← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 179

Sashe 54

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shessheƙar Kukan Azeeza Taji, Tasan bai wuci fitsari take Ji ba, ganin ita kaɗaice idonta biyu Yasa ta sauko daga saman gadon, Ta je inda fitilun ɗakinsu suke tabi kowacce ta kunna ta, kafin ta ɗauko ɗaya tana haska Cikin ɗakin, A tsaye ta hango azeeza ta matse idanuwanta, hawaye sharkaf, ƙarasawa tayi da sauri ta ruƙo hannunta,
Ta rakata Cikin Toilet, Tayi fitsarin A bakin fita daga Cikin toilet area É—insu, Angel ta tsaya tana haska fuskar azeeza,
"Angel" taji ta ambaci sunanta, ba ta yi tsammanin zata Shaida ta ba,

"Taya akai kika gane ni ce"? tayi tambayar tana kallonta,

"Naji ajikina cewa ke ce, " shiru angel tayi na É—an wani lokaci suna fuskantar juna kafin tace"Azeeza kema kin tsane ni ko? Baki son ganina ? Shiyasa ko magana ba kuyi mun,' idanuwanta acike tab da kwalla tayi maganar,

Girgiza kai azeeza tayi fuskarta da alamun rauni attare da ita tace"ba haka bane angel, dai dai da rana ɗaya ban ta6a jin tsanarki acikin zuciyata ba, kawai ba yadda zamuyi ne, sai kina yi mana uziri, mu kanmu bamu jin daɗin abunda ke faru atsakaninmu, " takai ƙarshen maganarta, tare da rungume angel a jikinta, kusan atare suka fashe da kuka,
Cikin shessheƙar kuka azeeza take faɗin"ni nasan cewa angel ba cutar mu kike yi ba, kamar yadda tsohuwa take faɗa mana, ke mai son mu ce, kina ƙaunar mu, kamar yadda kikayi niyar taimakon mu, kada ki fasa angel,"

Kalaman azeeza ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sosai ta ƙara huggin dinta tightly a jikinta,

Suna Cikin wannan yanayin su ka ji sautin shessheƙar kukan mutun, da sauri angel ta saki azeeza, ta wurga idonta kan mutumin dake tsaye abakin ƙopa, Da fitilar hannunta ta yi amfani wurin haska fuskarta, bakowa bace face batool, fuskarta sharkaf da hawaye Allah kaɗai yasan tun lokacin da take atsaye tana sauraronsu,

Muryarta adisashe tace "Ki yafe mun angel, nayi kuskuran juya maki baya dana yi, bada son raina hakan ta faru ba, Na zauna nayi tunani duk irin ƙuntata maki da su haris su kayi dai dai da rana ɗaya baki fasa tashi tsakar dare Kinyi mana addu'a ba, saboda ƙaunar mu da kike Yi........" dakatawa tayi da yin maganar tana sauke ajiyar zuciya, kafin taci gaba da cewa"Bana so kiyi kokwanto akaina angel, nasan abunda ya faru cikin ƴan kwanakin nan zaisa Kiji aranki kamar bana ƙaunarki ne, ko kusa angel, har yanzu kina nan yadda kike acikin zuciyata,'

Saboda Jin daɗin maganar Batool batasan Lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, Matsawa batool tayi inda suke Ta janyo Angel ajikinta ta rungumeta sosai, Ta mika hannu ta ruƙo azeeza itama ta rungumota, atare suka cigaba da yin kukan,

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

Muryar Javed su ka ji yo daga bayansu

"Nima ina neman yafiyarki angel, duk da bana ɗaya daga cikin masu ƙuntata maki" raba jikinsu su ka yi daga cikin na juna, kowannansu idanuwanshi ya kaɗa yayi ja saboda kukan da suka sha, still hawayen basu daina sintiri saman faces ɗinsu ba,

Kallon javed su ka yi dake a tsaye, Shima da alamun nadama atattare da shi, cikin sanyin murya angel tace"basai kun nemi yafiya ta ba, saboda ba laifinku bane, nayi maku uziri tuntuni'

Ƙarasa shigowa Cikin toilet area ɗin yayi ya tsaya a kusa da su, sannan yace"Angel, muna so mu tabbatar da gaskiya, a tsakanin ki da tsohuwa, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da zamu shaida hakan," yakai ƙarshen maganar idon shi akan fuskarta,

"Ku bani lokaci, bi'iznillahi Zan kawo maku ƙwaƙƙwarar hujjar da zan wanke kaina, ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA BA GIDAN MARAYU BANE, SANNAN ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA AKWAI ALLAH WANDA YA HALICCE KU, BA DAGA SAMA KUKA FAƊO BA,"

Baƙaramin daɗin maganarta su ka ji ba, batool ta ruƙo hannayen angel biyu acikin nata, cikin natsuwa ta soma magana"Ina yi maki fatan nasara Angel, muna atare dake,"

Angel tace"Bana so ku nuna mun shirya agaban tsohuwa, Ku cigaba da pretending cewa Kuna goyan bayanta baku atare dani, ta hakanne zan samu damar bayyanar maku da gaskiya,'

Atare suka haÉ—a baki wurin amsa mata da toh, Kallon azeeza ta yi wadda ke atsaye tana jinsu amma bata iya ganinsu,

"Mu koma Ciki mu kwanta, Azeeza ta gaji da tsayuwa" ta ruƙo hannun azeeza, Batool da javed su ka yi gaba a cikin ɗakin suka yi ma juna sallama, Kowa ya wuce gadonshi, sai da tafara kai azeeza saman gadonta ta kwanta ta lullu6eta da bargo, kafin Ta koma nata gadon, daga ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, ta haye saman mattress ɗin taja bargo ta lullu6e jikinta zuwa saitin neck ɗinta, kasa runtsawa tayi, ɗan juyawa ta ɗanyi tare dakai idanuwanta saman shimfiɗar Danish, why Har yanzu ba a dawo da shi ba? Allah yasa dai ba jikin nashi bane yayi tsauri sosai ba, duk da babu sabo a tsakanin mu, naji na yi kewarsa sosai, inaso na sake ganin danish, Fatana Allah yasa adawo dashi, kada maganar batool ta tabbata na cewa duk wanda aka ɗauka ba'a dawowa da shi ya tafi kenan har abada! To wai ina ake kai su? Idan suna araye meyasa ba a ta6a dawo da su ba? Ni dai a iya sanina mutuwa ce kaɗai idan akayi ta ba'a dawowa!!!!!

ÆŠaura hannunta na dama tayi asaman goshin ta zagoyo da shi, idanuwanta na fuskantar ceilling,

"Menene ma'anar Gidan Kurkukun ƙaddara? A iya sanina Gidan Kurkuku Yana nufin Gidan Gyara hali, Amma wannan kurkukun meyasa last name ɗinshi Ya ƙare da ƙaddara! Dole ya kasance ɗaya Cikin biyu, Kodai kyakkyawar ƙaddara ko kuma mummuna, ' lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ware su, Zuciyarta Cike fal da tunani, Tun lokacin da daddynta ya gudo da ita daga Gidansu, Take lissafin kwanaki, bata ta6a bari lissafi ya kwace mata ba, ko babu calender tana iya hasashen Yau nawa ga wata, ku ma ta canka dai dai,

Tana Cikin Yin tufka da warwara, Tajiyo Takun Tafiyar Mutun, Tunkafin ma takai idonta kan wanda ya shigo ɗakin nasu, Ta yi hasashen tsohuwa ce, daga kwance ta wurga eye balls dinta kan tsohuwa dake shigowa Cikin ɗakin, Sanye cikin shigarta, ta gado jar doguwar riga me hula, hannunta ruƙe da kaskon turaren wuta, zagaye ɗakin ta soma Yi tana kora hayaƙin ta ko'ina, murmushin takaici angel ta saki, yau ta ƙudiri aniyar sai tayi mata magana ga da ga, batare da jin tsoro ba, ta mike tare da saukowa daga saman gadonta, Cikin sanɗa take tafiya har ta ƙaraso bayan tsohuwa ta Cigaba da binta suna tafiya atare, batare da tsohuwa ta ankara ba, kasa kunne angel tayi tana sauraran ɗalasiman da take karantawa, kai daga jin yadda take Karanto su zaka shaida cewa ba abun arziƙi bane, wani mugun abunne take ƙulla masu,

"Æ´ar nan Kina tunanin bansan Kina bin bayana bane"? Tsohuwace tayi maganar, batare da ta juyo ta kalli bayanta,

Koda angel taji maganarta, bata ji wani fargaba ba, saima ƙwarin gwiwa da ta samu na cewa" nasan kinsan ina bin bayanki mana, Taya ki aiki nake yi, naga kina ta wahala ke kaɗai, Me zai hana yau Ki bani Kaskon turaren wutar In rage maki aiki"? juyowa tsohuwa tayi suka fuskanci juna ita da angel, Wani irin balagaggen murmushi ne ɗauke akan fuskarta tsohuwa,

Ɗaure fuska angel tayi tamau ba fara'a ko misƙala zarratin,

"Bibiyata kike Yi kenan? Da alama har yanzu baki daddara ba, Ina mai baki shawarar Ki ajiye makaman yaƙin ki, Ki yi rayuwarki tamkar salihar dabba, ki ajiye wannan Girman kan naki, da taurin kan nan da kafiya, Muyi rayuwa Cikin salama,' takai ƙarshen maganar tana washe wawulan bakinta,

Still angel bata tanka mata ba, Jira take ta kammala Suratan nata marasa kan gado,

"Ƴata faɗa da aljani ba riba, Ko har yanzu Kina tunanin zaki Ci galaba akaina ne eye? Tsabar takaici Ji take kamar ta shaƙo wuyan matar, mummunar banxa kawai, ta ambaci hakan acikim zuciyarta, a fili kuma tace"tun yaushe kuma? Cin galaba akanki tuni na fara, bari na faɗa maki abunda kike tunanin bansani ba,' ƙura mata kwarkwararrun idanuwanta tsohuwa tayi tana jiran jin me zata ce,
"Kafin na faɗa maki irin nasarar dana fara samu akanki, zan fara faɗa maki babban kuskuran da kuka tabka," fuskarta ɗauke da murmushi takai ƙarshen maganar, Tsohuwa dai tayi kasaƙe tana kallonta,

A tsanake angel taci gaba da cewa"Kuskuren kuwa shine, ɗauko ni da ku kayi zuwa Cikin gidan Kurkukun nan, ganganci ne mutun ya ɗauko ajalinsa ya raine shi da hannunsa, ada ina tunanin meyasa na kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara? Amma yanzu na samu amsar tambayata, inaji araina Ba hakanan Allah ya ƙaddara mun rayuwa acikin gidan kurkukun nan ba, babu shakka Nice zanyi silar tarwatsewar........" bata kai ƙarshen maganar ba, Sakamakon wata ƴar iskar dariya da tsohuwa ta fashe da ita, Ta wage wawake bakinta, Haƙoran nan jawur dasu, kasancewar angel na a kusa da ita, Da sauri ta kawar da kanta gefe Jin ƙarnin Jini na fita daga cikin bakin tsohuwa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai zuciyarta ta shiga ruɗani, gaba ɗaya ta rikice tana zare ido, fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki da aljabi ta ɗago tana kallon tsohuwa a lokacin ta dakata da yin dariyar,

Da shaƙaƙƙiyar Miryarta ta tsoffi tace"Your dream will neva come true angel, Wasiƙar jaki ce kike saƙawa aranki, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, har yanzu akwai sauran kuruciya atattare dake, shiyasa nake yi maki uziri, bakisan komai game da gidan kurkukun ƙaddara ba, ki kalli ginin da kyau, Tsohon ginine wanda tun kafin zuwana duniya aka ƙirƙire shi,"

Angel fa ta shiga ruɗani, Idanuwanta azazzare take kallon tsohuwa, sama sama take fahimtar zancenta, wata irin narkakkiyar zufa ce ta shiga tsastsafo mata ta ko'ina ajikinta, saman goshinta duk ya jiƙe da zufa, bakomai ya tsara mata arai ba, face wannan ƙarnin Jinin da taji abakin tsohuwa,
Chapter 54 · 0% Book details