← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 179

Sashe 39

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harara danish ya jefa mata, dama haushin ta yake ji, bai dai ce komai ba haris ne yace"yanzu kina so mu yadda dake mubar 6angaren tsohuwa? Wai ke da me kike taƙama ne? idan bakisan wacece tsohuwa ba, bari in ƙara tunasar dake, itace ta raine mu ta kuma gatanta mu, bamu da tamkarta a duniyar nan,'

Cike da takaici angel tace"dukkan ku baku da tunani, bakusan ciwon kan ku ba, Ni bansan taya zan fahimtar daku ba, gidan kurkukun nan ba alkhairi bane, gatan da kuke faÉ—in tsohuwa ta baku, ba gata bane gata shine abar mutun ya yi rayuwar Æ´anci, amma ku an killace ku, an hana ku ganin hasken rana, acikin kurkukun ma an yi maku iyaka da shiga ko'ina, a rana sau É—aya kuke samun abinci, an haÉ—a maza da mata É—aki É—aya suna kwana shin wannan gata ne? Kullin mu ne yawo cikin uniform kala É—aya, wai ku baku gajiya da rayuwa a kulle ne? Kuyi tunani mana babu alkhairi atattare da kurkukun nan"

Murmushi Batool ta ɗan saki, kafin tace"angel, dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa indai akan tsohuwa za ki yi magana babu wanda zai ta6a fahimtar ki, its better ki yi shiru da bakin ki, yadda kika ganmu kibar mu kawai mu haka ƙaddarar tamu rayuwar take a cikin kurkuku"

Shiru angel ta ɗanyi, sai lokacin ta ƙara tabbatarwa kanta cewa An gama dasu tabbas ba hakanan tsohuwa ta ƙyale su ba, batasan wata irin huɗu ba ta yi masu ba, da har suka gaza fahimtar dai dai, taso ace sun yarda da maganarta ta hakan ne zasu haɗa hannu wurin nema ma kansu mafita, sai dai kash sunƙi bata haɗin kai,

"Ina son fita daga cikin kurkukun nan, amma bansan meyasa ba, bana jin zan iya rayuwa awajensa, a duk lokacin da nayi tunanin fita daga cikinsa sai inji ƙunci da raɗadi suna taso mun acikin zuciyata" javed ne ya yi maganar,

"Nikaina ina sha'awar wata rana in ganni awajen kurkukun nan, but i don't know why bana jin zan iya fita daga cikinsa koda na samu damar yin hakan"

Kasa kunne angel ta yi tana sauraron su kowa yana tofa albarkacin bakinsa, banda Danish, da ya lumshe idanuwan shi tamkar mai yin bacci,

"Tsohuwa ba gaskiya take faÉ—a maku ba, nasan zaiyi wuya ku fahimce ni, amma kuyi tunani mana, Kowani É—an adam Da Allah ya halitta A duniyar nan, ba daga sama ya faÉ—o ba, shin kun ta6a tunanin Ina iyayen ku su ke? Meyasa kuka kasance marayu? Idan iyayen ku sun rasu ina danginku su ke? Idan na baku labarin rayuwata ina da tabbacin zaku fara kwaÉ—ayin yin rayuwa a wajen kurkukun nan, kuma zakuyi tunanin Ina iyayen ku da dangin ku su ke......." muryar Deeja ce ta katse mata xancen nata da cewa,

"Kince kowani É—an adam da Allah ya halitta? Waye É—an adam É—in kuma wanene Allahn da kike magana akai"

Mamaki ƙarara akan fuskar angel ta ɗago tana kallon deeja dake zaune can saman gadonta, fuskarta babu alamun wasa ta yi tambayar,

Speechless sam ta kashe mata baki, tsabar mamakin tambayar da Deeja ta yi mata, har wani shock taji, sai lokacin ma ta tuna dasu wa take magana, ta jima tana mamakin wannan ikon Allahn, Gaskiya yaran nan an cuci rayuwar su, basu san komai ba game da wanda ya halicce su, wato su kawai rayuwa suke yi kara zube,

"Kinyi shiru baki ce komai ba"? Deeja ce ta yi maganar, jin tayi shiru bata ce komai ba, buɗe baki angel ta yi da niyar ta bata amsar tambayarta, ba zato ba tsammani taji an daki kokwan kanta, wani irin duhu cikin idanuwanta, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta dake yi mata raɗaɗi muryarta na kerma ta shiga ambaton"LA'ILA HA'ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!" gaba ɗaya suka tsareta da ido ganin ta runtse idanuwanta, Jikinta na kerma, da sauri batool da su hanna suka sauko daga saman gadajensu suke nufi gadon angel, Suna tambayarta lafiya meya faru, bata basu amsa ba, jiki ba ƙwari ta sulale saman mattress ɗinta ta kwanta,
Kallon juna su ka yi cike da tsantsar mamaki,
Hanna tace"Anya kuwa lafiya? Kodai bata jin daɗin jikin ta ne" miƙa hannu batool ta yi saman wuyan angel ta shafa shi, Sanyi taji sosai " kallon su tayi"lafiyarta qalou, bacci ta ke yi,"
Sautin dariyar Haris suka ji, a tare suka juya suna kallon shi, hannun shi rungume da pillow,
"Dama karta farka, kowa ya huta"
Hararar shi batool ta yi, tare da kawar dakanta, Cigaba da magana Haris ya yi"Saboda ita duk kun ta shi hankalin ku, yarinyar nan fa ba son mu take yi ba, saboda bata son tsohuwa....." kafin yakai ƙarshen maganar shi, Danish yace"haris, pls stop talking about her,' shiru haris ya yi saboda Danish ya nuna baya son yana maganarta,
A gefen gadon angel su batool suka zazzauna suna jiran ta farka, hankalansu sam bai kwanta da irin baccin da angel ta yi ba, shiyasa suka gaza komawa saman beds É—insu,
Lamarin ya É—aure masu kai, tsawon awanni tana bacci, Tun suna sanya ran zata farka har suka fara fidda rai,
"Kodai inje in faɗa ma Tsohuwa ne? Acewar Hibba, Batool tace"Mu ɗan ƙara jira mu gani, wata'ƙil kafin dare ta farka,' Azeeza duk tafi shiga yanayi saboda ita tausayi gareta ga tsoro, muryata a sanyaye tace"Ni bana so wani abu ya samu angel, saboda ina sonta,'

Haris dake sauraron su, kamar ya miƙe yaje ya rufe su da bugu haka yake ji, don shi ya tsani ya ji suna damuwa da ita,

Saukowa javed yai daga saman gadon shi, hannyen shi Cikin Aljihun wandonshi ya nufi gadon angel, inda suke a zazzaune, a tsaye ya tsaya yana kallon su"ku kwantar da hankalin ku, zata farka ne, zaman ku anan yana ƙara takura mata"
"To kai meye ruwanka da ita'? Haris ne yai maganar, Kallon shi javed yai tare da cewa"Cos she's my sis, i must worry about her, " yakai ƙarshen maganar shi, tare da janye idon shi daga kan haris Ya mayar da shi kan su batool da har yanzu basu matsa daga saman gadonta ba,
Dogon tsoki Haris Yaja rai aɗan 6ace yace"daga zuwanta har ta fara canza maku tunanin ku," Mubeen yace"Ka fa iya bakin ka, halan ka manta bugun da muka sha a hannunta ɗazu da safe, kodan kaga tana bacci ne"? Cike da zolaya yakai ƙarshen maganar yana dariya, Janyo pillow haris Yayi tare wurga ma mubeen saman fuskar shi, Cafke pillown mubeen ya yi a hannun shi still da dariya akan fuskar shi yace"Yarinyar fa akwai ƙarfi, Na lura gaba ɗaya tsoranta ku ke ji, duk masu nuna basu sonta sunfi kowa jin shakkarta,' wannan maganar da mubeen ya yi ce tasa Danish satar kallon shi ta wutsiyar idonshi, yadda mubeen ya yi maganar kamar ya karanci abunda ke a cikin zuciyoyonsu, shifa a halin yanzu bai ƙi angel taƙi farkawa ba, saboda ko motsi ta yi sai yaji gaban shi ya faɗi, Ya tsani mutun mai tsiwa ita kuma taci ka kwakwazo, ɗazu a cikin toilet ɗinnan da ta rufe shi da faɗa har zazza6i ya ji a jikin shi, dauriya kawai ya yi wurin mayar mata da martani, don baiso ta gane yana jin shakkarta,
"Zan koya mata hankali ne, ai ba ƙyale ta nayi ba," haris ne yayi maganar fuska a ɗaure,
Javed yace"Zaka koya mata hankali ko zata koya maka hankali? Nakasa fahimta,' shiru haris yae bai tanka ma shi ba,
"Yarinyar nan fa duk cikin mu babu tsaranta, saboda ƙarama ce, amma sai shegen wayau ga ƙarfi, Ni har tsoro take bani in tana magana, ƙwayar idonta ma tsoro take bani, Ita sam bata jin shakkar kowa" Deeja ce ta yi maganar,

Naufal yace"Ni kuma ba ƙaramin burgeni take yi ba, yanayin rayuwarta ya banbanta da namu, tana da ƙwarin gwiwa sosai, babu tsoro acikin lamuranta,"

Naufal nakai ƙarshen maganar shi, Batool tace"Ni ina ji araina zuwanta cikin rayuwar mu, tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, idan har zamu zauna da ita cikin lalama zata koya mana abubuwa da dama waɗanda bamu sani ba, saboda ita ta yi rayuwa A wajen kurkukun nan, muna buƙatar neman ƙarin haske dangane da rayuwar mutanan dake a wajensa"
Jinjina kai eve ta yi tare da cewa"Kalamanta na É—azu sun tsaya mun araina, har na fara tunanin Ina iyayen mu su ke waÉ—anda suka haife mu? Ina dangin mu? Nafara doubting akan wani abu, Amma kafin nan, inaso angel ta farka ta bamu labarin rayuwarta, Inaso inji, kuma inaso ta faÉ—a mana wanene Ya halicci kowa, kuma wanene É—an adam da ta take magana akai,"

Maganganun da su ke yi ba ƙaramin ƙona ma haris rai su ke yi ba, ganin Yarinyar ta fara cin galaba akansu, taya wata can baƙuwa zata shigo cikinsu, ta soma kokarin canza masu tunanin su'
A harzuƙe ya daka masu tsawa, har saida Danish ya firgita, don baisan Tsawa ko kaɗan, Jikin shi har kerma yake yi, idon shi akan Haris dake ta faman huci,
Nuna su ya yi da yatsan hannun shi "kada wanda ya kuskura ya ƙara magana makamanciyar wannan acikin ku, ban ta6a sanin baku da hankali ba, sai yau, taya zaku fara ɗaukar maganganun ƙaryar da take faɗa maku? Yarinyar na fa bata da cikakken hankali, batasan me take yi ba......" muryar shi a disashe yakai ƙarshen maganar idon shi akan danish daya daddafe kanshi da hannayenshi biyu, jikinshi nata kerma

Gaba É—aya hankalinsu Ya koma akan Danish, Sun san lalurar shi ta rashin son hayaniya, idan abun ya motsa kusan burkice masu yake yi,
Chapter 39 · 0% Book details