← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 179

Sashe 144

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu yasa ya share hawayen dake akan fuskarshi, Idonshi akan na haris yace"ina ƙara baku haƙuri, idan ma hakan bai yi maku ba, zan duƙa saman gwiwowina in roƙe ku akan ku yafe min, kai idon ma kuna so ku cire min idona ne don ku huce takaicin abunda nayi maku to gasunan, ku yi abinda ku ka ga dama, amma karkuce zaku raba ni da azeeza, saboda tana bani kulawa, ina jinta tamkar ƴar uwata Gabriella,"

Yana kawo nan a maganarshi, Ya zube saman gwiwowinsa, Da sauri azeeza ta miƙe tana roƙonshi akan ya tashi tsaye ya daina zubar da hawayen shi.

"Kada ka damu, komai ya wuce awurina, koda ace su basu yafe maka ba ni na yafe maka" acewar Hannah. Tana rufe baki parveen ce"tunda dai ya riga ya faru, bamu isa mu canza komai ba, don haka nima na yafe maka" Ɗaya bayan ɗaya suka dinga cewa sun yafe mashi, Mutun ukune basu tanka mashi ba, Haris da deeja da kuma Naufal, Su sunce sai an dawo musu da ɗan uwansu sun ga awani hali yake ciki tukunna zasu Yafe mashi, a ƙalla ya ji sanyi aranshi ganin dayawan su sun yafe mishi sunce zasu cigaba dayi mashi magana bazasu ƙara nuna mashi wariya ba, Yaji dadin hakan ga kuma Azeezar shi mai sanya shi farin ciki, itama tana Atare da shi, bayan komai Ya lafa, Gabriel Ya miƙe ya nufi sashen toitet ɗinsu, don yayi wanka,

ƙarasa shigowa cikin ɗakin parveen ta yi hannunta ruƙe da na majnun don tun ɗazu tana a tsaye tana sauraronsu Gabriel ganin sun samu maslaha atsakanin su yasa ta motsa, sai da ta fara wurga pillown hannunta saman gado tukunna ta nufi jamima da ke a tsaye gefen gadon Angel ta damƙo hannunta, ta haɗa su duka biyun takaisu gaban Gadon azeeza a lokacin harta koma ta zauna.

"Ku bata hakuri idan ba so kuke ranku ya 6aci ba," acewar parveen, ÆŠagowa su kai suna kallon fuskar azeeza da tayi jawur.

"Idan har baku bata haƙuri ba, Yau babu wanda zan bari yaci abinci acikin ku, kunsan dai halina tau," jin haka yasa suka haɗa baki wurin furta"We're really sorry sister azeeza ba zamu ƙara ba"

hada kama kunnansu kamar zomaye, hakan da su ka yi ba ƙaramin dariya yabata ba, Miƙa ma Jamima hannu tayi"muje inyi maki wankan tun da mun shirya" Ba musu ta amsa mata da toh, Saukowa azeeza tayi daga smaan gadon ta ruƙe hannun Jamima acikin nata, suka nufi toilet, Bayan shigarsu, Parveen ta koma saman gadonta tana yi musu sambatun yunwa take ji, majnun kuma ya nufi tsakar ɗakin su Yanata Yin ƴan tsalle tsallen shi.

Ɗakin yai tsit na ɗan wani lokaci, Fitowa daga cikin sashen toilet dinsu Gabriel yai su azeeza na a biye da bayanshi ita da jamima da ta yi ma wanka, Sai murmushi suke saki Shigowasu yayi dai dai da turo ƙopar ɗakin su da aka yi, Gaba ɗaya hankulan su suka koma akan benan, Banda Angel data mannewa pillow, ta kammala shan kukan nata, ta lallashinta kanta ta yi shiru, Ajiyar zuciya suka sauke ganin Giants ne masu kawo musu abinci, Hannayensu ruƙe da Wooden trays kamar yadda aka saba, A jere suka nufi ɗakin bayan sun ajiye su saman carpet, suka ja da baya tare da ƙamewa,

"Abinci ya iso, wanda bai wanko bakinshi ba, yai sauri yaje toilet muna jiran ku" Hannah ce tai musu magana, su ka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya su ka dinga miƙewa suna shiga sashen toilet ɗinsu, within minutes kowannansu ya dawo suka zauna saman carpet domin cin abinci, ganin taƙi tasowa tazo suci yasa Deeja ɗaga murya ta ƙwala mata kira"Angel Ki taso muci abinci" shiru bata tanka mata ba, haris ma yai magana amma shiru taƙi tasowa, naufal yace su ƙyale ta, inyaso sun ajiye mata nata acikin kwando,

Har sun yi nisa da fara cin abincin, kowa ya natsu yana ci, Majnun sai cusawa ya ke yi abankinshi Parveen nata jifar shi da harara ganin yadda yake yin cin mugunta.

Babu wanda ya lura da ita, Saukowa tai daga saman gadonta fuskarnan sharkaf da hawaye ta yi jawur da ita, tafiya take yi kamar zata kife ƙasa saboda rashin kuzarinta, bata nufi ko'ina ba sai wurin Giants dake a tsaye kamar dakarun Yaƙi.

Dab dasu ta tsaya kamar zata faɗa musu, fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin, zuciyarta a bushe take, muryarta a sanyaye ta soma yi musu magana

"Bawani abu ya kawo ni wurinku ba, so nake ku faɗamin, yaushe zaku dawo mana da ƴan uwanmu? Batool shiru har yau, Danish kuma bansan awani hali yake ciki ba, ni dai don Allah na roƙe ku, ku taimaka ku faɗamin awani hali suke ciki, shin suna raye ko sun mutu ne, idan naji sai in haƙuri in fidda rai......" tun da Angel ta soma yi musu magana Hawaye nabin fuskarta, gaba ɗaya muryarta ta janyo hankalin su Mubeen akanta, tuni sun dakata da cin abincin suna kallonta, an rasa me buɗe baki ya dakatar da ita.

Girgiza kai ta yi tare da lashe hawayen daya gangaro saman la66anta da harshenta, kafin taci gaba da cewa"wai ku ba zaku ta6a aikata abun kirkiki ba arayuwarku? Haka zaku ƙare wurin aikata zalunci......." muryar Haris ce ta katse mata maganarta

"Angel, pls ki matsa daga wurinsu! Kodan saboda mu, idan wani abu ya same ki mu zata shafa, mun rasa mutun uku acikin mu yanzu idan kema wani abu ya faru da ke ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance'? Fashewa tayi da matsanancin kuka, azeeza tuni ta kama yin kukan itama.

Cikin shessheƙar kuka Angel tace mashi"don bakasan yadda nake ji acikin zuciyata bane, ni ƙwara ma su kashe shi in huta, da irin wannan rayuwar mara amfani....." daƙyar ta ƙarasa maganar saboda wani irin jiri da ta soma gani acikin idanuwanta, ƙirjinta yai mata nauyi tamkar zai dare biyu, hannu ɗaya tasa ta dafe kanta, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Gabriel saurin miƙewa shi da yake a zaune ƙarshen carpet din dab da inda suke hannu biyu yasa wurin tarbeta, Ya ɗauke ta Ya nufi Gadonta, a sama ya kwantar da ita, hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, abincin ma ya fita aransu, duk suka miƙe da sauri suka nufi Gadonta don ganin meke faruwa da ita, Mutun biyu suka rage kan abincin, majnun da Jamima, kallon juna su ka yi kowannansu ya cunkusa abinci abakinshi, Suna tauna suna magana

"Ki ɗauko kwandon batul mu ɗibar masu abincin kada waɗannan dodonnin su tafi dashi," Majnun ne yai mata magana, harara ta wurga mashi"Kai bazaka je ka ɗauko ba, saini," ƙarasa cinye abincin bakinsa yai tare da yunƙurawa ya miƙe ya nufi gadon batul hada ɗan gudunsa, Ya zuƙunna a gaban ƙarƙashin gadon ya zaro kwandon da sauri ya dawo ya zuƙunna kamar mutumin kirki, Ya dinga kwasar abincin Yana zubawa ciki komai Ya haɗe musu kusan Duka ya kwasar musu har saida kwandon yai soro, ya ɗago ya kalli Jamima dake ta tura plaintain chips abakinta.

"Tun da ni na ɗauko kwandon, Ke zaki maida yanzu" ta6e baki tayi"ae bani da ƙarfin iya ɗaukarshi, faɗuwa zanyi ƙasa, kai ka ɗauka mana" Girgiza kai majnun yai kamar babban mutun Yasa hannu ya ɗauki kwandon, Ya nufi ƙarƙashin gadon Ya tura shi ciki, yana ƙoƙarin miƙewa Yaji muryarta abayanshi"Gashi na ɗauko" kallonta yai, Robobin ruwa ne ta rungumo guda uku a ƙirjinta, sai yatsina fuska take yi, Hannu yasa ya kar6a Ya tura a ƙarƙashin gadon, yace mata ta kwaso sauran, Ta koma ta daukosu, Ta miƙa mashi ya kar6a ya ajiye musu, babu wanda Ya tuna da abinci ba su san ma sun ajiye musu ba, Hankalinsu gaba ɗaya yana akan Angel sun kewaye gadonta damuwa ce danƙare akan fuskokinsu, sai kiran sunanta suke yi tare da jijjiga jikinta don ta farka amma taƙi motsawa, hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankalin yai ba,

"Angel! Pls ki tashi! Dan Allah ki farka!' azeeza ce keta magana tana matsar kwalla, Deeja tace"Allah yasa ba waÉ—ancan mugayen bane su ka yi mata wani abu ba," haris yace"nima abunda na ke hasashe kenan"

muryar Gabriel ce ta janyo hankalinsu akan shi" Ba abunda ya same ta, Yunwa ce take ji, ku miƙo min ruwa" yatsina fuska Naufal yai"kawai saboda tana jin yunwa saita yanke jiki ta faɗi? A ina ka sami wannan ilmin" Banza Gabriel yae dashi bai tanka mashi ba, Haris yace"Shisshigi ne kawai," Dogon tsoki Gabriel yaja tare da kallon Azeeza da ke ta yin kuka yace ta ɗabo mashi ruwa, Kafin tayi yunƙurin zuwa ɗebowa Sai ga majnun bakin gadon hannun shi ruƙe da bottle water yaji suna nema shine ya kawo musu, karo nafarko kenan da majnun ya ta6a yi musu abun kirki.

Ba tare da 6ata lokaci ba, Gabriel ya kar6i robar ruwan, ya samu wuri daga gefen gadonta ya zauna tare da sanya hannun shi ɗaya ya ɗago da kanta ya ɗaura shi gefen chest dinshi, azeeza ce ta buɗe mashi murfin robar hannun shi ta ruƙe a hannunta, Ya kanga ma Angel robar abakin ta, Duk suka baza ido suna jiran ganin in zata motsawa, aiko kamar jira take taji an daura mata robar ruwan abakinta, ta dinga kur6arshi kamar zata shaƙe maƙoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!

Saboda tsabar kunyar da ta kama su haris da Naufal Sai gashi sun sadda kansu Ƙasa, Kusan rabin ruwan ta shanye, wani irin yunƙurin amai ne yazo mata, saboda rashin ƙwarin jikinta bazata iya miƙewa taje toilet ba, asaman rigar Gabriel ta shiga kwara aman, tsananin tausayinta duk ya kamasu sai sannu suke yi mata, kamar zasu ɗauke mata ciwon haka su ke ji, duk da irin aman da ta ke yi ajikinshi bai ji komai ba, ko irin ƙyanƙyamin nan, saima ƙara ruƙe ta da ya ke yi da hannayenbshi don tuni ya miƙa ma Azeeza robar ruwan, bakomai ke fita acikin bakin nata ba face kayan marmarin data sha tun jiya da zallar ruwa, Sai nishi take yi tana faman lumshe idanuwanta.
Chapter 144 · 0% Book details