Sashe 109
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya tana faɗin"Ae ba'a dawwama cikin farin Ciki a gidan kurkukun ƙaddara, Waɗannan sabbin gadajen da ku ka gani, Ƴan uwanku ne za'a kawo, Nan badajimawa ba, daga yau zuwa gobe zaku Iya ganinsu, Sa'annan kayan amfanin da aka zuba muku acikin makewayinku, Nice nayi fafutuka wurin ganin an sanya muku su....." dakatawa ta ɗanyi da yin maganar, haƙiƙa sun ji dadin jin cewa itace ta sanya aka kawo musu kayan amfanin, a karo na farko kenan da tayi musu abun kirki, gani suke kamar akwai wani abu da take so ta fada musu, wanda ba lallai bane yayi musu daɗi ba,
Duƙar da kai ƙasa tsohuwa tayi na wani lokaci, suna ta kallonta, kafin ta ɗago idanuwanta akan fuskokinsu, sai suka ga kamar ruwan hawayene kwance acikinsu.
Kafin su yi yunkurin yi mata magana ta riga su cewa"Ku É—auko mini akwatin nan da aka kawo muku" da sauri naufal da haris suka je suka janyosu agabanta suka kwantar da akwatin nan,
"Kunsan menene aciki"? Suka haɗa baki wurin cewa a'a, murmushi ta saki tare da cewa"Sabbin Uniform ɗinku ne masu kyan gaske, tare da takalma, da sauran abubuwan da nasan zaku buƙata, Zaku Iya buɗewa ku gani"
Wani irin farin Ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu, Jiki na rawa suka zuƙunna agaban akwatunan haris ne jagaba wurin buɗe akwatin farko, Kaya ne danƙare acikinshi, A ninke suke an jera su, uniform ɗin farko Launin baƙaƙe ne sun sha banban da kalar style din na jikinsu,
"Mutun Uku, Su fiddo da kayan a hankali sai ku dudduba a tsanake" acewar tsohuwa,
Suka amsa mata da toh, haris da deeja ne sai angel suka sanya hannayensu cikin akwatin suna zaro kayan tare da ɗago dasu suna warware ninkin da aka yi musu, haɗaɗɗun riguna ne masu kyan gaske, basu da banbanci da Wrap coat, suna da igiyoyi guda biyu a jikinsu, tsayin su zai kai har gwiwowinsu, sannan suna da dogon hannu, gefe da gefe akwai aljihu ajikin rigunan, yadin jikinsu mai matuƙar kyau da ɗaukar ido, kowace shirt tana da ƴar vest launin red acikinta, Uniform ɗin farko masu launin Black, Mallakin angel da batool ne tare da Danish, Numbobinsu ne akai no 1 no 2 zuwa 3, A bayan rigunan, wani abun mamaki daga ƙasan numbers na jikin uniform ɗinsu, Kowa da sunan da aka sanya mishi su ukun nan, da turanci aka rubuta sunayen anyi amfani da launin Ja, A bayan rigar Batool an rubuta
*HEART BEAT*(Bugun Zuciya) rigar danish an rubuta *PRISON SHIELD* (Garkuwar kurkuku) yayin da ita kuma Angel abayan rigarta aka rubuta *DESTINY* Wannan suna dai ya É—aure musu kai, Har tsohuwa su ka tambaya menene ma'anar sunayen tace masu kada su damu, suna ne kawai, Angel bata yadda da sunayen ba, basu kwanta mata aranta ba, tabbas akwai dalilin dayasa aka rubuta musu sunayen abayan rigunansu, su ukun nan, Ita dai fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane.
kowace riga tana da dogon wadonta masu kyan gaske, Uniform dinsu azeeza sunyi kyau sosai launin Ja, iri É—aya ne dana su Danish banbancin kala ne kawai, Sai kuma rubutun dake abayan rigunansu Angel, babu anasu rigunan sai dai numbobinsu, abun burgewa kowace riga tana da cotton scarves, Irin É—an mayafin nan da mazan indiya suke É—aurawa asaman wuyan su.
*â¤â¤â¤PRISONERSâ¤â¤â¤*
Launin ja, tun daga kan fuskokinsu zaka shaida irin tsantsar farin cikin da suke aciki, tun kafin ma su sanya kayan ajikinsu har sun fara Imagining irin kyan da zasu yi musu, tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, daga ƙasan Uniform ɗin nasu, wasu haɗaɗɗun rigunan sanyi ne masu dan banzan kyau, launin bright rust red da kuma dark brown, sai faman ɗaɗɗaga rigunan suke yi suna kallonsu, sun rasa bakin magana saboda tsabar murna, ga wasu hats haɗaɗɗun hulunan gayu na mata dana maza masu kyan gaske, Ƙasan akwatin gaba ɗaya sabbin takalmansu ne kala bibbiyu, zubin anckle boots da kuma slippers, Yara fa sun zama ƴan gayu, kaf saida suka zazzage kayan akwatin suna ta kallonsu suna yaba kyawunsu haɗi da nuna irin farin cikin da su ka yi.
Tsohuwa tace su buɗe ɗayan kwatin su duba kayan dake acikin shi, tasan zasu Yi farin ciki, akwai wata ƴar kyauta data sanya musu aciki, taban mamaki, Jin wannan maganar yasa suka tattara uniforms din da komai na akwatin farko suka maidasu ciki suka datse shi, cike da zumuɗi Angel ta buɗe musu akwati na biyu, a danƙare yake da kaya, abu na farko da suka fara Cin karo dashi, hankys ne launin ja da baƙi, mai ɗauke da sunayen kowannan su, sun yi matuƙar Yi musu kyau, Hada mayukan gyaran Jiki dana gyaran gashi, da Set na kayan gyaran akaifa, ga wasu ribboms na ɗaure gashi, Yawanci duk basu san yadda zasu yi amfani dasu ba, amma tunda ga angel sunsan zata Yi musu bayanin komai.
"Tsohuwa, kince akwai gift da kika sanya mana, Ta na ina? Ko su ne waÉ—annan kayan"? Angel ce tai mata tambayar tana kallonta,
Tsohuwa tace"Ku duba daga can ƙasan akwatin zaku same ta" Jiki na rawa suka ɗaɗɗaga kayan har suka taddo wrapping sheet ɗin dake nannade da wani abu, wanda shape ɗinshi daga sama round ne mai faɗi, ƙasa kuma ya ɗan tsuke, kallon juna suka yi cikin ƙagara da son ganin menene aka nannaɗe haka, kowa ya baza ido suna jiran ganin menene, A tsanake angel ta soma warware wrapping sheet ɗin awani slow, Sai da ta taddo ƙarshen shi ta yakice paper ɗin da aka nannaɗe shi, A hankali take bin shi da kallo, Su azeeza duk suka zazzaro idanuwansu ganin wani abun ban mamaki da basu ta6a gani ba, shin kunsan menene? Nasan Kun ƙosa kuji, To ba komai bane face*MADUBI,*
wani irin farin Cikine ya bayyana akan fuskar angel da ƙarfi ta ambaci sunanshi MIRROR, yayin da take kallon kyakkyawar fuskarta wadda yaushe rabon da taga suffar face dinta tun tana atare da daddynta tsawon shekara huɗu da watanni yama kusa ci ka 5yrs,
Ya burge ta sosai, madubin Round shaped ne mai matuƙar ɗaukar ido, Yadda kasan ƴan ƙauyen ido sama, Haka suka kewaye madubin Suna Kallon fuskokinsu, sun saki baki kamar lehen sakarai, In ka cire mutun ɗaya wanda Yaja gefe ɗaya kamar baya maraba da ganin sabon abunda basu ta6a gani ba, su kuwa sai ihu suke Yi suna Murnar ganin fuskokinsu kamar suyi hauka, Ɗakin nasu ya cika da Hayaniyar su, abun nema ya samu, Tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, Sun tasa madubin gaba Na tsawon lokaci, sai faɗi suke wai dama haka fuskokinmu suke? azeeza tace Wai Allah na, dama haka nake da kyau? Komai na fuskata ɗan ƙarami mai kyau, Hanna tace"Nima fa kyakkyawace, Idanuwana farare ƙyal, ga dogon hanci, " deeja tace"duk da ban kai ku kyau ba, amma Nima ba daga baya ba, Manyan kyau ne dani," tana rufe baki yasmin tace"ni matsalata idanuwana ƴan mitsi mitsi kamar zasu shige ciki, hancina luluyayye, har ƙwara bakina ma, " gaba ɗaya suka kwashe da dariya hada tsohuwa, parveen dai ta ƙura wa madubin ido ita da Rubina sai kallon fuskokinsu suke yi kamar zasu lashe su, har sai da haris Yakai hannu ya danƙwashi kawunansu tukunna suka zabura, suna faman wurga mashi harara,
"Idan kun gama kallon ƙurallan ku bamu abun muma mu duba kyawun fuskokinmu" Wani irin kallo parveen tai mishi tare da cewa"shawara kyauta haris, Ka haƙura da duba abun nan, saboda Ina jiye maka tsoron munin fuskarka da zaka gani, zai iya sawa zuciyarka ta buga" kafin haris ya bata amsa deeja ta riga shi cewa"Ki Iya bakin ki Parveen, Ƙarya kike kice wai haris bai da kyau, don kawai yana da duhun fata ne, kuma ahakan Ba ƙaramin kyakkyawa bane, kawai kina yi mishi baƙin Ciki ne," takai ƙarshen maganar tana jifarta da harara, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma haris ba, koba komai deeja ta yabe shi, abunda ma ya ƙara burgeshi, da kanta ta ruƙo madubin daga hannun angel ta kanga mashi saitin fuskarshi, Atare suka haɗa faces ɗinsu suna kallon juna ta cikin madubin sai dariya suke saki,
Satar kallon danish angel tai don taga a wani yanayi yake ciki, Yana zuƙunne a tsakaninsu javed da mubeen, yaɗan duƙar da kanshi ƙas, Yayin da idanuwanshi suke akan yatsun hannun shi, Aranta tace Shi kuma haka zai ƙare! Kowa Yana kallon fuskarshi acikin mirror, banda shi, wama ya sani ko aljani ne, shiyasa yake tsoron Ya haska fuskar shi Cikin madubi, Amma dai zanso Ya kar6i mirror ɗin nan kodan yaga irin baiwar kyan da Allah yae mishi......." kasa ƙarasa maganar tai ganin yana ƙoƙarin ɗago da kanshi da alama yaji ajikinshi ana kallonshi,
da sauri ta duƙar da nata kan ƙasa tana faman tsuke baki, koda ya ɗago Bai ci sa'ar haɗa ido da ita ba, Sai suka haɗa ido da Haris Ya sakar mishi murmushi yana faɗin" Deeja bani abun nan in haska ma Sarkin kyau fuskarshi, Nasan yau danish ko bacci bazai iya yi ba idan har yayi tozali da kyakkyawar fuskarshi," Ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu Ya ruƙo madubin, Ya ɗan yunƙura ya miƙe ya nufi danish, sai dai kafin ya ƙarasa danish yae saurin kifa kanshi saman gwiwarshi, bubbuga bayanshi haris yae tare da cewa
"Kar ka bani kunya mana, Kowa ya share ka sai ni na damu dakai, pls bro Ka É—ago ka kalli fuskarka," batare daya É—ago da kanshi ba yace"Haris i can't bana son ganin shi, pls ka janye shi daga saiti na, zai iya affecting lafiyata,"
jin wannan maganar ta Danish yasa duk suka É—ago da idanuwansu suna kallon shi, Lamarin ya É—aure musu kai,
Deeja tace"But why danish? Kowa fa ya duba fuskarshi Kuma lafiya lou ba wani abu daya cutar damu, sai kai zaka ƙi kallon fuskarka? Javed yace "Haba danish idan ma saboda abunda ya faru a tsakanin mu dakai ne yasa kace ba za ka duba abun nan ba, Ina mai baka haƙuri just for today a matsayin mu na ƴan uwa mu kalli fuskokinmu acikin baƙon abun nan,"