Sashe 104
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Am sorry angel....ni ne silar komai, pls stop crying it's hurting my heart, bazan juri ganin ki, cikin wannan Yanayin ba......" Wani irin matsiyacin kallo ta jefa mishi, idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, dama tunda ta farfaÉ—o daga suman da ta yi fuskarta take a kumbure, cheeks É—inta sunyi ja, La66anta sunyi luhu luhu ,
Duk da irin kallon da take wurga mishi hakan baisa shi ya dakata da yin maganar shi ba,
"Angel, nima bada son raina ba, Na miƙa batul ba, bana tunanin akwai wanda yakai ni ƙaunarta acikin ku, Batul tamkar jinin dake yawo ajikina take, Na rayu da ita tun ban mallaki hankali ba, mun shaƙu da juna, kusan komai atare da ita muke yi, a duk lokacin da lalurata ta tashi ta rashin son hayaniya, ita ce take jana ajikinta, ta rungume ni har sai taji na samu natsuwa tukunna take saki na, Meyasa ba zaku fahimce ni ba? Ku yi tunani mana, Ni har raina zan iya sadaukarwa akanta...." daƙyar ya ƙarasa magnar tare da kifa kanshi saman katifar gadonta, da alama kuka yake yi,
Gaba É—ayan su kuka suke yi babu mai lallashin wani acikin su, duk wannan budurin da ake yi Æ´an uwansu dake ta sharar bacci babu wanda Ya motsa acikinsu, kamar matattu, idan har ba danish Yaje ya tashe su ba, zaiyi wuya su farka da kansu, In ba wani iko na Allah ba, saboda baccin nasu bana Allah da annabi bane, shi kaÉ—ai yasan mai ya yi musu da har suka kama yin shi, duk da yai hakan ne don ya kawar musu da damuwar dake acikin zuciyarsu,
a hankali ya É—ago da kanshi daga saman mattress É—in, idanuwanshi sunyi jawur dasu, launinsu ya ciza sosai, fuskarshi tayi jawur da ita, Cikin sanyin murya yace"dame xanji? Idan har kuka juya mini baya zan shiga damuwa, Ni bazan hana Ku tsane ni ba, idan ma takama ku buge ni son ranku, but please don't say that you'll cutt me off from u, abun zaiyi mini yawa, ga rashin batool ga kuma rashin Æ´an uwana,"
Tun da ya soma yin maganar, ta tsagaita da yin kukan idanuwanta na fuskantar ceilling, Haƙiƙa kalaman danish sun kashe mata jiki, sun so suyi tasiri akanta, Sai dai a duk lokacin da ta tuna da irin yadda ya damƙo hannun batul Ya rabata da ita, Yaje ya miƙa ma Giant, Sai ta ji tsanarshi Ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarta,
ÆŠauke eyes É—inta tayi daga kallon ceilling da take Yi, ta tsayar dasu akan fuskarshi, bakomai take gani ba acikin idanuwanshi face tsantsar nadama.
Sun ɗauki tsawon lokaci suna kallon juna batare da wani daga Cikin su Ya ƙyafta idanuwan shi ba, Kowa Da abunda zuciyarshi take raya mishi, ganin ta fara motsa la66anta alamar za ta yi magana, sai yaji sanyi acikin ranshi, yayi tsammanin zata yafe mishi ne, amma sai yaji tace"inaso ka yi mini alƙawari..." a ƙagare yake kallonta cike da son jin wani alƙawari ne takeso Ya ɗaukar mata, Don a shirye yake daya bi umarninta.
Muryarta adisashe taci gaba da cewa"idan ka yi mini wannan alƙawarin zanyi farin Ciki, kuma zan tabbatar da cewa Kai ɗin mai ƙaunata ne," aɗan ruɗe yake kallonta, shi dai fatan shi Kada tasa yayi mata alƙawarin da ba zai Iya cika mata shi ba.
Calmly ya furta"Ki faɗa mini menene kike son in ɗaukar miki alƙawari akanshi? Girgixa kai ta ɗanyi, Still hawaye na bin kuncin tace"Ka fara ɗaukar alƙawarin kafin na faɗa maka akan menene"
Hawaye wasu nabin wasu akan fuskarshi Yace"I can't, saboda nasan ba alkhairi xaki faɗa mini ba," Saukowa yai daga saman gadonta, Ya zuƙunna saman gwiwowinsa, a ƙoƙarinsa naya nemi yafiyarta, don shi har ga Allah baison tayi fushi dashi, Yana matuƙar Jin ƙaunar angel acikin zuciyarshi,
"Nasan idan nace ka dawo mini da batool bazaka Iya ba, Haka zalika idan nace Ka faɗa mini wanene kai? Still amsa ɗaya zaka bani shi ne baka sani ba, kaga kuwa baka da amfanin da zaka Iya mini...." bai bari ta karasa maganar ba, yai saurin katse mata hanzarinta da cewa"I know bani da amfani awurinki, amma ki tuna abunda ya faru jiya, may be kin manta, ni ne naje na ceci rayuwarki, na faɗa miki ne badan Ina tunƙaho da hakan ba, sai dan kisan cewa ni ɗin mai ƙaunarki ne kuma ina da amfani awurinki," awahalce yai maganar, daga shi har ita babu mai ƙoshin lafiya acikinsu, Daƙyar suke magana kamar anyi musu dole, kayan jikinsu ba ƙaramin tsami suke yi ba, hada ƙarnin jininta da yai bleeding jiya,
Fuskarta a yamutse tace"danish, ban damu da duk wani abu da zaka faɗa mini ba, alƙawarin da nake so ka ɗaukar mini shi ne, Ka nesanta kan ka dani! Ras! Yaji gabanshi ya faɗi, tun kafin ma yaji ƙarshen xancen nata, Ya soma girgiza kai alamar bazai Iya ba,
"Bana son ka ƙara kusanto ni, balle ma har kayi tunanin zuwa wurina, koda gigin wasa kada ka kuskura ka bari mu haɗa ido da juna, ya zamar maka dole ka janye jikinka daga nawa, idan har kana son zaman lafiya acikin kurkukun nan......."
Bawan Allah ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi, ya riga dayasan Halinta, tana da wuyar sha'ani, ga kafiya idan ta furta magana zai yi wuya ta canza ta, duk da wani lokacin tana da saurin sauka idan tayi fushi sai dai wannan karan babu sassauci akan fuskarta,
"Har tsawon wani lokaci kike so in janye jikina daga naki"? Idanuwanshi cike tab da kwalla yayi mata maganar,"
"Har zuwa lokacin da za'a dawo da batool, Idan tace ta yafe maka shikenan nima zan yafe maka mu cigaba da yin rayuwar mu kamar yarda muka saba, idan kuma har ba'a dawo da ita ba, hmmmmm....." ta ambaci hakan saboda tagaza idasa maganar, sai faman taunar la66anta take yi, har sun ɗan ƙara fashewa dama abushe suke.
Ba ta yi tsammanin zai ɗaukar mata alƙawarin ba, sai ji tayi yace"I promised u angel, bazan sake koda kallon ki ba, ballantana har inyi miki magana, Inaso in tabbatar maki da cewa ni mai ƙaunarki ne, Kuma inason farin Cikin ki,......." dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana bin fuskarta da kallo, tun yanzu ya fara jin kewarta a tare da shi, wahalallan murmushi ya sakar mata har dimples ɗinshi suka lotsa sosai, da sauri ta kawar da fuskarta gefe ɗaya, saboda wani irin shock da taji, Kyanshi na ƙoƙarin jan hankalinta, idan har taci gaba da kallonshi zata fara danasanin janye jiki dashi,
"Angel zan tafi, Amma kafin nan, ina neman alfarma a wurinki, ina fata zaki yi mini abunda nakeso a ƙaro na karshe, Muryarta ƙasa ƙasa tace"menene"?
"Ki kula mini da kanki, sannan an kawo mana breakfast ɗin mu, kada damuwa ta sanya ki gaza cin abinci nasan kina jin yunwa, ki samu wanda zai taimaka miki acikinsu wurin yin tafiya saboda ƙafafuwanki sun raunata sosai, ba zaki Iya taka su ba, bayan haka Jiya na same ki acikin mawuyacin hali kina ambaton sunan daddynki, zai iya yiyuwa kinyi ƴan gane gane da suka shafi mahaifinki, wanda ba gaskiya bane, inaso ki kwantar da hankalin ki, akan wannan, after that, akwai taimakon da zan Iya yi maki, ta yadda zaki gane cewa, mahaifinki da batool awani hali suke ciki, idan har kin amince mini zan nuna maki," wani irin kallo angel take binshi dashi na rainin wayau, sai kace wani malamin duba, da alama yana ƙoƙarin yi mata wasa da hankaline,
"Nasan zaiyi wuya ki yarda dani, but pls Ki bani dama"muryarshi ce ta katse mata zancen zucinta da take Yi, shiru ta É—anyi tana was wasin kalaman shi acikin zuciyarta, kafin ta É—an yamutsa fuska tace"its ok, ka nuna mini ta wace hanya zan iya gane a wani hali suke Ciki,"
Ba ƙaramin daɗi yaji ba, da sauri ya Juya mata bayan shi tare da cewa"Ki hau in goya ki," fuskarta a ɗaure tace"Ina zaka kaini"? Ya bata amsa da cewa"Cikin toilet ɗin mu," ba don taso ba, ta yunƙura daƙyar ta miƙe xaune tana faman cizon la66anta, ta sanya hannayenta biyu ta ruƙoshi, Ta hau saman bayan shi, ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu ɗauke da ita a bayan shi, Sam bata lura da sabbin gadajen da aka kawo musu acikin ɗakinsu ba, Saboda ta lumshe idanuwanta, yayin da yake wucewa da ita cikin toilet ɗin, Bayan ya shiga cikin makewayin nasu, wanda keda glass window ɗin nan, Yayi mamakin ganin Kayan amfanin da aka zuba musu sababbi acikin toilet ɗin su, An gyara shi tsaf komai a tsaftace, An ajiye musu trash can mai girma, Daga can sama Jikin bango inda cabinet dinsu Yake, Care product ne a jere tun daga kan hair gel, shower gel, conditioner, komai ma aka tarkata musu hada Toothbrushes da aka ajiye musu acikin holder dinsu, tare da toothpaste, Kuma kowani product yana ɗauke da sunan kurkukun ƙaddara, hakan na nufin ma'aikatan Prison ɗinne suka haɗa su, Ya yi farin Cikin ganin sabbin kayan amfanin da aka sanya musu acikin toilet, ta wani 6angaren kuma sam Bai ji sun kwanta mishi a ranshi ba, tun da ba dawwama zasu yi cikin farin ba,
Jin yaƙi cigaba da tafiya yasa ta ɗan ɗago da kanta daga saman kafaɗar shi, Ta cunkuli fatar cikinshi da hannunta, Har saida ya ɗan ciji la66ansa saboda zafin daya ji, Muryarta a kausasace tace"Idan ba zaka nuna mini ba, ka sauke ni in koma ɗaki," Muryarshi a sanyaye ya furta mata am sorry, Taja tsoki, tafiya yaci gaba da yi cikin toilet ɗin ya nufi ƙatuwar tukunyar fulawar nan dake a killace Jikin bango, Anan ya ɗan zuƙunna ya sauke Angel, ta xauna a ƙasa tana faman lumshe idanuwanta, ta ko'ina raɗaɗi take ji ajikinta, sai lokacin ta lura da sabbin kayan dake a cikin toilet dinsu, da mamaki akan fuskarta take binsu da kallon ƙurulla, Sai ta dinga gani kamar ba gaskiya idanuwanta suke nuna mata ba,