← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 179

Sashe 80

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan tafiyar giants, Safa da marwa suka shiga Yi acikin É—akin duk babu daÉ—i saboda rashin Æ´an uwansu, an rairaye su yanzu sun koma su goma sha É—aya, Babu mutun HuÉ—u acikinsu, dole suyi maraicin rashinsu atare dasu, ga zullumin da suke Yi da fargabar ko awani hali suke Ciki?

Idan suka gaji da zagaye É—akin sai su koma saman gadajensu su zauna, a haka har dare ya rutsa dasu, ÆŠakin Ya yi duhu, Rubina ce ta kunna musu fitilun ÆŠakinsu Haske Ya gauraye ko'ina, Kowa Ya kishingiÉ—a saman gadonshi,

Ta yi tsammanin sunyi bacci Jin É—akin Yayi tsit, Juyawa tayi tare da fuskantar gadon danish, idonshi biyu Ya kwantar da kanshi saman pillow,

"Meya hana ka bacci"? Amsa ya bata da cewa"ke zan tambaya, me kike Yi har yanzu baki runtsa ba"? Ta6e baki ta É—anyi"Damuwace ta hana ni bacci, ina jin duk babu daÉ—i zuciyata"

Shiru baice mata komai ba, sai dai kallonta da yake yi, kamar yadda itama take kallonshi, Gani yayi ta miƙe ta sauko daga saman gadonta, a bakin gadonshi ta zuƙunna tare da ɗaura hannayenta saman mattress ɗinshi

Da É—an mamaki yace"lafiya"? Murmushi ta É—ansaki kafin tace"Bakomai kawai ina so Muyi fira ne," mayar mata da martanin murmushin yayi, har dimples É—in shi ya lotsa,

"Ai ni ban Iya fira ba, in fact ko surutu ban iya ba, sai in ta kama dole," tace" toh ka ƙaddara ta kama dolen ne, tambaya ce nake so In yi maka hope zaka amsa mini" ɗaga mata gira yayi tare da cewa" Am all ears"

Kame kame ta shiga Yi, abun ma sai yaso ya ba shi dariya, hannun shi yakai saman sumar kanta ya ruƙo gashinta tare da cewa"Faɗa mini mana, indai nasan amsa zan baki," tace"Dama nayi mafarki ne, kana da wuƙa, shin dagaske ne"? Da budar bakinshi sai ce mata yayi"you're trying to be smart, tell me the truth waya faɗa maki cewa ina da wuƙa? Nasan ba mafarki ki kayi ba,"

Hararar shi Tayi jin ya ganota, taso tayi mishi wayau,

"Na ta6a tambayar batool, cewa Inaso zanyi amfani da wuƙa, shine take faɗa mini cewa Akwai wadda tsohuwa ta baka lokacin da kace mata kana so ka rage yawan sumar kanka," Wani kallo taga yana binta dashi, Can kuma yace"me zakiyi da ita"? Dariya tayi tare da cewa"bafa kai zan kashe ba, Nasan abunda kake tunani kenan, ni kawai inaso In rage sumar kaina ne, bama ni kadai ba hada batool itama Gashin kanta yayi yawa yana takura mana" tayi maganar tana yamutsa fuska,

Ta6e mata baki yayi"Nima namanta inda na ajiye ta, ko na mayar mata da ita ko ban mayar mata ba, namanta, "

A ƙagare tace"pls ka daure ka tuna, Zata yi mana amfani,"

"Angel idan Kina son In rage maki gashin kanki ne, Ba buƙatar Yin amfani da knife, i can use my nails to cut it for u" zaro ido ta ɗanyi da mamaki tace"taya zaka Iya amfani da akaifa wurin rage yawan gashin kaina, baka ga yawanshi ba ne"

"Idan kin bani dama zan Jaraba" girgiza mashi kai tayi"a'a, Ni dai nafi so Inyi amfani da wuƙar, Idan Allah yasa ka tuna inda ka ajiyeta sai ka ɗauko mini" ta faɗi hakanne saboda ba gashin take so ta rage ba, Wuƙar take buƙata saboda tsaro,

"Its Okey, Kije ki kwanta, duk time dana tuna i will let u know" ya karasa maganar tashi tare da jan bargo ya lullu6e jikinshi har zuwa kanshi, Miƙewa Ta yi tare da juya ta koma saman gadonta ta kwanta, A daren ranar saida ta roƙi Allah Akan Yasa itama ta fara Menstruation kodan saboda giants su ɗauketa sukaita ɗakin nan taga uban me suke aikatawa, Idan Allah yasa Hankalinta bai gushe ba kenan,

Wasa wasa Yau har tsawon One week kenan ba'a dawo dasu Hannah ba, Tun suna sanya damuwa aransu har suka haƙura suna zaman jiran tammani, Tun daga ranar da aka ɗaukesu Kullum sai ta roƙi Allah tsakar dare Akan Ya karesu aduk inda suke, Bayan haka kuma Tana yawan yin addu'ar akan Allah yasa ta fara jinin itama, duk don saboda da taga me ake yi musu,

Yanzu ta kaiga ko tsohuwa basu tambaya dangane da ƴan uwansu, saboda sun fahimci cewa ita ɗin bata da banbanci da totan masara awurinsu, bi ma'ana bata da amfani duk wani magiyar da zasu Yi mata bazata iya Sanyawa adawo masu da ƴan uwansu ba, sai da ta gaya musu ƙarairakinta,

Yau tsawon 3 weeks kenan Suna ta baza ido suga an dawo musu Da ƴan uwansu, Sai acikin satin karshe na watan da suka shiga, Aranar da daddare suna zaune saman carpet Suna fira sun kunna fitilun ɗakinsu, Ba zato ba tsammani sai ga giants Huɗu sun shigo cikin ɗakin nasu Kafaɗunsu Ɗauke dasu Hannah, A wani irin zabure suka miƙe suna kallonsu, wuce wa cikin ɗakin giants su ka yi adai dai bakin gadajensu hannah masu ɗauke da numbobinsu suka kwantar da kowannansu, Atare suka juya suka fuce daga cikin ɗakin,

Azeeza sai tsalleta take Yi tana murna an dawo musu da ƴan uwansu, Su batool kuwa Kallon Kallon suka shiga Yi atsakaninsu, sun rasa gane farin Ciki zasu Yi ko baƙin Ciki? Ga shi dai an dawo musu da ƴan uwansu da suka daɗe suna jimamin rashinsu, Sai dai ga dukkan alamu Basu acikin hayyacinshi, Har ƙwarama lokacin da aka dawo dasu parveen sunyi magana, Amma waɗannan bayin Allahn, Idanuwansu ne kaɗai suke motsi, Numfashin su da hucin zafi yake fita, ƙafafuwansu duk sun tale, Wani abun tashin hankalin ma, Hada Yakushin akaifa asaman wuyansu, fatar wurin tayi jawur, jini ya kwanta, La66ansu sun faffashe, Hankalinsu danish ba ƙaramin tashi yayi ba, Matan kuwa Sun sha kuka kamar ransu zai fita, Angel tace Yanzu babu buƙatar saita yi musu bayani game da cewar cutar dasu ake yi yau dai gashi nan zahiri idanuwansu sun gane masu, Sahun yakushin akaifar dake asaman wuyansu, Haƙiƙa sun yi matuƙar girgiza, hatta mazan saida suka zubar musu da hawaye saboda tsabar tausayinsu daya kama su, daren ranar basu Iya runtsawa ba, A gefen gadajensu Hanna suka zaune suna Jimami, har garin Allah Ya waye, Koda suka je bakin ƙopar ɗakin tsohuwa suka kwankwasa mata, Munafukar bata fito ba, Hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa Bata da gaskiya,

Haƙiƙa sunsha wahala wurin Yin jinyarsu Hannah, kamar bazasu Rayu ba, jikinsu yayi tsauri sosai, babu sauƙi saima abunda ya qara gaba, sai da takai ga Komai daga kwance suke yin shi, fitsari kashi, duka dai, a ƙalla sun ɗauki tsawon one month suna yin jinyarsu kafin Allah yasa suka samu sauƙi Jikinsu ya warware, Suka koma kamar yarda suke da, Sai dai babu wani walwala atattare dasu, Suna yawan firgita, Ko kiran sunansu Kayi sai kaga sun ɗan zabura, Idan suna bacci kuma Sun dinga sambatu suna koke koke, Ahaka ahaka dai da taimakon Allah angel Tana yi musu addu'a duk rana ta Allah, Sai gashi sun wartsake, Sun dawo normal, Bayan sunji sauƙi, Sai ga tsohuwa ta shigo ɗakinsu, Wani irin mugun kallo da suka dinga jefa mata, ba arziƙi taja sandarta ta koma Cikin ɗakinta, Angel taso ace su hanna sun Iya tuna abunda ya faru dasu amma sun kasa, kwata kwata basu Iya tuna komai, Da ace sun tuna koda kaɗan ne to kuwa tabbas sauran ƴan uwan nasu zasu Ƙara gasgata maganarta, duk da ayanzun ma ta fara cin nasara saboda kokwanton su Ya ninku akan gidan kurkukun, Sun sha jinin jikinsu, Sun fara tsorata da lamarin, Haris har alƙawari ya ɗauka akan bazai ƙara bari giants su ta6a wani acikin su ba, Sai dai in bayan babu ranshi, danish dai bamu san matsayarshi ba, Shi dai baice komai ba, Iya nuna 6acin ranshi akan fuskarshi ne, Amma su naufal mubeen da javed duk sun ɗauki wannan alƙawarin na hana atafi da ƴan uwansu idan basu da lafiya! Kallonsu kawai angel take Yi domin kuwa tasan babu abunda zasu Iya yi, ba wani ƙarfi gare su ba, balle suce zasu Iya ja da giants, Mutanan da take tunanin Ba cikakkun mutane bane, Ƙarfinsu bana jinsin bil'adama bane,

Bayan komai Ya lafa tsawon Watanni uku wani iko na Allah, cikin matan ba wanda ya ƙara Yin Menstruation, kamar an ɗauke musu da jinin, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma angel ba, Yanzu hakalinsu ya ɗan kwanta,
Chapter 80 · 0% Book details