← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 179

Sashe 94

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cool voice ɗinshi ce ta ratsa kunnanta"its me, me kike yi agaban gadon batool? Ko kinzo ne ki sace mana steak ɗin mu da aka ajiye mana ne? wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar danish, Ta harzuƙa sosai ashe shine ya firgitar da ita, tayi matuƙar yin mamakin taya akai ya iya ganinta Cikin duhu? Kuma har yasan cewa tazo satar naman da aka ajiye musu ne, bayan basu da masaniyar sun ajiye musu,

"Am talking to u, ki amsa mini, dama har yanzu baki daina bin abincin mutane kina satar musu ba"? Yawu ta haÉ—iya, tare da sanya hannayenta ta zame mashi hannunshi daya toshe mata baki dashi" ta juyo tana fuskantar inda yake atsaye, duhu ya hana ta ganshi dakyau,

Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"Ae zuwa nayi inga idan ya lalace, in zubda, tunda naga tun É—azu da safe aka ajiye maku amma baku ci ba" muryarshi asake yace"A cikin Cikin ki zaki zubda shi ko?" shiru tayi bata bashi amsa mishi ba,

"Maza ki wuce kije ki kwanta, tunkafin in yi wurgi dake" tana ƙunƙuni ta juya tana laluban hanya harta gano gadonta ta haye ta kwanta, zuciyarta duk ajagule, taso ace tacinye naman duka, ita uwar haɗama, kuma ba yunwa take ji ba,

Bayan tafiyar parveen, danish ya duƙa inda ta ajiye kwandon, yana ƙoƙarin ruƙe handle ɗin yaji an damƙi hannunshi, har sai da ya ɗan ji bugun zuciya, duk da bai iya gane wacece ba, amma yaji aikin shi cewa ANGEL ce, itama parveen ɗazu daya Canko sunanta, saboda yasan halinta ne, Ya farka yana Jin yunwa, ɗazu yaji haris yana cewa arage musu nasu naman shiyasa ya yi tunanin akwai saura, wannan dalilin ne yasa shi saukowa daga saman gadon shi, ya nufi gadon batool donya duba yaga idan an rage musu nasu, Yana tunkaro bakin gadon yaji motsin mutun, nan take ranshi ya bashi cewar itace, dama halinta ne,

Kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, gashi dai basu ganin juna dakyau, saboda duhun da ya mamaye idanuwansu, muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta"Angel" Muryarta a kausashe tace"Ni ce, sai me? Idan ma yankan naman nan kazo ka ɗauka sai dai ka haƙura kabar mini saboda nafi ka jin yunwa " yadda tai maganar babu sassauci, dagaske yunwa take ji sosai, kamar ta cinye ƴan hanjin Cikinta, shima kuma yunwar yake ji, cikin sanyin murya yace"me zai hana mu ci atare, sai mu raba" kamar tana ganin shi tace"A'a, kawai dai ka haƙura kabar mini, saboda ba isata zaiyi ba"

"but why ɗazu baki ci ba? Da haris ya yi maki magana"? A harzuƙe tace"Saboda bana jin yunwa a lokacin yanzu kuma ina jinta, meyasa ma ka tambayeni? bata jira yabata amsa ba, ta kuma cewa"To kai meya hana ka cin naman ɗazu"? Tayi tambayar tana jiran jin amsarshi, sai da ya ɗanyi jim before yace"saboda ke, na damu da halin da kika shiga, naji kince ba zaki ci abinci ba, shiyasa nima naƙi ci, saboda bana so ki ji yunwar ke kaɗai," sam bata ji ɗaɗin maganarshi ba, saima haushin shi data ƙara ji, muryarta ƙasa ƙasa tace"Nifa baka burgeni komai zaka Yi, ko son ganinka ma bana yi, wlh haushinka nake ji kamar in nannaushi fuskarka, ka 6ata mini rai sosai, Kana nuna ka damu dani wannan duk abanza ne, tun da baka iya nuna damuwarka akan deeja, da aka dawo da ita daren jiya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa amma kai kaja baki kayi shiru amatsayinka na babba acikin mu, har haris ma yafi ka sanin yakamata," Tana kai ƙarshen maganar, ta fusge kwandon daga hannunshi ta miƙe, cikin duhu ta nufi table dinsu ta ɗauko fitila ɗaya ta kunnata, A saman dining Carpet ta zauna, Ta ajiye kwandon agabanta, ita kuma fitilar ta ajiyeta a gefe, Zuciyarta duk ba daɗi, ita kanta bada son ranta take gaya mashi magana ba, daurewa kawai take yi,

Daga inda yake a zuƙunne bakin gadon batool yana hangenta, jikin shi yayi mugun yin sanyi, duk sai yaji ya rasa kuzarinshi, tamkar ya fashe da kuka haka yake ji, baya son angel tana yin fushi da shi, hatta faɗan da take yi mashi baya so, dan ba yadda zai da ita ne, kasa jurewa yai ya yunƙura ya miƙe ya nufi saman dining carpet ɗin, Yana ƙarasawa ya zauna tare da lanƙwashe ƙafafuwanshi Yayi zaman cin tuwo kamar yadda tayi, Ya kasance suna fuskantar juna ita dashi, Ko kallo bai ishe ta ba, bakinta acunkushe da yankar naman data tura sai tauna take yi, duk in suka haɗa ido saita jefa mashi harara, bawan Allah miyan sai tsinkewa yake yi,

yana so ya ɗauki naman yaci, sai dai ya kasa saboda gudun faɗan ta, Muryarshi arauna ce yace"pls angel, ki bari na ɗauka naci nima, koda fruit ɗinne, am serious yunwa nake ji" sai da ta kammala taunar naman dake abakinta tukunna tace"baka da ƙarfin da zaka ƙwata ne? Wai kai wani irin namiji ne? Mace kake marairaice ma fuska? duƙar da idanuwanshi ƙasa ya yi batare daya tanka mata ba, dogon tsoki taja, takai hannu ta ƙara ɗaukar yankan naman ta tura abaki tana ci, Sai da ya rage saura biyu, tace mashi"in kaga dama ka ɗauka kaci," tayi maganar tana daukar fruits din ciki tana sha" muryarshi na rawa yace"bazan ci ba, saboda me zaki dinga yi mini faɗa? Nifa haka rayuwata take, ki ƙyale ni mana, bana jin daɗin yadda kike kushe ni," Ranshi amatuƙar 6ace ya miƙe, Ya juya ya nufi gadonshi ya haye ya kwanta,

Sai bayan daya tafi, Jikinta yayi sanyi, daƙyar ta iya shan fruits ɗin, idanuwanta suka Cicciko tab kwalla, yunƙura ta yi tare da miƙewa ta ɗan ranƙwafa ta ɗauki fitilar ahannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun kuma ta ruƙe handle na kwandon, wurin gadon shi ta nufa, daga gefe ta ajiye fitilar tare da kwandon, idanuwanta na akan gefen fuskarshi, ya ƙanƙame pillow aƙirjinshi, jikin shi har wani kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki, Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan kada ta kuskura tace zata lallashe shi ta ƙyale shi wata'kil yayi hankali, gani take ma idan taci gaba da lallashin shi zai ƙara lalacewa ne, ƙwara ta koya mishi hankali, jinjina kai ta ɗanyi alamar gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata,

"Idan kaga dama ka tashi ka ɗauki naman kaci, idan kuma baka ci ba, matsalarka ce" Takarasa maganar tare da watsa hannayenta, Irin bata damu din nan ba, wuce wa tayi zawa gaban table ta ƙara ɗauko wata fitilar ta kunna ta, kaitsaye ta nufi gadon deeja, domin ta yi mata yaji ƙi, tun ɗazu da safe take ta son taje wurinta amma damuwa ta hanata, zuciyarta tayi mata nauyi a ƙirjinta, shiyasa ta tagaza tashi daga saman gadon ta yi kwanciyarta,

Daga gefen gadon deeja ta zauna, tana haska fuskarta da fitilar hannunta, da alama tayi nisa acikin baccinta, har cikin zuciyarta taji daɗin yadda deeja ta samu sauƙi, don jiyan nan zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, harta fara fidda ran da zata rayu, sai gashi Allah ya taimake su, deeja ta wartsake, a hankali ta ɗaura yatsun hannunta saman fuskar deeja ta ɗan shafata, kafin ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata,

"Bazan tashe ki daga bacci ba My lovely sis, gobe in sha Allah, idan kika farka daga bacci zanzo in yi maki ya jiki, Allah ya ƙara maki Lafiya, " janye hannunta tayi daga kan fuskar deeja ta mayar dashi saman sumar kanta, dake a hargitse duk ta yamutse babu gyara, aranta ta ayyana cewa, idan deeja ta samu lafiya sosai jikinta yae kyau zata gyara mata gashin kanta, ta kuma yi mata kalaba, kalar tasu azeeza, sauƙin ma ita gashin nata bai kai nasu tsayi da yawa ba, ya dai sauko har saman kafaɗarta, baƙi wulik, kamar na ɗiyar roba, Ta jima zaune tana kallon deeja, daga bisani ta miƙe hannunta ruƙe da fitilar tabi gadon kowannan su ta tottofesu da addu'o'i, lokacin da ta dawo zata wuce gadonta, Sai da ta saci kallon shimfiɗar danish, Still bai ɗauki naman shi yaci ba, duk sai taji ba daɗi, Duk yinin yau baici komai ba, ko ruwa bata tunanin yasha mutun sai kace aljani, anya kuwa zata biye mashi, kodai taje ta lallashe shi ya tashi yaci?

A ƙasan gadonta ta ajiye fitilar hannunta, wurin ya ɗanyi haske hada ƙarin ɗayar fitilar dake a kusa da gadon danish,

daga Gefen gadonta ta zauna tana kallon bayanshi, still babu alamun yayi bacci, yatsun ƙafarshi basu daina yin kerma ba, Zuciyar imani ce ta zo mata, ta miƙe taku ɗaya biyu, ta zuƙunna abankin gadon shi, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanshi"Danish" shiru bai amsa mata ba,

"Fushi kake yi da ni, saboda kawai na faÉ—i gaskiya," ta É—anyi maganar tana hararar bayanshi,

"Its ok komai ya wuce, bazan ƙara ba, pls ka tashi ka ci naman nan kasha fruit din idan ma baka Iya Ci da hannunka sai in baka abaki, ba wani abu bane, ni kawai bana so ne ka kwana da yunwa, dama ka faɗa mini cewa saboda ni ne baka Ci abinci ba, To yanzu ni naci kaima saika tashi kaci, ko ba haka ba My man"? Bakinta ƙumshe da dariya tayi maganar, babu alamun zai tanka mata,
Chapter 94 · 0% Book details