← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 179

Sashe 42

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Angel taci gaba da cewa" ina zargin jiya ke ce kika kwaɗe mun kaina da sandar hannun ki, Saboda kinga ina ƙoƙarin kwance shirinki, wato so ki kayi nima ki ɗaure mun kaina ta yadda zan manta da komai, tabbas kinso ki yi nasara sai dai Allah bai baki ikon yin hakan ba, farkawar dana yi daga bacci komai dana manta sai da ya dawo cikin kaina, Kuma bazan fasa faɗa masu Allah ba, har sai na fargar da su,
"Taya kenan zaki iya aiwatar da hakan? Ko kina tunanin zaki iya sarrafa tunaninsu ne? Yaran da ni na raine su da hannu na, na gatanta su, tun da suke basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, komai suna samu ba'a abunda ban yi masu ba, matsayin uwa nake a wurinsu, a haka kike tunanin zasu ji maganarki fiye da tawa"? Tsohuce ta yi maganar yayin da take sakin wani irin bazawarin murmushi,
Wani irin kallon rainin wayau angel tayi mata"Wlh tun da nake arayuwata ban ta6a ganin Muguwar maca ba, Azzaluma kuma macuciya irin ki ba!"
Yadda tayi magana batare da jin ɗar ba, ya yi matuƙar girgiza tsohuwa,
"Wai ke baki jin tsoron Allah? Ki tuna fa komai kike yi Allah yana kallon ki, har kina da bakin da zakice kin basu gata? Kin raine su? Kuma har kike kiran kanki a matsayin uwarsu? Tirr wlh ji nake kamar inyi kakin majina in watsa maki akan fuskarki saboda natsane ki, Wlh nafi son mutuwa ta so dubu dake!" Zuba mata ido tsohuwa tayi tana kallon Ikon Allah,
Sassauta murya angel tayi Idanuwanta cike tab da ƙwalla tace"Kin cuci rayuwarsu, kin gama dasu, ni banmasan ya zan kwatanta irin cin zalinsu da ki kayi ba, kuma ga dukkan alamu kin sani kike take sani, dan baki yi kama da jahila ba, Kawai salon tsabar mugunta ne, Yaran nan ko nonon raƙuma suka sha iya abunda zasu yi kenan, Ga sunan Wasu kala da su they don't even know anything about the one who created them because you never told them, cos of your wickedness Kin barsu a cikin duhu, sun zo duniya a wahalce kuma zasu koma a wahalce, Idan yau ɗayansu ya faɗi ya mutu menene makomarshi dan Allah meyasa ki ka yi musu haka? Meyasa?.........." kasa ƙarasa maganar angel tayi saboda wani irin ƙuntataccen kuka daya kubce mata, kuka sosai ta fashe da shi,
Tsohuwa kuwa ta kafe ta da waɗannan Kwala kwalan idanuwanta nata, masu kama dana ƴan ƙwaya,
Cigaba da magana ta yi"Idan wani zunubi suka aikata maki, bai kamata ki É—auki fansa ta wannan hanyar ba, balle ma nasan basu aikata maki komai ba, To kodai cikin danginsu wani ya yi maki badaidai ba, shiyasa kike É—aukar fansa akansu" ta yi tambayar idanuwanta jawur hawaye duk sun wanke fuskarta,
Tun da suka soma magana babu wanda ya farka daga cikin masu yin baccin, tamkar wasu matattu,
Jinjina kai angel tayi"dama nasani bazaki bani amsar tambayata ba, sai dai ki kafe ni da ido kina kallo," ta yi maganar cikin sanyin murya tare da sanya hannunta da dama tana share hawayen dake silalowa,
Kafin ta ɗaura da cewa"Allah ba azzalimin bawansa bane, Allah zai bi masu haƙƙinsu, inda na gode ma Allah, Mutuwa tana akan kowa, Walau mutun walau aljan, akwai kwanciyar ƙabari akwai kuma hisabi, Ina fata duk kin shirya ma wannan........" Muryar Batool ce ta katse ta ta hanyar kiran sunanta"ANGEL" koda tsohuwa taji muryar batool, Sai ta juya da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar shiga ɗakinta,
Har ta kusa shiga ciki muryar angel ta sake katse ta da cewa"Baki san Su ji me muke tattaunawa ne shiyasa kika nemi hanyar guduwa? Allah dai yana a madakata yana jiranmu, kuma inaso ki sani Zanyi amfani da ilmin da nake da shi, da kaifin basirar da nake da shi wurin Sarrafa tunaninsu, Kuma zansa su kar6i addinin musulunci, after that I will fight for our freedom, because no one deserves to live a locked up life!
Tsawon mintuna tsohuwa bata motsa ba, kuma bata juyo ta kalli inda angel take ba, can dai taci gaba da dogara sandar, har samu ta shige cikin ɗakinta taja ƙopa ta rufe,
Fashewa da wani sabon kukan angel ta yi, da sauri batool ta sauko daga saman gadonta, tazo gaban gadon angel ta zauna daga gefenta,
Muryarta aruÉ—e take faÉ—in"Sister what's wrong with u? and why are u crying"? Kallonta angel tayi da idanuwanta da suka rune, muryarta a karye tace"Batool ina kuka ne saboda ku"
"But why"?
"it will be hard for you to understand me, even if i tell you, so just forget about it," cikin shessheƙar kuka ta yi maganar,
Dafa shoulder É—inta batool tayi"Pls ki faÉ—a mun meyasa kike kuka sabo da mu"?
"Baki ga tsohuwa ba"? Angel ce ta yi mata tambayar, girgixa kai batool ta yi"Banganta ba, tazo ne? Ita ce ta saki kuka"?
Girgiza kai tayi"A'a, Mubar maganar, inaso zan shiga toilet," daga haka ta zuro da ƙafarta daga saman gadon ta sauko, ta nufi toilet ɗinsu, Ta tafi tabar batool da tunanin dalilin kukanta, meyasa ta ke yin kuka saboda mu? ta yi ma kanta tambayar da bata da amsarta,

Tunda ta shiga Cikin toilet ɗin taci burki ta tsaya Idonta na akan Window nan dake a jikin bango, wadda ta ƙwallafa ma rai akan son Fasa glass ɗin jikinta, don ta samu damar dura wa Cikin kurkukun.

Hannu tasa ta share hawayen dake akan fuskarta, Cikin zuciyarta ta soma yin magana"rana ta farko dana tsinci kaina cikin gidan kurkukun nan, A ƙagare nake dana nemi hanyar da zan fita daga Cikinsa, Amma Ayanzu bana sha'awar Barinsa batare da waɗannan bayin Allahn ba, Kuma batare da ƙwaƙƙwarar hujja da zan yin amfani ba, wurin ganin na tarwatsa duk wani shirinsu, Zanbi komai asannu domin Cimma nasara, Bi'iznillahi,'

Angel yarinya ce mai kaifin basira Fiye da tunanin mai tunani, wayan dake gare ta yafi ƙarfin shekarunta, wasu ɗabi'un nata da halayanta sam ba irin na yara bane, she's genius"

Lokacin da ta fito daga wankan, A tsaye ta samu Batool tana jiran na ciki ya fito ta samu ta shiga itama tayi wankan" Kallon juna su ka yi,

Murmushi Batool ta sakar mata tare da cewa"tun É—azu nake jira na ciki ya fito in samu nima in shiga in yi wanka,
Angel tace"Wani ya shiga sauran toilets É—inne"?
Jinjina kai batool tayi"Eh, Hanna ce ta shiga É—aya, É—ayan kuma Danish ne da deeja suka shiga Ciki," Har wata zabura angel ta yi jin abunda batool tace"What! danish da deeja ne suka shiga atare? Saboda me"?
Fuskar batool asake tace"Dama idan babu wuri kuma uziri ya kama mu, mutun biyu suna amfani da toilet É—aya......."
tunkafin Batool takai ƙarshen maganarta, Angel ta yi gaba zuwa ƙopar sauran makewayin, Rai a matuƙar 6ace takai hannu tana Bubbuga ƙofofin tamkar zata Fasa su,
"zaku fito ko saina 6alle ƙopar"? Tana huci ta yi maganar, Bama tasan wanne suke a ciki ba,
Kusan atare suka buɗe ƙofofin toilets ɗin, na biyun Hanna ce ta leƙo kai, Na ƙarshen ne Deeja da danish suka fito, wani matsiyacin kallo Angel ta shiga binsu da shi from head to toe, hannun shi na a ruƙe da rigarshi, ita kuma iya rigarce har guiwarta, wandonta na hannunta,
"lafiya kike bubbuga mana ƙopa"? Fuska aɗaure deeja ta yi mata tambayar"
Dakuwa angel ta sakar mata"Ungo nan, Ku dukanku ku kar6a ku raba,"

Kallon juna su ka yi don basu fahimci me take nufi ba, Runtse ido tayi zuciyarta na tafarfasa ta ambaci"Allahu ajirni fil musibati......
Batool sai faman tamyarta take yi lafiya? Meya faru"? Ware idanuwanta ta yi akan fuskar deeja da ta danish, sae faman lumshe eyes É—in shi yake yi, da alama bacci bai ishe shi ba, Sam tarasa ta ina zata fara, wato su awurinsu ba laifi bane idan mace da namiji sun shiga toilet É—aya, tun zuwanta bata ta6a sanin suna yin hakan ba, Sai yau da take ji awurin batool ta kuma gani da idanuwanta,

Cizon lips ɗinta tayi tamkar zata fasa su, Cikin fusata ta nuna Deeja da hannu"Zoki wuce, Ki jira idan ya gama ki shiga" maƙe kafaɗa deeja tayi"babu inda zanja, meye naki aciki?
Wata irin gigitacciyar tsawa angel ta daka mata, Saboda tsabar ruÉ—i a firgice danish Ya koma Cikin toilet din,"
Da gudu Sauran Ƴan uwansu dake acikin ɗakin suka faɗo Toilet area ɗin, Haris da su aziza,
"Meke faruwa ne"? Javed ne yae tambayar, Batool tace"Nima bansani ba, ranta ya 6aci ne saboda na faÉ—a mata cewa idan uziri ya kama mu kuma babu wuri mutun biyu suna shiga toilet É—aya shine take fushi,"
Harara haris ya watsa mata tare da cewa"To ke meye naki aciki da har zaki nuna 6acin ranki akai"?
Matsawa angel tayi Saitin inda haris yake a tsaye, Kafin ta soma magana atsanake,
"Saboda hakan bai dace ba, Koda kuwa Namiji da namiji ne su shiga toilet ɗaya balle kuma Mace da namiji, bazan bari ana aikata 6arna batare dana hana ba, don haka daga rana irin ta yau, idan har na ƙara kama mutun biyu acikin toilet ɗaya, Saina Karanta ma shi charman dudu Cikin shi ya kumbura ya mutu kowa ya huta"

Jin wannan maganar ta angel yasa hankalin kowannansu ya tashi, musamman deeeja tuni idanuwanta sun cicciko tan da ƙwalla,

"Ya kike so muyi idan uziri ya kama mu, a lokaci É—aya"? Hanna ce tayi mata tambayar,
"Sai ku matse koma menene ku ke ji, idan na ciki suka kammala suka fito sai mutun ya shiga"
"Ammaaaa......."kasa ƙarasa maganar haris yayi ganin tana nannaɗe hannun rigarta alamar za ta yi dambe,
"Abi Umarni na azauna lafiya, Shine kawai idan kuma mutun yace zaiyi mun gardama, yasan me zai biyo baya,"

Gaba ɗaya duk suka sha jinin jikinsu, juyawa tayi tare da kallon deeja"Ke kuma Munafuka, zoki wuce ki jira idan ya kammala ki shiga, ni dama sam ban yarda dake ba, da wasu idanuwanki tubarkalla kamar na kwartan mazuru, idan shi yana da ta6in hankali ai ke da hankalinki, Sullu6iyo kawai, zaki wuce kosaina Zubar maki da haƙoran gaba"? Jiki na rawa deeja ta ƙarasa fitowa daga cikin toilet ɗin Taja ƙopar ta rufe,
Chapter 42 · 0% Book details