← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 179

Sashe 33

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 5 min read

❤dedicated to Aunty kubra❤

*Daga alƙalamin Boss Bature✍️*

*E11

Tuntsirewa su hanna su kayi da dariya jin yadda ta gwasale Batool,
"Bai kamata ki yi mun haka ba, kowa yaƙi kula ki a lokacin da ki ka suma ni ce kaɗai na damu da ke amma shi ne kika watsa mun ƙasa a ido"?
Cigaba da kuka angel ta yi ba tare da tace mata uffan ba, ita kaÉ—ai tasan raÉ—aÉ—in da take ji,
Zuba mata ido Batool ta yi batare da ƙyaftawa ba,
Adai dai wannan lokacin suka soma jiyo motsin buɗe ƙopa, gaba ɗaya suka kai idanuwansu bakin benan
Turo ƙopar a kayi waɗannan Giants ɗin ne su uku masu sanye da baƙaken kaya su ka shigo hannayen su ɗauke da Faffaɗan wooden trays masu ɗauke da kayan abincin su, kowanne na a ruƙe da faranti ɗaya,
Bayan sun ƙarasa sauko wa kai tsaye su ka nufi jan carpet din nan, a saman shi su ka sauke farantan, kafin suka ja gefe ɗaya suka goya hannayen su asaman ƙirjinsu, dama ƙa'idar aikin su ce idan suka kawo masu abinci ba su tafiya tsayawa suke yi har sai sun kammala tukunna su kwashe kayan abincin su tafi, kuma basa magana sai in ta kama dole,
one by one su ka soma saukowa daga saman gadajen su, izuwa gaban kayan abincin kowa ya samu wuri ya zauna, ruƙo hannun angel batool ta yi tare da cewa"ki taso muje mu ci abinci," fusge hannu angel ta yi" bazan ci ba, ni kawai a mayar dani inda aka ɗauko ni,"
"This is the only chance u ave to eat, we get food once a day, if u don't eat it now, u will lose ur food," cikin sigar lallashi batool ke yi mata magana, ita kuwa ta kangare akan baza taje taci abincin ba.
Miƙewa batool ta yi duk bata ji daɗi ba, taso ace yarinyar ta saki jiki da ita amma ta nuna kafiya, wuri ta samu saman carpet ɗin ta zauna,
faranti na farko Grilled Chicken wraps ne guda goma sha biyar a jere, iya adadin su, faranti na biyu kayan marmari ne nunannu an yayyanka su, a faranti na uku wooden cups ne guda goma sha É—aya, sai jugs guda biyu É—aya na ruwa me sanye É—aya kuma na Lemu ne da aka hada da nau'ikan kayan marmari,
A tsanake kowa yakai hannu ya ɗauki chicken wraps ɗinsa, suna Ci suna satar kallon angel, batool dai bata ji daɗi ba, ganin taƙi tasowa taci, ga nata nan ajiye shi kaɗai, idan wani ya cinye tayi asara, in kuma ba'a samu wanda yaci ba, zasu tafi da shi ne.
baiwar Allah ta galabaita sosai, ga jaraba nacin ta ga yunwa ga kuma abinci amma taƙi ta shi taje ta xauna cikin su ta ci, wani irin ƙululun baƙin ciki ne acan ƙasan zuciyarta, eyes ɗinta a rufe hawaye ke gangarowa saman kuncinta,
Ƙasa ƙasa da murya batool ke yi mata magana"ki taso ko ci," maƙe kafaɗa angel ta yi, alamar baza ta zo ba,
A ƙarshe ma sai ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta jure a haka ta taka izuwa gaban waɗannan Giants ɗin ta ci burki ta tsaya,
"Ku maida ni inda ku ka É—auko ni, bansan zunubin dana aikata ba, da har za'a sato ni izuwa cikin wannan kurkukun," magana take yi masu amma ko uffan basu ce mata ba, domin kuwa a tsarin aikinsu basa magana da prisoners,
"Dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa waÉ—annan da kike gani basa ji basa gani, idan kuma kika ce xaki matsa masu jikin ki ne zai gaya maki"
Juyawa angel ta yi da sauri don taga wani ja'irin ne ya tsoma mata baki, É—aya daga cikin matasan ne me suna naufal,
Nuna shi ta yi da yatsan hannunta"karka kuskura ka ƙara shiga hurumina, ba ruwan kowa da rayuwata," juyawa ta kuma yi kansu cikin xafin rai tace"magana nake yi maku, ku faɗamun wanene ya bada umarnin a kawo ni wurin nan? Shiru basu tanka mata ba ga shi bata iya ganin koda ƙwayar idonsu ce balle tasan ko suna kallon ta,
Zubewa tayi saman guiwowinta tana raira masu kuka tamkar ranta zai fita,
tana ji tana gani suka kammala cin abincin, Giants É—in nan suka tattara kayan abincin suka kama hanyar fita daga É—akin, ranta ya 6aci ta dunga É—ura masu ashar kamar É—iyar maguzawa,
Da gudu tabi bayansu tana kuka tana zagin su, ƙopa suka buɗe suka fuce, ƙopar ta datse, ta dinga bugun ƙopar tana kuka, silalewa tayi bakin kopar ta kwantar da kanta, tako ina babu sauƙi,
"Idan kina jin bacci, gadon ki shi ne no 1 zaki iya zuwa kije ki kwanta" batool ce ta yi mata maganar, tana a tsaye saman matattakalar benan, buɗe idanuwanta tayi waɗanda suka kaɗa su kayi jawur, ta watsa mata harara muryarta a disashe tace"wai ke mayyace? Ki rabu dani mana kamar yadda sauran ƴan uwanki suka yi," jinjina kai batool ta yi," I worry about you but you don't worry about yourself, i won't disturb u again tun da kin buƙaci hakan, just whenever u change ur mind, za ki iya yi mun magana,' jiki a sanyaye batool ta juya ta koma cikin ɗakin,
Tuni kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, wasu suka kama bacci wasu kuma suna zaune suna fira,
Chapter 33 · 0% Book details