← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 179

Sashe 62

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Giants ne, Sun kawo abinci kuma sun tafi dashi bansan meyasa ba"?

Waro ido waje batool tayi fuskarta da alamun tashin hankali tace"mun shiga uku! Shikenan yau mun rasa abincin da zamu ci, angel meyasa baki tada mu daga bacci ba lokacin da suka zo"? Fuskarta a hargitse tayi maganar,

"Ina fa kokarin in tada ku daga bacci, sai naga suna tattara kayan abincin, kuma har roƙonsu nayi su tsaya amma basu saurare ni ba....." tunkan takai ƙarshen maganarta, suka soma Jin shessheƙar kukan Parveen, gaba ɗaya suka kai idanuwansu akanta, zaune take saman gadonta, ta wage baki tana ta kuka, Jin cewa Giants sun zo sun tafi da abincinsu,

Sautin Kukan Parveen ne ya farkar da sauran Ƴan uwan nasu, Hanna tana hamma tace"wai meke faruwa ne? Me akayi ma Parveen take kuka"

Javed yace"Yanzu haka rigimartace kawai, duk tabi ta tashi mutane daga bacci, saboda tsabar jarabarta,

Hannu danish ya sanya tare da zame bargon da ke lullu6e a jikin shi, idanuwanshi sun ƙanƙance daƙyar yake iya ware su, saboda baccin bai ishe shi ba,

Haris dake faman yin miƙa yace"kun yi shiru baku bamu amsa ba, Meyasa take kuka"?

Batool ce ta bashi amsa da cewa"Saboda giants sun kawo abinci, Angel bata samu damar tada mu daga bacci ba, har suka tafi da kayan abincin shine take ma kuka"

saboda tsabar tashin hankali Har suna haɗa baki wurin cewa"What? giants sunxo sun tafi da abincin mu"? Amatuƙar ruɗe kowannasu yake faman baza ido,

Dafe kai javed yayi"ae shikenan mun rasa abinci yau, Mu da ganinsu kuma sai gobe, kafin lokacin mun gama jigata,"

Yana rufe baki Rubina tace"Wlh bazan iya jurewa ba, da matsiyaciyar yunwa na farka yau...." mubeen yace"ae ba ke kaÉ—ai ba, Cikina har wani kukan yunwa yake yi" yayi maganar yana shafa stomach É—inshi,

"Yanzu ya zamu yi kenan"? Naufal ne yayi tambayar yana kallonsu,

Azeeza tace"Mu ci hakuri kawai, Idan munji ƙishi musha ruwa sai mu kwanta muyita bacci har gobe tayi, Harara Hibba ta jefa mata daga inda take zaune saman gadonta"Wannan fa ba abun wasa bane azeeza, magana ake ta babu abincin da zamuci yau, " azeeza tace"idan bamuyi haƙuri ba, to ya zamuyi" tayi maganar tana watsa hannayenta,

Da buÉ—ar bakin deeja sai cewa tayi"bakowa bane ya jamana xama da yunwa ba face angel, meyasa da suka zo baki tashe mu daga bacci ba? Saboda tsabar mugunta,'

Shiru angel tayi don bazata biye mata su yi cece kuce ba, tun da ita halinta ne bata gajiya da shiga sabgar mutane,

"Kodai naje na faɗa ma tsohuwa, ta taimaka tayi magana, su giants su dawo mana da abincin mu," fuska amarairaice parveen tayi maganar, tagama shan kukan nata, taga babu mai lallashinta ta haƙura don kanta,

"Koda kinje babu abunda tsohuwa zata iya yi mana, kema kinsani" yasmin ce tayi maganar, fuskarta a hade, shi dai danish yayi lamo saman gadonshi yana bin bakunansu da kallo, sam baison hayaniyar da suke yi, don ba yadda ya iya ne daya dakatarsu,

Bakowa Angel tafi jima tausayi ba, Sai danish sanin cewa Jiya baici abincin shi ba, ya basu suka cinye, yanzu ga shi sun rasa abincin yau, dole yafi kowa jin yunwa bawan Allah,

Yau fa ba kanta, Duk jikinsu yayi laushi, Ko toilet babu wanda ya shiga don yin wanka ko wanke fuska, damuwarsu Yunwar da zasu kwasa yau, an sanyasu yin azumin dole batare da sunyi niya ba,

Saukowa haris yayi daga saman gadonshi, Ya wuce gadon danish, daga ƙasa ya zuƙunna tare da ruƙo hannun danish acikin nashi, idonsu cikin na juna, yace"ɗan uwana, ya jikin naka"? Cikin sanyin murya ya amsa mashi da cewa"da sauƙi sosai," murmushin haris yayi"Am glad to hear that, Nayi kewarka sosai na tsawon kwana biyar din nan, saina ji kamar na rasa wani sashe na jikina ne" wannan maganar ta haris ba ƙaramin faranta mashi rai tayi ba, shi kanshi ya shaida irin ƙaunar da haris ke yi mashi aduk duniya bai da tamkar shi,

"Haris, nima nayi missing É—inku sosai, har bazan iya misaltawa ba........." dakatawa ya É—anyi da yin maganar, ya juya bayan shi yana kallonsu batool,

"Can i talk to u"? Danish ne yayi tambayar yana kallon kowannnsu, Jin haka yasa suka sauko daga saman beds ɗinsu, suka Nufi gadon danish, a kewaye da gadon suka tsaya curko cirko suna yi mashi Yaji ki, ƙasa ƙasa da murya yake amsa masu, yayin da idanuwanshi ke akan fuskar angel dake a tsaye can nesa da su, Batool ce ta lura da kallon angel da yake yi, ta fahimci yana son itama tazo ne, amma tasan bazai iya kiranta ba, hakan yasa ita ta kira ta da kanta tace"Ki zo mana, danish yana son yin magana damu" tafiya ta soma yi xuwa bakin gadonshi ta tsaya a gefensu tare da goya hannayenta saman kirjinta,

Calmly yaci gaba da cewa"dama inaso nayi maku godiya ne, bisa irin nuna kulawarku agare ni, kun damu dani sosai, nasan kunyi missing ɗina na tsawon 5 days da bana acikin ku, nima kuma duk da bana atare daku kuna araina, i luv u so much guys......" tun da ya soma magana suka natsu suna sauraronshi, Yaushe rabon da suji danish yayi magana mai tsayi irin wannan har sun manta, lallai jiki yayi sauƙi suka ayyana hakan acikin ransu,

still bai janye idanuwanshi daga kan fuskar angel ba, itama shi É—in take kallo, So yake yayi mata godiya amma ya kasa, ita kanta angel É—in ta lura da hakan amma saita basar, Jira take taga idan zaiyi mata magana,

Muryar javed ce ta janyo hankalinta wurin kallonshi" Angel Amadadin danish, muna matuƙar yi maki godiya, bamu ta6a tsammanin zaki iya taimakon shi ba, a lokacin da kika nemi alfarmar mu baki dama, Sai gashi kin bamu mamaki, Ta silarki danish ya fara wartsakewa, tabbas ke ɗin alkhairi ce agare mu, Kuma yakamata Gaba ɗayanmu mu fahimci cewa angel masoyiyarmu ce ba maƙiyiyar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon fuskokin sauran ƴan uwan nashi, kafin yaci gaba da cewa"Idan har muka yi ma angel biyayya zamu koyi abubuwa da dama awurinta wanda bamu Iya ba, zata wayar mana da kanmu, kuma zata ɗaura mu akan hanyar dai dai, Amma fa shawara ce nake bamu muyi tunani," yakai ƙarshen maganar yana jira yaji amsar da zasu ba shi,

Deeja ce tace"Amma ae tsohuwa tace mana kada mu yarda da ita, mu daina sakewa da ita, zata gur6ata mana tarbiyarmu ne, kuma tana yi mana ƙarya nidai gaskiya bazan yarda da angel ba, " tayi maganar tana maƙe kafaɗarta, maimakon angel taji haushin maganar deeja, Saima ta saki murmushi saboda ta lura hada quruciya ke ɗawainiya da ita,

"maganar da Javed ya faɗa gaskiya ne, Angel masoyiyarmu ce, kuma komai take yi mana tana ƙoƙarine don taga mun dawo akan hanyar dai dai, Ina roƙon duk wani dake ƙyararta acikinmu ya ajiye makaman yaƙin shi, yazo mu rungumi juna, faɗa ba namu bane," a tsanake batool takai karshen maganarta,

"Silar angel, danish ya samu sauƙi, bashi kaɗai ba, Tun jiya da angel ta raira mana waƙar nan mai daɗi da sanyaya zuciya, gaba ɗaya jikin kowannanmu yayi sanyi,......" dariya angel tayi jin abunda azeeza tace,

"Ba waƙa bace, Karatun al'qur'ni ne mai girma, " cike da mamaki suka maimaita kalmar"Karatun al'qur'ani mai girma" Hanna tace"menene ma'anar hakan? Ko zaki iya fahimtar damu"? Tayi maganar a ƙagare da son Jin amsar da angel zata basu,

Ƙoƙarin buɗe baki tayi da niyar ta ba Hanna amsar tambayarta, Sai dai kafin tayi yunƙurin yin hakan, Suka Jiyo Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Nan fa hankalinsu gaba ɗaya ya koma akan ƙopar ɗakin,

Fitowa tayi daga Cikin É—akin tana dogara sanda, Fuskarnan a tur6une babu walwala acikinta, da sauri Su hanna suka Nufe ta, Cikin girmamawa suka gaishe da ita, babu yabo babu fallasa ta amsa masu,

Parveen tace"tsohuwa Yunwa muke ji, Giants sun kawo mana abinci, A lokacin bamu farka daga bacci ba, har suka tafi da shi"

Jinjina kai tsohuwa ta É—anyi tana bin fuskokinsu da kallo, Su kansu sun lura da canjin dake atattare da ita, kamar wani abu na damunta, Hanna tace"tsohuwa Baki da lafiya ne? Naga kamar bakya Acikin walwala," sai lokacin tsohuwa ta buÉ—e baki tace" kunyi kuskure da ku ka bari giants suka juya da abincin nan, ai kunsan basa wasa da lokaci, meyasa baku farka daga bacci ba har suka tafi? Bayan kunsan cewa Ba dawowa zasuyi ba, idan har suka tafi dashi"!

Muryar Parveen tamkar zata fashe da kuka tace"yanzu shikenan bazamu samu abinci ba yau"? Idanuwanta suka cicciko da ƙwalla,

angel dake acan tsaye ruƙe da qugu, ta tunkari inda suke, agaban tsohuwa ta tsaya tare dacewa"Irin ƙaunar da kike masu kenan? ashe uwa zata Iya barin ƴa'ƴanta da yunwa? Alhalin ita tacika cikinta ta ƙoshi! Waye bai kuskure rayuwa? Yin bacci ya zama laifi kenan? Inbanda rashin lissafi taya mutumin dake bacci zai zama mai laifi? Meyasa su giants ɗin da suka zo basu ajiye mana farantan abincin ba, su sai su tafi idan yaso aduk lokacin da muka farka sai mu ci, Amma saboda tsabar zalunci shine suka tattara kayan abincin suka tafi dashi, Anya kuwa tsohuwa? Cike da tuhuma takai ƙarshen maganar tana kallon fuskar tsohuwa, ta tsareta da waɗannan Jagwalallun idanuwan nata,

Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Haka dokar Aikin Giants suke! Lokaci gare su, basa wasa da aikinsu, idan suka kawo abinci suka ga babu wanda yazo yaci zasu kwashe ne su tafi dashi," wannan itace amsar da tsohuwa taba angel,

Mamaki akan fuskar angel tace"Wannan wata irin dokace mara kan gado mara tsari? Wannan ae horo da yunwa ne! Abincin ma da sau ɗaya ake bamu shi a rana, mun ƙoshi bamu koshi ba wannan ba damuwarku bace, Shine kuma harda wata dokar in an kawo abinci bamu hallara ba, za'a juya dashi? Me hakan ke nufi? Wai mu me kuka ɗauke mu dabbobi ko me? A harzuƙe angel tayi maganar,

Wata irin gigitacciyar tsawa Batool ta daka ma angel, gaba É—aya saida kowa ya razana hatta danish dake a kishingiÉ—e saman gadonshi saida ya firgita ya nemi zaucewa,
Chapter 62 · 0% Book details