Sashe 32
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
BATOOL!" ta kai ƙarshen maganar tana nuna wannan mai kyakkyawar matashin nan da sandar hannunta tare da wannan matashiyar mai kama da larabawan, sunayen su ne ta faɗi, masu kalar uniform ɗin angel," Angel dai wani irin kallo take binta da shi, mamakin ta ke taya akai tsohuwar take karantar abunda mutun ke saƙawa acikin zuciyarshi"? "Ni duk ba wannan ba! Meyasa aka kawo ni gidan nan? Nifa ba marainiya bace, Ko da ace ni marainiya ce taya za'a sato mutun akawo shi cikin wannan munafukin ginin ace wai gidan marayu ne? Taya akai ku ka san cewa ni marainiya ce? That means ku ne ku ka kashe mun mahaifina kenan? Sannan ku ka raba ni da mahaifiyata itama ku ka kashe ta ko? Dama can kuna bibiyar rayuwata in ba haka ba ta ya akai ku ka san ina a hannun fulanin daji? Har ku ka tura aka ɗauko ni? wai menene manufar ku tayin hakan huh? "Gidan kurkukun ƙaddara Gidan Marayu ne wanda suka rasa gatansu, duk yaron da ki ka gani acikin prison ɗin nan to ba shi da iyaye! Zai iyayiyuwa iyayenki sun mutu batare da sanin ki ba, sa'annan duk wanda ki ka gani acikin kurkun nan na jininsa ne ya sadaukar dashi zuwa gare mu don mu gatanta shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin shi" tsohuwa ce ta kora mata wannan jawabin, Still angel ta gaza fahimtar inda zancen ta ya dosa cikin ɗaga murya tace"If it's an orphanage, then why is it called a prison? You just wanna mislead me with your lies, I won't believe you, idan har kuna son zaman lafiya ku mayar dani inda ku ka ɗauko ni cikin salama in ba haka ba zan addabi rayuwar ku" takai ƙarshen maganar tana haki ta harzuƙa sosai, Sauran prisoners ɗin duk suna a tsaitsaye cirko cirko suna sauraran tattaunawar baƙuwar yarinyar da su kayi tare da tsohuwa, tun da suke a gidan prison ɗin ba'a ta6a samun yarinyar me taurin kai da kafiya ba irin baƙuwar da suka tsinta yau acikin su, "Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!" A wani slow angel ta juya don taga wani isasshe ne ya yi mata magana, sauke idanuwanta ta yi akan kyakkyawar fuskarshi sai ka rantse da Allah bashi bane ya yi maganar, daga ganin shi akwai izza atattare da shi," "Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!" Tana huci takai ƙarshen maganar tare da ɗauke idanuwanta daga kan shi ta mayar dasu kan tsohuwar" ke kuma tsohuwa na dawo gare ki! Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, Kuma a faɗa mun uban wanene ya sadaukar dani xuwa gidan nan! Saboda idan na samu damar fita daga cikin sa inje in naƙasa rayuwar shi" Lallai angel ba sauƙi a zafafe take magana tana huci yadda kasan mayunwaciyar zakanya, Sassauta murya ta yi"idan kun saba rainawa mutane hankali kuna ɗaukosu ku kawo su cikin gidan nan da sunan zaku gatanta su, to ni ba kalar su bace, ni ba marainiya bace kuma ni bana buƙatar gatanci daga wurin ku, Gata na shi ne Allah koda kuwa bani da kowa a duniyar nan ina da Allah," Murmushi tsohuwar tasa ki yayin da take kallonta tace"buri ya yi kama da mutun, da ace baki yi wannan haukan ba, da bazan tabbatar da cewa ke ɗiya ce ga Zaheer tajuddeen ba, hatsabibiyar yarinyar da ta addabi mahaifinta ina da labarin ki tunkafin zuwan ki duniya" Ruƙe qugu angel ta yi yayin da take kallonta, jin wani soki burutsi da tsohuwar ta yi mata, "Bazan yi jayayya dake ba, saboda nasan wacece ke! abu ɗaya nake so in tunasar maki shi ne, ke marainiya ce mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan mahaifiyar ki ma ta rasu babu ita, danginki kuma su ne suka damƙa mana ke don mu raine ki wannan dalilin ne yasa kika kasance acikin Gidan kurkuku saboda mu ne gatan ki, kuma muke da alhaƙin ɗaukar responsibilities na rayuwarki, kama daga cin ki shan ki da sauransu....idan ki kayi biyayya mu kuma zamu sama maki farin ciki," Hawaye ne suka wanke fuskar angel jin cewa mahaifinta ya rasu duk da bata gasgata maganar dattijuwar ba cikin shessheƙar kuka tace"kiji tsoron Allah ki fada mun gaskiya daddy na bai mutu ba! Kuma ƙarya ki ke yi mun na cewa dangina ne suka kawo ni cikin wannan kurkukun," Matsawa tsohuwar ta yi zuwa inda angel take atsaye, ta tausasa murya tare da cewa"ƴar nan ki kalle ni tsofe tsofe dani da ace na ta6a aure da yanzu nayi tatta6a kunne dake, amma har kika iya buɗe baki ki kace mun ƙarya nake yi? Lallai babu tarbiya atare dake shiyasa ƴan uwanki suka kawo ki prison don mu koya maku ladubban rayuwa, sa'annan ina mai ƙara tabbatar maki da cewa mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan, nasan ke bakisan da hakan ba saboda ya jefa ki acikin ruwa shiyasa baki ga lokacin da ya rasu ba, idan har kina son sanin komai game da mutuwar mahaifin ki, zan fada maki hatta wanda su kayi silar mutuwar shi, amma fa ba yanzu ba sai naga hankalin ki" Tana kai ƙarshen maganarta, bata jira angel ta bata amsa ba, ta juya tana dogara sandarta a daddafe ta nufi ƙopar shiga ɗan ɗakinta, Zubewa angel ta yi saman guiwowinta tare da fashewa da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, komai ya sire mata zuciyarta ta karaya dama saida ranta ya bata cewar kodai daddynta ya mutu ne, dama yasan mutuwa zai yi shiyasa ya jefa ta acikin ruwa shi kuma ya tsaya waɗannan mutanan da suka biyo su da mota suna harbinsu suka kashe mata daddynta, Ƙara sautin kukan nata ta yi tana ambaton"Innallahi wa'inna ilahirraji'un! Wayyo Allah na daddy na! Sun kashe mun daddyna shikenan sun raba ni da farin ciki na, sun raba ni da Mahaifina sun naqasa mun rayuwata, ya Allah ka ɗauki raina nima in huta........."sosai take kuka fuskarta ta yi jawur jaga jaga da hawaye hada majina, Duk suna tsaye suna kallonta, an rasa wanda zai lallashe ta, saboda basu saba da ita ba, wasu kuma shakkar ta suke ji yayin da wasu kuma suke jin haushinta saboda ta zagi tsohuwa wadda suka ruƙa amatsayin mahaifiyarsu, Tuntana yin kukan nata da sauti har takai ga kakarewa muryarta ta dissashe ta, anan ta yanke jiki ta faɗi a sume. Guntun tsoki matashin saurayin nan yaja, tare da ta6e lips ɗinsa ya yi gaba abun shi ya nufi gadon shi me ɗauke da no 2 haka kowani gado yake da number, Suma sauran matasan suka wuce zuwa saman gadajen su, mutun ɗaya ce ta kasa tafiya saboda tsananin tausayinta da take ji, kuma ita har ga Allah yarinyar ta kwanta mata aranta, Hannayenta bibbiyu ta sanya tare da tallabo kan angel dake a ƙasa ta ɗaura shi saman cinyarta, juyawa ta ɗanyi tare da kallon kowannan su dake kishingiɗe saman gadonshi, tsayar da ƙwayar idonta ta yi akan Hannah ta ɗan ɗaga murya tare da cewa"abunda ku kayi ba ku kyauta ba, kuna ganin halin da take aciki na rashin mahaifinta amma kowa ya yi shiru ya wuce ta babu me lallashinta? Ta6e baki hanna ta yi"rashin mahaifi akanta aka fara rashi? tafi mu gata fa dayawan mu nan tun muna jarirai aka kawo mu kurkukun nan, mun ta shi ba mu san kowa namu ba, bamu da wanda ya damu damu tsohuwace kaɗai gatan mu, kuma agaban mu ta zageta tass ba ta ga girman gemun ta ba, saboda rashin kunya irin ta ta," Hanna na rufe baki, wani saurayi dake a cikinsu tuttu6e6e me suna haris yace"nifa bata kwanta mun araina ba, kyau kamar aljanna, kuma daga gani ma duk mun girme ta, "yana rufe baki mubeen ya kar6e da cewa"bazata wuce shekara takwas ba wannan jibi yadda take raira mana kuka kamar ba'a gama rainon ta ba," Gaba ɗaya suka sanya dariya, ran batool ya 6aci, "Is enough, kunsan bana son hayani ya" wannan kyakkyawar saurayin ne da tsohuwa ta kira da sunan DANISH ya yi maganar tare da lumshe idanuwanshi ya kwantar da kanshi saman pillow, Jinjina kai batool tayi, jiki asanyaye ta sauke kan angel a ƙasa, ta miƙe da hanzari ta nufi toilet ɗinsu, jim kadan ta fito hannunta ɗauke da ruwa sai sauri take yi saboda zubar da yake yi, adai dai saitin fuskar angel ta yarfar da ruwan, nan take taja dogon numfashi batare da ta buɗe idanuwanta ba, yatsun hannunta ne kaɗai suke kerma, miryarta adisashe take faɗin daddyna bai mutu ba, he is still alive ina ji araina sai sambatu take yi, ga wani irin matsanancin ciwon kai daya far mata ga yunwa da ƙishir ruwa duk ita kaɗai, Cikin sanyin murya batool ta yi mata magana"SISTER" har cikin kunnanta taji sautin kiran yadda kasan wadda aka tsokano a hargitse ta buɗe idanuwanta da suka kada su kayi jawur da su, yunkurawa ta yi da hanzari ta ɗauke kanta daga kan cinyar batool, ta jefa mata uwar harara tare da cewa"bana son ganin kowa a kusa dani, bana son kowa,"