← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 179

Sashe 65

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata bata amsa ba, sai da tafara zagayo da hannayenta saman bayan azeeza tukunna tace"Ae ni banci appales ɗina ba, Ni da danish, Ku da kuka Ci ku kayi bacci, gaya nan yanzu kun wartsake," ɗagowa azeeza tayi daga kan Jikin angel tace"Amma ae lokaci bai motsa ba, har yanzu fa safiya ne, yau zamu yini muna jin yunwa" aɗan shagwa6e tayi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba angel ba,

"Sister"! Batool ce ta ambaci sunanta, tana atsaye kusa dasu, ruƙo hannunta Angel tayi acikin nata tace"My other half, nayi missing dinki, ina fata kin tashi lafiya, an sha bacci" lumshe ido batool tayi fuskarta a yamutse tace"am not feeling well, sai nake ji kamar wani abu ya faru da muna bacci, na shiga ruɗu," janyota angel tayi zuwa jikinta, ta rungume ta, batool ta kwantar da kanta saman kafaɗar angel, hannu tasa tana shafa bayanta tace"Ki kwantar da hankalin ki, ba abunda ya faru, bacci kawai kuka sha," ajiyar zuciya batool ta sauke tare da raba jikinta daga na angel, still idonsu acikin na juna

"Yakamata Ku je ku yi wanka, bazan 6oye maku ba, tsami ku ke yi, daurewa kawai nake Yi ina yin magana daku" cikin zolaya tayi maganar, gani tayi suna shinshina Jikinsu, harara batool ta jefa mata"Sister kinyi wanka shine baki tada mu daga bacci ba, Munyi wanka mu ma,"? Fuskarta akwa6e tayi maganar,

"Ae ni bana tada mutun idan yana bacci, yanzu tun da kun farka, sai kuje ku yi,"

Juyawa batool tayi tare da kallonsu Hibba dake zaune saman gadajensu, Ko motsawa basuyi ba,

"Ku tashi muje mu yi wanka," saukowa Kowannan su yayi daga saman gadon shi,

"Jiya nida danish mun wanke hada uniform É—inmu," su6uce mata maganar tayi

Cike da mamaki batool tace"Jiya kuma"? Da sauri angel tace"Ina nufin ɗazu da safe, lokacin da kuna bacci, ae na fada maki ni da shi bamu Ci namu apples dinba," takai ƙarshen maganar tana ƴan kame kame, Batool kamar bata yarda da maganarta ba, gyaɗa kai kawai ta yi tare da wuce ta nufi toilet,

Batool ce tabasu shawarar suma su wanke nasu Uniform ɗin, Sai da kowa ya cire uniform ɗinshi, Suka yi ɗaurin gaba da Bargunansu, Hada maxan su, tattara Uniform ɗin Batool tayi ita da Angel da Hanna, Suka shiga toilet sec ɗinsu, Anan Suka tara kayan wankin, Azeeza da javed ne suka ɗebo ruwa a buckets, rubina ta ɗauko masu detergent, Su Uku Suke wankin kayan suna yi suna fira, Sauran ƴan uwan nasu ba wanda ya taya su dama su suka sanya kansu zasu wanke masu kayan, don sunce su baza su yi wanki ba kada ƙarfinsu ya qare, Gashi yau babu abinci, angel dai jinsu kawai take yi, ta ƙosa taga reactions ɗinsu idan su giants suka zo kawo masu abinci, zasu sha ruwan mamakin sanin cewa Sunyi baccin kwana ɗaya,

Angel ta dage sai Cuɗa kayan take yi, Koda tazo kan Uniform ɗin haris saita yatsina fuska, Ta ɗago su tana shinshina su, A karshe ta wurga ma batool saman fuskarta tace"ki wanke su, Ni bazan wanke ma ƙato kaya ba"

Dariya su kayi gaba ɗayansu, azeeza tace"Amma kuma kike wanke ma Mubeen dasu javed? Su ba ƙattan bane"? Girgiza kai angel tayi a yayin da take matse rigar data kammala Cuɗawa, tace"Idan kika lura Haris duk yafi su girman Jiki, shifa tuttu6e6ene ga Tumbi, Kuma mummuna......" bata ƙarasa maganar ba, karaf idanuwanta suka sauka akan haris dake atsaye bakin ƙofar toilet ɗinsu, Fitowarshi kenan daga wanka, ya ruƙe qugu jikinshi na sanye da bargon daya lullu6a, fuskarnan babu walwala attare da ita, harara angel ta watsa mashi, ita fa idan ta ɗauko magana ba wanda ya isa ya hana ta ƙarasawa, don haka taci gaba da cewa"sam baida kyau, Hancinshi gajere ne, gashi baƙi, idanuwanshi mitsi mitsi," tayi maganar tana murguɗa mashi baki,

Tayi tunanin haris zai tanka mata, amma sai taga ya girgiza kai kawai, Ya wuce cikin É—akinsu,

Batool tace"Na lura angel baki son haris, bansan meyasa ba," takai karshen maganar tana kallonta,

"batool, he hates me for no reason, that's why I don't like him" takai ƙarshen maganar, a yayin da take kai hannu ta ɗauki Bucket ɗinta, da niyar taje cikin toilet ta zumar da ruwan kumfar ta ɗebo wani ruwan da zasuyi ɗauraya da shi,

A bakin fanfo, ta tsaya ta tura bokitin ta kunna tap din ruwa ya shiga kwararowa, zuƙunnawa tayi tana jiran bokitin ya cika,

Bakomai ya faÉ—o mata arai ba, face Lokacin da Tana agida Tare da daddynta, Ita ko hanyar laundry bata sani ba, daddynta da kanshi yake zuwa ya wanke mata uniform É—inta na makaranta, Yayi goge mata su, duk wannan wahalar bata san da ita ba, shi ne yi mata wanka ya zura mata kayan ajikinta, Allah sarki rayuwa kenan,

Ganin ruwan ya Cika bokitin, yasa takai hannu ta kashe fanfon, ta miƙe ta ruƙo handle ɗin bokitin ta fuce dashi, a lokacin har su Batool sun kammala Yin nasu sa6in, saura ɗauraya, atare suka dinga ɗauraye kayan, Azeeza ce take zuwa ta shanya su asaman igiyar dake a cikin toilet ɗinsu,

Suna dab da zasu kammala, Sai ga Yasmin ta faÉ—o Cikin toilet sec din Fuskarta aÉ—auke da murmushi sai faman washe baki take yi

"Lafiyarki kuwa kike ta faman zabga murmushi"? Batool ce tayi mata tambayar,

Daƙyar ta samu natsuwar cewa"Giants ne suka zo kawo mana abinci, "

Da mamaki akan fuskar batool tace"are u serious? Jinjina kai Yasmin tayi"Ku dai kuzo muje mu ci abinci," azeeza tace"amma nayi mamaki, yau ba rabon mu kwana da yunwa," angel dai sai murmushi take saki tana kallonsu, ganin har yanzu basu gane cewa wata ranar bace ta zagayo,

"Bari mu mayar da buckets din Gamu nan zuwa, Allah yasa dai ba wasa kike yi mana ba," acewar azeeza,

Yasmin tace"Am serious ku dai kuyi sauri kuzo, " ta juya cike da zumuÉ—i ta fuce,"

Da sauri suka ƙarasa shanyar kayan nasu, hannayensu a ruƙe dana Juna suka Faɗo Cikin ɗakin, A tsaye suka samu Giants Sun ƙame, Ga kayan abinci nan saman dining carpet ɗinsu, A shaƙe, Su Mubeen duk suna a zazaune Kowa Ya natsu Jikinsu sai kerma yake Yi saboda tsabar yunwar da suke Ji,

Ƙarasa shiga Cikin Ɗakin su ka yi, a gefen ƴan uwansu suka zauna a jere, Batool, azeeza da angel,

Parveen ce ta yaye masu jan ƙyallen tray na farko, waro ido tayi tare da wage baki ganin Tsiren nama A shaƙe Da tray din, saboda yawanshi har suci su rage da anjima su ci, Wani irin maiƙo tsiren ke yi, yaji kayan ƙamshi hada su albasa da tumatur, batare da 6ata Lokaci ba, kowa ya zura hannu yana ɗaukar tsiren naman yana Ci, yadda kasa akuyoyi haka suke taunarshi, mutun ɗaya ne yake Ci atsanake tamkar baison ci, sam baison Cin abinci, karasa uban me yake ci ya ƙoshi, ranshi ne ya bashi cewar ana kallonshi, slowly ya ɗago da idonshi, da sauri angel ta duƙar da nata idon don kada ya gane shi take kallo,

"Kinsa min ido sosai," ya ambaci hakan acikin zuciyarshi,

"Saboda ban yarda dakai ba, kai ɗin abin tuhuma ne, dole na sanya maka ido, duk wani motsinka akan idona," acikin zuciyarta tayi maganar, tamkar ta bashi amsar maganarshi alhalin kuwa batasan me yake saƙawa aranshi ba,

"Bansan meyasa kike tuhumata ba, laifin me nayi maki ne? Yayi tambayar acikin zuciyarshi,

Itama tabashi amsa acikin zuciyarta"baka yi mun laifin komai ba, sai dai Ina zarginka, taya akai jiya ka faɗo mini cikin toilet? Bayan na datse ƙopa ta ciki? Taya akai ka shigo? .........." bata kai ƙarshen zancen zucin nata ba, muryar rubina ta katse mata hanzarinta,

"Kuna ta Cin nama kun manta da shan ruwa"

Tayi maganar tana kallon kowannan su, dakatawa su kayi da Cin naman, Hibba tace bari ta zuba masu ruwan, Bottle water ta ɗauka me sanyi, Ta tsirara masu ruwan acikin Wooden cups ɗin dake a jere, Kowa Ya mika hannu ya ɗauka yana sha, Saboda tsabar kallon angel da yake yi har sai da ya shaƙe ya hau yin tari, da sauri haris ya ɗaura hannunshi akan bayan danish yana ɗan bubbugawa, sai da ya daina yin tarin tukunna ya zame hannunshi,

Dariyar gefen fuska angel tayi saboda ta gane itace silar daya shaƙe, Ta san ya tsargune da irin kallom da tayi mashi ɗazu, abunda ke faruwa su duka biyun basu yarda da Junansu ba, Shi yana kokwanton canzawarta, ita kuma tana zarginshi da ba cikakken mutun bane, tun Daren jiya daya faɗo mata toilet batare da ya kwankwasa ta cire jam lock ya shigo ciki ba, ta ina ya shigo? Shine abunda ya sanya mata ruɗi agame da shi,

Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran da suka rage, Hada kayan marmarin da aka kawo masu da kuma snacks, Batool ta tattarasu ta kwashe acikin kwandonta, takai karkashin gadonta ta 6oye masu,

Tattara Kayan abincin giants su kayi, Javed Ya ɗauko masu Na shekaran Jiya da suka kawo ma danish Ya miƙa masu suka kar6a, kafin suka fuce daga Cikin ɗakin,

Lokacin da Uniform É—insu suka bushe Kowa Ya É—auko Ya sanya kayanshi ajikin shi,

Saboda tsabar Jin daÉ—in da su ka yi, Hanna ta basu shawarar suyi wasa,

Gaba É—ayansu suka taru, a tsakiyar É—akin nasu, raba kansu su kayi gida Biyu, mutun bakwai bakwai, sai mutun É—aya ya rage, itace me gabatar da wasan, wato hanna, bayani ta soma Yi masu akan yadda zasu gudanar da wasan,

"Duk wanda na canko acikin ku, zan rufe ma shi ido da tafin hannaye na, in matse su, zan ba shi sunan wanda zai gano mana, idan har ya kuskura bai canka dai da ba, da shi da wanda ya canko, kowa zaiyi masu dundu É—aya abayansu, kun amince" HaÉ—a baki su kayi wurin cewa Eh mun amince,"

Duk wannan abun da suke Yi tsohuwa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta tana kallonsu, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta ɗauke da wadataccen murmushi,
Chapter 65 · 0% Book details