Sashe 26
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 5 min read
Duk rana ta Allah sai angel da danejo sunje Bakin ruwan nan, Kullum ne wani lokacin har dare suke kaiwa abakin ruwan, atare suke fita kiwon shanu, hatta tatsar nono sai da danejo ta koya mata, da wasu abubuwan nasu na fulanin dajin, baiwar Allah ba yadda za ta yi don dole take rayuwa a cikinsu, Allah ne kaɗai yasan halin da Zuciyarta take aciki, a kullum idan suka kwanta suna Bacci, tare da su danejo da hasiya, bata iya runtsawa, Zama take yi tsakar dare, tadinga kukan zuci tana roƙon Allah yasa daddynta yana A raye, ta karaya sosai, wani sashe na zuciyarta yana raya mata cewar Waɗannan mutanan da suka Biyo su suna harbin motarsu sun kashe mata daddynta, amma kuma har cikin ranta tana jin cewa Yana A raye, taya zata tabbar da hakan? Ita dai bata ga gawar mahaifinta ba, balle tashai da yabar duniya, A ƙalla Angel tayi shekara Biyu A hannun fulanin dajin nan, A lokacin Tafara Jin fulatanci sama sama saboda xama da tayi da su,
duk da sabon da tayi da su hakan bai sa ta fasa ƙudirinta na guduwa daga Cikin dajin ba, duk don saboda taje neman Mahaifinta, abunka ga Yaro ga kuruciya, zuciyarta saita dinga raya mata cewa ta gudu taje gidan su, zata samu mahaifinta agida.
A ranar data shirya guduwa daga Cikin dajin, Sai da tabari kowa Ya yi bacci, batare da jin tsoro ba ta fito daga Cikin bukkar, Ko'ina duhu kasancewar darene sosai, Cikin sanÉ—a take tafiya Tana nufar cikin dajin, duk in taji kukan shanayensu saita firgita, gani take kamar zasu farka daga bacci ne su hana ta guduwa
Ganin tayi nisa daga inda bukkokinsu suke, ta soma tunanin wace hanya zata bi don ta fita daga cikin dajin, ga duhu ko'ina, sai É—an hasken farin watan da ba'a rasa ba, tana cikin wannan tunanin ta jiyo muryar mutun a bayanta, A firgice ta juya don taga wanene, Hasken fitila tagani amma ba ta iya tantance wanda ya biyota ba, duk da taso ta É—auki murya,
Tattare zanin jikinta tayi na kayan fulanin da suka bata sune sanye ajikinta, ta watsa aguje cikin dajin tamkar zata tashi sama, tana gudu tana tuntu6e wani lokacin har faɗuwa kasa take yi a haka za ta daure ta miƙe taciga ba da gudu tana waiwayan mutumin daya biyo ta, ganin shi ma yana gudu, nan fa ta ƙara gudun nata, tsawon lokaci suna wannan ƴar guje-gujen cikin dajin ita da mutumin daya biyo ta har Allah Ya kawo ta bakin titi a galabaice ta haye saman titin, wani irin jirine ya soma ɗibar ta. Ta fara tangal tangal za ta faɗi ƙasa, a haka ta jure taciga ba da gudu, ba zato ba tsammani sai ga wata zungureriyar mota baka ta yi parking a inda take a tsaye, A slow murfin motar ya zuge,
Zuro Hannu aka yi daga cikin motar aka ɗauke ta, murfin motar ya koma ya zuge da kanshi, da gudu motar ta miƙi titin.
A daidai wannan lokacin Danejo ta faɗo saman titin a galabaice hannunta riƙe da ƴar filita. Ashe ita ce ta biyo Angel, don ta ga lokacin da za ta gudu daga Cikin bukkarsu.
Waro ido waje ta yi ganin dankareriyar motar da ta ɗauki Angel, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta fara yin tozali Mota, Tsoro duk ya cika ta, hankalinta ya yi matuƙar tashi, ganin an raba ta da Angel. A gefen titin ta tsugunna tana kuka tamkar ranta zai fita. Wannan shi ne silar rabuwar Angel da Fulanin Daji.
A nan gefen titin Danejo ta yanke jiki ta faɗi a sume, a washe garin ranar ƴan uwanta suka farka daga barci, ba su ga Angel da Danejo ba, hankalinsu ya tashi gabaɗaya suka bazama cikin dajin neman su. Har Allah Ya sa Su Bawuro suka tarar da ita a gefen titi ita kadai a kwance ba numfashi, lamarin ya yi matuƙar girgiza su, tunda suke da Danejo ba ta ta6a yin nisan kiwo irin na yau ba, sun yi mamakin ganin ta ita kaɗai ba tare da Angel ba.
Bayan komawarsu cikin rigarsu, Suka yayyafa ma danejo ruwa ta farfaɗo, fashewa ta yi da matsanancin kuka tana faɗa masu yadda suka rabu da Angel. Duk jikinsu ya yi mugun sanyi, kowa bai ji daɗin lamarin ba, sai dai ba su da yadda za su yi. Da ma tsintacciya ce duk da sun yi sabo da ita, zuwan Angel cikinsu ba ƙaramin farinciki ta samar masu ba. Sun ji takaici da baƙin cikin ɗauke tan da aka yi, to ya za su yi? Allah Ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan.
Da daɗi da ba daɗi haka Danejo ta ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da takaicin rashin Angel, ta rame ta ƙanjame tamkar ba Bafullatanar nan ba mai yawan fara'a mai son yin rawa, yanzu ta koma salihar ƙarfi da yaji. Kullum cikin yin zazza6i take, kuma kullum tana akan hanyar zuwa bakin ruwan nan inda suke yawan zuwa ita da Angel su zauna. Kafin tafiyar Angel ta ba su labarin mahaifinta daya gudo da ita cikin daji, a lokacin ta fara jin Harshensu na Fulatanci, ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da su.
*ANEELERH*
Kwance take saman haɗaɗɗen gadonta na gidan su, A gefenta ƙaramin yaronta ne wanda bai wuci shekara ɗaya da ƴan watanni, Jikin shi na a sanye da overall pink colour, Kyakkyawan yaro rainon madara, fari tass kamannin shi sak na mahaifiyar shi, tamkar ta yi kakin shi, kan shi a cike yake da kwantacciyar suma mai laushin gaske, mommyn ta shi dake kwance gefen shi tana ta sharar bacci Rigar bacci ce a jikinta launin sky blue,