Sashe 171
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunanta suka dinga kira shiru bata amsa masu ba, Atare suka haɗa ƙarfi wurin bugun ƙofar sai dai ga dukkan alamu An garƙame ta da Jamlock, Tamkar zasu fashe da kuka suka dingayi mata magiya akan tayi masu koda tari ne don su san cewa tana acikin toilet ɗin, saboda su samu hankalinsu ya kwanta amma shiru Angel bata tanka masu ba, kamar zasu 6alle ƙofar saboda Yadda su ke kai mata zazzafan naushi da hannayensu, a ƙarshe da suka Gaji agalabaice suka zuzzuƙunna Haɗi da jingina bayansu Jikin bango, jin motsin shigowar mutun cikin sashen Yasa suka kai idonsu ga mai shigowa,
Jamimah ce ta shigo hannunta ruƙe da kwando ta ajiye masu shi a tsakiyarsu, Bakinta a cunkushe ya ke da kingin ganyen da bata ƙarasa taunewa ba ahaka ta ke yi masu magana,
"Ku ci naku ne na kawo maku" kallonta kawai su ke yi, Ta zumbula bargo ajikinta sai ja da ƙasa Yake yi, jin sunyi shiru basu tanka mata ba, yasa ta haɗe girar ta"Ni ba ruwana Idan ba ku ci ba, Ku yunwa zata kama, Sannan Ina GENIE ɗina ta ke? Ko haryanzu bata fito daga wankan bane?
.................... WHERE'S ANGELâ—â“
💋PRISONERS💋
"Ita mu ke jira ta fito daga wanka, Ki koma É—aki ki kwanta, Yanzu zamu shigo Ciki" Hibba ce ta bata amsar tambayar ta, juyawa jamimah ta yi zuwa cikin É—akin su ta koma saman gado ta haye tare da kwantawa.
"yanzu haka zamu zauna muna ta jiranta? Shiru duk irin bugun ƙofar da mu ka yi babu alamun zata buɗe mana, Anya kuwa lafiya? Ni tsoro na kada ace wani abun ne ya same ta," a cewar Deeja, hankalin su duk ba a kwance ya ke ba.
"In sha Allah ma ba abun da ya same ta, Zai iya yiwuwa bacci ne ya ɗauke ta a cikin toilet ɗin ko kuma zurfin tunani ta shiga....." tunkan Batul ta rufe baki Sarah tace "wani irin bacci ne wannan mai nauyin gaske da har za'a dinga bugun ƙofa mutun bai farka ba? In kuma zurfin tunani ta shiga ai yaci ace bugun da muke ya dawo da ita hayyacin ta, Gaskiya bana tunanin haka sai dai wani abun ne na daban," kowa na tofa albarkacin bakinsa,
"Yunwa nake ji, ƙwara ku zo mu haɗu Mu ci ganyen nan idan mu ka kammala sai mu ƙara jaraba Bugun ƙofar" A cewar Parveen, Atare su ka matso kusa da kwandon, Kamar akuyoyi haka suka dinga kwaso Ganyen Suna Cunkusa shi Cikin bakunan su, a tsiyace su ke taunar shi, Zuciyoyin su duk ba daɗi, damuwar rashin Angel ta hana su sakat.
Suna tsaka da Cin Ganyen kunnuwan su suka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙofar ɗakin su, A firgice su ka ɗago Suna kallon Junan su! Zuciyar su cike da fargabar Motsin buɗe ƙofan da su ke Ji, Tun da sun riga sun san An kawo masu Abinci, shiru su ka yi an rasa mai ƙwaƙƙwaran motsi A cikin su, hatta ganyen da suka cusa a Cikin bakunan su sun dakata da taunar su, babban abunda suke jima fargaba kada ace Tsohuwa Zafreen ce ta kawo masu ziyara, Tuni kowannan su Yasha Jinin Jikin shi.
Garam! Su ka ji an datse ƙofar alamar wanda Ya shigo Ya fita, nauyayyiyar Ajiyar zuciya kowaccen su ta sauke, Kafin wani yai yunƙurin motsa La66ansa Muryar Jamimah ta karaɗe kunnuwan su.
Wata irin razananniyar ƙara ta fasa Mai kuwar gaske, Hankulan su A tashe su ka mimmiƙe da gudun gaske suka faɗo Cikin ɗakin a sukwane Suka ci uban burki Suna faman Haki, A tsakiyar ɗakin su ka ganta Ɗaure da bargo a jikinta Sai tsalle ta ke yi, babu wanda Ya lura da me ta ke Yima Murna, Rai a6ace Parveen tace"Wannan wani irin rashin Hankali ne jamimah? Salon kawai ki kara tada mana hankulan mu shine kika fasa Ihu kamar mai ta6in Hankali"? Jin muryar Parveen Yasa ta juyo tana kallon su fuskarta ɗauke da murmushin Farin Ciki,.
"An dawo mana dasu Ƴan uwan mu dole in yi farin Ciki....." Tun kan ta ƙarasa maganar Kusan atare Suka kai idanuwan su akan benan Ɗakin su! Wani irin bugu zuciyoyin su suka yi atare, Abu ne da basu Yi tsammanin shi ba, Tamkar A mafarki Haka suke ganin su, sun kasa Yarda da abunda idanuwan su suke nuna masu!
A tsaye su ke cirko cirko saman Matakalar benan, su biyar babu Danish Daga ganin su babu ƙoshin Lafiya atattare dasu, Fatar Jikin su Ta yi haske Hatta Haris da ya ke da duhu fatar shi ta canza, Sun rame sun bushe kamar babu Jini a jikin su, ƙafafuwan su kansu ba adai dai su ke ba, musamman ƙafar Mubeen da ta javed rawa su ke Yi kamar zasu kasa, Sumar kansu Kuwa Duk a hargitse Dama Allah yayi su da tarin sumar kai, Ba kamar Javed Da Gabriel sai Naufal, yanayin yadda suka yi tsayuwar Ya nuna sam babu kuzari a jikin su Kamar waɗanda Aka ɗebi Naman Jikin su, Sun faɗa sun zabge........"
Muryar Deeja Na rawa ta furta sunan HARIS! Mamaki ne ƙarara akan Fuskokin su, Lamarin Ya yi matuƙar ɗaure Masu Kai, Cikin karyayyiyar Murya Parveen Ta furta Sunan NAUFAL! Hannun Batul dafe da saitin Zuciyar ta ta furta Sunan JAVED!! Muryar Hannah A disashe ta ambaci Sunan MUBEEN! Cikin shessheƙar Kuka Azeeza Ta ambaci Sunan GABRIEL! kamar a mafarki haka suke ganin su, Jikin su ba ƙaramin sanyi yayi ba, zuciyoyin su sun karaya sosai, Ganin yadda ƴan uwan nasu Suka Ƙi motsawa, Bakomai ya ɗaga masu hankali ba face Ganin Yadda Haris daya fi su ƙiba Ya koma Ramamme uwa su Javed, Sun fita hayyacinsu, Daga ganin idanuwan su ba ƙaramar izaya suka sha ba, Allah kaɗai yasan Azabtarwar da su ka yi masu na tsawon watannin da su ka yi a hannun su.
Tuni idanuwansu Deeja sun Cicciko tab da ƙwalla, Parveen tana kuka tace"Wlh kamar basu ba! Kamar an canza mana ƴan uwanmu! Ku kalli yadda suka rame ko magana ma basu Iya yi, Ni ina tsoron kada ace irin na unaiza su ka yi masu........" daƙyar ta ƙarasa maganar saboda kukan daya ciyota, Cikin rauni na murya Deeja Tace"Haris kaine ka koma haka? Ina Jikin ka ya ke? Javed Mubeen Naufal baku Iya magana? Meyasa ku ke kallon mu kamar Ba ku gane mu ba"?
"Ba kallon su Ya kamata mu tsaya muna yi ba, Yakamata muje gare su, wata'ƙil Sun kasa yin tafiyar ne" A hankali su ke tafiya suna tunkarar su kamar sunga abun tsoro, Koda su ka ƙaraso gaban benen Atare suka dakata da yin tafiyar suna kallon su, Gwanin ban tausayi farar fatar wuyan su harda jajayen ta66una na yakushi, Wurin yayi jawur La66an su duk sun faffashe sun bushe, Gabriel hada busasshen jini saman Ƙaramin lower lip ɗinsa daya ciza launin shi pink, Fatar idanuwan su sun yi ja alamar sun yi kukan mutuwa Sakamakon wata azabtarwar da aka yi masu.
Fashewa su ka yi da kuka tamkar ransu zai fita Yayin da su ke cigaba da bin Æ´an uwan nasu da kallo mai nuni da tsantsar Tausayin su da su ke ji.
Azeeza Ce tai Ƙoƙarin matsawa ta haura saman matakalar farko har takai ga inda Gabriel Ya ke atsaye, Faɗawa ta yi saman jikin shi tana cigaba da yin kuka, Ganin ta ta6a shi bai nuna yaji zafi ba yasa Deeja matsawa Ta rungume Haris a jikinta, Da sauri batul ta hau benan ta Ruƙo Javed ta kwantar da kanshi saman kafaɗarta, Parveen ta nufi Naufal ta janyoshi ta rungume shi sosai tana cigaba da yin kuka, Hanna ce ta ruƙo Mubeen ta haɗa shi da jikin ta, Yadda suka ƙanƙame su A jikin su suna yin kuka tamkar ran su zai fita, Sun yi kewar ƴan uwan su sosai.
Matsawa saman benen Yasmin da su rubina su ka yi, A bayan su Batul dake rungume da ƴan uwansu maza suka ɗaura kawunan su, Gaba ɗaya sautin shessheƙar kukan su ce ta karaɗe Ɗakin nasu, Jamimah da sarah ne kaɗai su ka rage a tsaye bakin benan suna kallon su Idanuwan su cike tab da ƙwalla.
Batul da ke ruƙe da javed taji Jikin shi ya saki gaba ɗaya ya tafi zai sulale ƙasa da sauri ta daddafe shi a haka suka Zauna saman Matakalar benen, ta tallabo fuskar shi da Hannayenta biyu "Javed! Pls ka yi mini magana Inaso insan a wani hali ku ke ciki" Daƙyar ya ke iya kallon fuskar ta, saboda raunin da idanuwan shi su ka yi mashi kamar zasu lumshe, hatta numfashin su da hucin zafi Ya ke fita.
"Haris Ɗina ne ya koma haka? Inna lillahi Wa'inna ilaihirraji'un! Wlh ba zamu ta6a yafe masu ba, Allah ya isa tsakanin mu dasu Mugaye Azzalumai, Duk sun canza masu Halittarsu, ko magana ma ba su iya yi" cikin jin Ƙunar rai Deeja ta yi maganar, har lokacin bata janye haris daga jikinta ba, Kamar zata maida shi Cikinta,
"Dan Allah Naufal ka buɗe baki Ka yi magana, Hankalin mu ba a kwance ya ke ba, Muna so Muji koda muryoyin ku don mu tabbatar da cewa kuna da Lafiya" parveen ce ta yi maganar, fuskar ta sharkaf da hawaye yayin da ta ɗago da kan Naufal daga saman kafaɗar ta, Bawan Allah sai bin su da ido Ya ke yi, fuskar shi Ta yi jawur saboda hasken da ke gare shi, Dama duk Cikin mazan In ka cire Danish a wurin haske sai Naufal mutun na gaba Javed ne Duk da shi ba fari bane sosai amma Baya a cikin jerin baƙaƙe Launin fatar shi Chocolate ce, Yana da tarin sumar kai, iya kafaɗar shi ta tsaya, Bayan shi sai Gabriel Kalar fatar su Kusan ɗaya Da Javed babu bambanci, Kamar za suyi hauka wurin yi masu magiya akan su yi masu magana ko sun ji sanyi acikin ran su, Gaba ɗaya sun manta da zancen Angel tun da su ka yi tozali da Ƴan uwan nasu.