← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 179

Sashe 18

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

A washe garin Ranar, Angel ta farka bata same shi a saman gadon su ba, Tunda ya tafi sallar a suba bai dawowa ba.

Ita kaɗai acikin gidan, Ga yunwa tana ji, fito wa ta yi daga bedroom ta sauko down kaitsaye ta nufi cikin falo, Fridge ta buɗe ta ɗauko Fura a cikin roba, Ta koma saman sofa Tana sha, duk in taji kamar motsin mutun saita kalli ƙopar taga idan shi ne Ya shigo,

Wuraren ƙarfe tara na safe Ya shigo Cikin falon, A kwance ya sameta, Tana ta bacci, ga robar furar data sha a jiye saman table,

Ƙarasawa yayi a gabanta ya zuƙunna tare dakai hannu yana shafa gefen fuskarta, Yasan tayi neman shi har ta gaji, Shi kan shi baisan ya akai bacci ya ɗauke shi a masallaci ba, Kodan jiya bai samu isasshen bacci ba ne,
Kasa janye eye ɗinshi ya yi daga kan fuskarta, hakanan ya dinga jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa, sallamar uzair ce ta katse mashi kallon nata da ya ke yi, Miƙewa taj ya yi tare da juyawa Yana kallon shi,
Gaisawa suka fara yi, kafin suka rungume juna kamar yadda suka saba,
"Inason magana dakai" acewar uzair,"
Nuna mashi wuri yayi saman sofa"bismillah"
Zama Yayi saman 2 seater, taj kuma ya zauna a saman 1 seater, kallon kallo su kayi ma junansu na tsawon mintuna biyar batare da wani daga cikin su yace ƙala ba, Sai da taj ya gaji da zaman tukunna yace

"Ina sauraronka"?
A tsanake uzair ya soma magana"game da waÉ—annan mutanan da muka gani jiya"
"Suwa kenan"? yadda yayi tambayar tamkar baisan komai ba,
"Ina nufin waÉ—annan Miyagun da suka Kashe malamin nan da Æ´a'Æ´an shi,
Wani irin kallo Taj ya yi ma shi"Wai dama ba mafarki bane"?

Harara uzair ya É—an jefa ma shi"take it serious pls, Banason wasa so nake muyi magana a kansu,'
Girgiza kai taj yayi"badani ba wlh, Na riga da nabar komai a matsayin mafarki, Bana so kasa ke tunamun a bunda ya faru jiya,"

"Kana nufin xamu ƙyalesu ne suna aikata 6arna acikin ƙasarmu"?acewar uzair ,A harzuƙe taj yace"ƙwarai kuwa, tunda bamu da yadda zamu yi da su, sunfi ƙarfin mu, mubar su da Allah shi kaɗai ne zai yi mana maganin su,

Uzair yace"Ba haka na sanka ba taj, Nayi tunanin zamu haÉ—a hannu a matsayin mu na Æ´an jarida wurin ganin mun fallasa su, don a É—auki mataki a kansu,"

Taj yace"Allah ya taimaka, Amma ni dai babu hannuna a ciki, kaima kuma ina gargaɗin ka akan ka manta da su, tamkar baka ta6a sanin su ba, In ba haka ba zaka jefa kanka cikin matsala ne , domin kuwa waɗannan mutanan da kake gani Shaiɗanu ne, sunfi ƙarfin hukuma ita kanta ballantana kuma mu da muke ƴan jarida"

Abu kamar wasa, suka soma gaya ma juna magana, Shi uzair yasa kafiya a kan saiya bi ƙwaƙƙwafinsu don ya tona masu asiri, Shi kuma taj yana ƙoƙarin fahimtar da shi irin haɗarin da zasu jefa kan su, a ƙarshe dai Uzair Ya miƙe rai a6ace yace"idan har ban tona masu asiri ba,tabbas zan ajiye aikina na ɗan jarida ne, domin ban cancance shi ba" yana kai ƙarshen maganar shi ya fuce, Taj dai yana a tsaye ya yi kasaƙe yana kallon bayan shi, har ya 6ace ma ganin shi,

Duk wannan surutun da su ke yi akan kunnan angel tun É—azu ta farka daga bacci, duk da bata fahimci me suka tattaunawa ba,

"Daddy faÉ—a kuke da Daddy uzair?" a É—an ruÉ—e Ya kalleta, da sauri yace"a'a, muna tattaunawa ne, game da zuwan Uncle abdallah, na faÉ—a mashi cewa Ya bari mu fara zuwa buzaye shi kuma yace dole mu jira su dawo Sai mu tafi atare"

Murmushi tasa ki"Nima nafi so mu tafi tare da su mommy adama"

"Me zaki Ci in kawo maki"?

"Komai zaka ci nima zanci" miƙewa ya yi tare da juyawa Ya nufi kitchen, don yau ba aikin safe gare shi, Sai wurin mare ce zai fita.

Zama tayi tana Jiran dawowar shi, almost 15 mins Ya fito hannun shi ɗauke da plate, indomie ce daga sama Kuma wainar ƙwaice, Asaman table ya ajiye masu,Kafin Ya koma kitchen ɗin Ya haɗo masu tea a cup biyu,Yazo ya ajiye gefen plate din

tare suka zauna Suna ci, still zuciyarshi a cunkushe take, Yana so ya taimaka ma uzair wurin fallasa asirin waÉ—annan mutanan ta wani 6angaren kuma Yana jin tsoran su jefa kan su Cikin masifa, tunda mutanannan sunfi karfinsu nesa ba kusa ba, Allah ne kaÉ—ai zai Iya dasu, ga kuma angle din shi bayaso wani abu ya faru da ita ta sanadiyar shi gaskia yana cikin tsaka mai wuya

Ya yi zurfi cikin tunani, muryar Angel ce ta katse shi, "Daddy!"

Firgigit ya yi tare da kallon ta, "Na'am!"

Fuskarta da alamun damuwa ta ce, "Tun É—azu ina ta kiran ka amma ba ka amsa mini ba. Daddy kamar kana cikin damuwa."

Girgiza mata kai ya yi, "Am ok, ba wani abu. Kawai ina tunanin rayuwar duniya ne mai ban al'ajabi, rashin tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu mutanen. ban sani ba neman duniya ne koko mene ne yake jan hankalin su har su manta cewa wata rana za su mutu? Kuma za su koma ga Allah, sannan duk wani abu da suka mallaka ba za a ta6a binne su da shi ba, a gidan duniya za su bar shi."

Tun da ya fara magana Angel ta ƙura masa ido tana kallon shi, sam ba ta fahimtar kan me yake magana. Shi kansa ya manta da wa yake magana? Abin ne ya dame shi yasa yake ta sambatu ko ya samu ya rage raɗaɗin dake cikin zuciyarsa.

HaÉ—a ido sukayi da ita, lokaci É—aya yaja bakin shi ya yi shiru, da mamaki akan fuskarta take kallonshi, can dai tace"Daddy, Meya faru"?

Ƙaƙaro murmu shi ya yi"halan kinji inata zuba ko? wani programme ne da zamu gabatar a gidan radion mu shine nake tsara yadda zanyi shi"

Murmushi tasa ki"Allah ya taimaka daddy, I wish u all the best' ya amsa mata da ameen,

*ANEELER*

A zaune su ke ita da uzair saman dining chairs suna fuskantar Juna, gaba ɗaya hankalinta na akan fuskar Uxair tunda ya ruƙe spoon yake ta jujjuyashi Cikin abincin da ta zuba ma shi a plate sam ya kasa cin shi sai kacaccala shi yake yi kamar ƙaramin yaro, ta lura da canzawar da yayi daga daren jiya zuwa yau kamar wani abu na damun shi bama kama bace tabbas akwai abinda ke damun shi.

Gyaran murya ta ɗanyi ma shi, Ya ɗago suka haɗa ido tace"My man, kaƙi faɗamun abunda ke damunka, tun ɗazu nake kallon ka, sam ka kasa Cin abinci why pls"?

Daƙyar ya iya bude baki yace"don't worry ur self am ok, just bana jin daɗin zuciyata ne,"

"daka daure ka faÉ—amun may be in sama mana solution"

Murmu shi ya ɗansaki cikin zolaya yace"Matsalar bata asibiti bace balle kice za ki yi mun allura inji sauƙi"

Ta6e baki ta É—anyi tare da mayar mashi da martanin murmushin "kana nufin matsalar data shafi asibiti kaÉ—ai zan iya magani"?

Girgiza kai yayi"karfa ki dauka da zafi, It was a joke"
Kallon shi kawai tayi kafin ta mayar da eyes É—inta akan abincin dake gabanta,

Wuraren ƙarfe shida na marece, taj, Yana daga kishingiɗe saman Sofa, jikin shi na sanye Cikin jeans da white shirt, a lokacin angel tana can cikin ɗakinta,

Ƙwanƙwasa ƙopar falon shi a kayi daga waje, A hakanlali ya ɗan buɗe i danuwans hi tare da tambayar wanene, Ba abashi amsa ba aka turo kopar ɗakin, uzair ya gani a tsaye Sanye da jallabiya, fuskar shi babu walwala, miƙewa zaune taj yayi yana kallonshi yace"Shigo ciki mana"

Ƙarasa shigowa Cikin falon yae tare da samun wuri saman Sofa ya zauna, batare da ya furta mashi komai ba,

"Meke damun ka ne aminina? naga sauyi sosai akan fuskarka"

harara ya dan jefa mashi tare da cewa"Kaine damuwata Taj, saboda kaƙi bani haɗin kai akan abunda nakeson Cimmawa"

Murmushin takaici taj yayi"cos You wanna get yourself into trouble shiyasa naƙi goya maka baya, Idan suka kama mu munayi masu leƙen asiri what do you think will happen next? They will kill us as soon as they find out that we are investigating them,"

Jinjina kai Uzair yayi"Yanzu haka zamu zuba ido ana aikata 6arna batare da Mun hana ba"?

"Ƙwarai kuwa, Saboda bamu da yadda zamuyi,illa iyaka Muyi addu'ar Allah ya kawo mana ƙarshen su, that's the only solution"

Jiki a sanyaye Uzair ya miƙe ya soma tafiya har yakai bakin fita daga Falon ya ɗan dakata
"Ka manta alƙawarin da mu ka yi ma juna tun kafin mu fara aiki'? shiru taj ya yi yana kallon bayansa,

Cigaba da magana uzair yayi" duk runtsi duk wuya zamu ƙarfafa ma juna gwiwa wurin ganin mun taimaki ƙasar mu, amma sai gashi kaine na farko daka fara sare mun gwiwata, Narasa goyon baya daga gareka, ji nake tamkar narasa wani sashe na jikina,"

Miƙewa tsaye taj yayi tare da nufar inda Uzair yake atsaye Ya soma magana"Ina jiye mana tsoron abunda zai biyo baya ne, akan idon mu suka kashe mutun da ƴa'ƴansa, a haka kuma ka ke so Mu yi bincike akansu?wannan fa ba aikin mu bane, shin wai kai baka tsoron asirin mu ya tonu su gane cewa muna bibiyar su?ko ba don saboda mu ba, ka tuna kana da mata ni kuma inada ƴa, So ka ke Mu jefa su cikin masifa ne? Yana kai ƙarshen maganar shi uzair yace"In sha Allah hakan bazata ta6a faruwa ba, Nidai inaso ka bani haɗin kai kawai"
Chapter 18 · 0% Book details