aureta ba tare da sun samu matsala ba, kinsan su turawa da zarar yaro ya haura 18 years Yana da ƴancin da zai yi komi yake so, Iyayenta basu son auran sai dai ba yadda zasu yi dole suka haƙura tabi za6in ranta, Bayan sun dawo ƙasar Nigeria ne ta musulunta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma dangin shi ba, tun da iyaye na suka yi aure basu ta6a haihuwa ba, Har saida auran su yakai shekara goma tukunna Allah ya ƙaddara samuwata, A lokacin sun manyan ta mahaifina Ya tsufa, Ita kuma Mahaifiya ta tana da shekara arba'in a duniya.." dakatawa ya ɗanyi da yin Maganar, Angel ta zuba mashi ido tana jiran yaci gaba da bata labari.
Chapter 175 · 0% Book details