Sashe 147
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Angel kuwa bayan tagama Wanke fuskarta da jikin jikinta, Jiri ne ya ɗebe ta, ta sulale ƙasa babu numfashi, kafin wani lokaci ɗakin nasu yai tsit, baka jin sautin hayaniyar komai, Ko'ina ka kalla a cikin ɗakin, Jinin su ne, ita kanta Deeja da ta rage idonta biyu, A gefen Angel ta kwanta idonta arufe, busassun hawaye ta ko'ina akan fuskarta, kukan zuciya take yi mai raɗaɗin haske, batasan ya za ta yi ba, ita kaɗai ta rage taya zata iya ceton rayuwar ƴan uwansu? Ita kanta ba ƙoshin lafiya gare ta ba, don ba ƙaramin dakuwa kanta yai ba, lokacin da Angel ta bugata ga ƙasa har ta sume, Allah ne ya farfaɗo da ita harta tashi.
Cikin zuciyarta ta soma magana
_Ya Allah bamu da kowa face kai da ka halicce mu, Angel itace silar da muka san komai agame da mahaliccin mu, ta faɗa mana cewa kana ƙaunarmu kamar yadda ka ke son sauran bayin ka, kana ganin mu kuma kafi kowa sanin halin da muke aciki, mun yi imani da kai, duk da bamu da wadataccen ilmi akan ka, Ya Allah ta tausaya mana kaji ƙan mu, ka kawo mana ƙarshen wahalar nan, rayuwar mu a ƙuntace ta ke, bamu ta6a cutar da wani ba amma mu ana azabtar da rayuwar mu, babu mai taimakon mu, babu wanda yasan da zaman mu balle a kawo mana ɗauki, muna ji muna gani ana neman halaka mu saboda rayuwar mu bata da amfani awurin su, Bafa sune silar zuwan mu duniya ba! Mu ba bayin su bane, bayin ka ne Ya Allah! Baka halicce mu don a azabtar da rayuwarmu ba face don mu bauta maka, amma meyasa waɗannan mutanan suke ƙoƙarin mayar damu dabbobin su, Ya Allah idan har dagaske kai maji roƙon bayin ka ne, Ya Allah kajiƙanmu kaji koken mu, ka kawo mana ɗauki, koda ranmu ne ka ɗauka mu koma gare ka, zaifi mana sauƙi akan wannan wulaƙantacciyar rayuwar da muke yi mara ƴan ci, Ya Allah badan halinmu, mu ci albarkacin Annabin mu Annabi muhammand (SAW) mafi soyuwa agare ka_.........."
sosai ta runtse idanuwanta, ta yi zurfi acikin zancen zucin nata, ta soma jin motsin buɗe ƙopar ɗakin su acikin kunnuwanta, wani irin tsoro da firgici ne ya lullu6e ta, hakan yasa taƙi buɗe idanuwanta don taga wanene
Takun tafiyar mutun ta soma ji a cikin É—akin nasu, kamar ana kewaye É—akin, ji take kamar ta buÉ—e idanuwan nata sai dai tsoro ya hana tayi hakan, tana cikin wannan Halin taji wani irin matsiyacin bacci yana fisgarta, na ban mamaki, duk yadda taso ta tsayar da kanta don kada ta runtsa hakan ya faskara don tuni yai awon gaba da ita anan inda ta ke a kwance, Tsawon lokaci Deeja tana sharar baccinta, Har dare ya nutsa, hasken saman É—akinsu ya É—auke Na floor lamps É—insu Ya kunna kanshi, Haskensu ya gauraye ko'ina tamkar da rana.
A matuƙar firgice ta farka tare da ware manyan idanuwanta kan ceilling ɗin ɗakin, Zuciyarta na harbawa sama sama cike da fargaba, tunawa da ƴan uwanta ne yasa tai wuf ta miƙe a zaune, wani iko na Allah Kaf ɗinsu babu wanda ke kwance a ƙasa sai ita, duk suna asaman gadajen su, tamkar wani abu bai ta6a faruwa ba, babu ɗigon jinin mutun ɗaya daya kasance a cikin ɗakin, an goge komai babu shi, ɗakin ya koma fes ɗin shi, tsabar mamaki ne Yasa ta miƙe Jiki na kerma ta ke bin kowani gado da kallo, bacci su ke yi Hankali kwance, Jikinsu lullu6e da bargunan su, da sauri ta kalli gadon jamimah, tana a kwance Ga azeeza itama kwance saman nata gadon, Haka zalika parveen da rubina, eve and yasmin, suna kwance saman nasu gadajen Hada Sarah da hibba, uwa uba, Angel itama tana naɗe cikin bargonta tana bacci, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, wannan bakomai bane,
Jikinta na kerma ta nufi gadon Angel ta sanya hannu tare da yaye bargon jikinta, don taga idon raunin goshinta na nan, babu jini akan fatar fuskarta, sai dai akwai alamun fashewar goshinta dana tsinin hancinta, sai la66anta, yanayinta ya nuna alamar cewa babu raÉ—aÉ—in ciwo atattare da ita, kamar an kwashe mata shi,'
sakin bargon Angel ta yi tare da juyawa da sauri ta nufi gadon jamima, hannu tasa tana duba fuskarta itama babu jini, tunawa ta yi da haƙorinta data gani ɗazu a ƙasan ɗakin su, koda ta buɗe bakin ta, tabbas haƙorin ta ɗaya ya cire, sai dai babu kumburi abakinta, lamarin ya ɗaure mata kai, mamaki ne ƙarara akan fuskarta.
matsawa ta yi zuwa gadon Azeeza ta yaye bargonta tare da leƙa fuskarta, ko hawaye babu, yatsun hannayenta dai ne da suka faffashe, amma babu jinin daya tsastsafo akansu, idan ka kalli ciwon kamar ya kwan biyu.
Ɗaya bayan ɗaya saida Deeja tabi kowannan su ta duba shi, lafiyar su ƙalau, Babu ko zazza6i a jikin su.
Deeja ta ruɗe sosai ta rasa tunanin me za ta yi game da wannan iko na Allah, har aranta ta aminta da cewa Allah ne ya ji ƙansu ya kawo musu ɗauki, sai dai ba ta san takun tafiyar wanene taji ɗazu ba, a cikin ɗakinsu, tabbas akwai wanda ya shigo.
"Ruwa zan sha, maƙoshi na zafi"! Muryar Angel ce ta fargar da ta, a hanzarce ta mayar da dubanta gare ta, farkawarta Kenan daga bacci, Ko idonta bata buɗe ba, a gaggauce Deeja ta nufi ƙarƙashin gadon Batul ta ɗauko ɗaya daga ciwon bottle waters ɗin da Su Jamima suka 6oye musu ɗazu, ta nufi gadon Angel ta haye sama tare da taimaka mata ta miƙe zaune, bayan ta buɗe murfin ta kafa mata abaki, ta dinga kur6ar ruwan,'
Hankalin Deeja ba ƙaramin kwanciya yai ba, bayan ta kammala ta maida murfin robar ruwan ta ajiyeta daga ƙasan gadon, kafin ta ɗago idonta akan fuskar Angel dake ƙoƙarin buɗe nata idanuwan.
Ido cikin Ido suke kallon Juna ita da Deeja, muryarta na É—an rawa ta furta"Ina Danish ya ke"! Abunda ya fito daga bakinta kenan, fuskarta É—auke da matsananciyar damuwa ta amsa mata da cewa"Har yanzu ba a dawo dashi ba" girgiza kai Angel ta yi"ba'a dawo dashi ba, meyasa naji a jikina cewa danish ya ta6a ni!" A ruÉ—e Deeje ke kallonta, Jin abunda tace, tunani ta shiga yi anya Angel bata samu ta6in hankali ba?
Da alama ta manta abubuwan da su ka faru, ta manta jahilin bugun da tayi musu, kamar wadda tayi loosing memory É—inta.
Ganin yadda Deeja ta tsareta da ido yasa tace"meyasa kike kallo na? Wani abu ya faru ne? Nayi ma ki tambaya baki bani amsar da zata gamsar dani ba, nifa naji Danish Ya ta6a jikina, taya zaki ce min ba a dawo dashi ba'? A ruÉ—e ta yi mata maganar.
Deeja bata amsa mata tambayarta ba, saima ta sanya tafin hannayenta biyu ta tallabo fuskar Angel, murmushin yaƙe ne ya bayyana akan fuskarta wanda bai kai zuci ba, a hankali ta furta Alhamdulillah, Allah na gode maka, daka kawo min mafita, da yanzu bansan ya zan yi ba, Naji daɗi dana ga ƴan uwana suna bacci cikin kwanciyar hankali, na ƙara yarda cewa addinin musulunci gaskiya ne, Kuma ubangijin mu Allah maji roƙon bayinsa ne, idan su ka yi imani dashi, babu tantanma zai agaza musu a lokacin da suke cikin buƙatar taimakon shi.
da alama taji daɗi sosai, da irin taimakon da Allah ya yi musu, daba don haka ba, da yanzu batasan awani awani hali zasu tsinci kan su ba, domin kuwa ba ƙaramin jiki zasu ji ba, Jinya ce zasu yi bata wasa ba, sai kowa yaji a jikin shi, musamman Jamima da haƙorinta ya 6alle, da kuma Sarah wadda aka buga ta da ƙasa qugunta ya daku, da sauran waɗanda aka buga kansu jikin bango.
"Deeeja na kasa fahimtar komai, dan Allah ki yi min bayani, inaso inji meya faru ne, naji araina kamar wani abu ya faru, sai dai na kasa tunawa......" da sauri Deeja tace"in sha Allah ba za ki tuna ba"
Maganar Deeja ta ɗaure mata kai, yunƙurin saukowa tai daga saman gadonta, da sauri Deeja ta ruƙo hannunta"Ina zaki je? Dare ne fa! Ki koma ki kwanta" ba tare data juyo ta kalle ta ba, tace"Toilet zan shiga" Jin haka yasa Deeja sakin hannunta, Hankalinta bai kwanta da kalaman deeja ba, shiyasa tace mata za ta shiga toilet ne don ta samu damar ƙarewa ɗakin nasu kallo, duk don ta samu ta tuna abunda ya faru, don ta fahimci cewa akwai wani abu da take 6oye mata.
Tana ƙarasa saukowa daga saman gadon, kaitsaye idanuwanta suka sauka akan shimfiɗar su Haris, nan take taji gabanta yai wani irin bugu na tashin hankali, ganin babu kowa asaman gadajen su, sai bargunansu da matashin kansu, babu haris babu naufal babu javed da mubeen.
A fujajen ta waiwayo tana fuskantar gadajensu Sarah, Tsayar da idanuwanta ta yi akan shimfiÉ—ar Gabriel wayam babu kowa saman gadon shi, zuciyarta a hautsine ta wurga eye balls É—inta kan gadon Majnoon, babu kowa, tsabar ruÉ—anin da ta shiga ya hana ta furta komai, Tuni deeja ta lura da yanayin da ta shiga.
saukowa ta yi daga saman gadon, ta nufi Inda Angel ta ke atsaye ta ɗaura hannunta ɗaya saman kafaɗarta, idanuwan ta acike tab da ƙwalla ta soma magana