← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 179

Sashe 146

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yunƙurin buɗe baki deeja ta yi, sai dai bata kai ga furta abunda take son faɗi ba, idanuwan su, su ka sauka akan Angel da ta soma motsi tana banƙarewa, yatsun hannayenta nata kerma, wani irin gurnani take fitarwa da huci, Nan take maganar tsohuwa zafreen ta faɗo musu aransu, wani irin mugun tsoro ne Ya kamasu, la66an Deeja na kerma tace dasu"ku tashi mu 6oye in ba haka ba, Angel zata iya cutar damu......"

kafin wani daga cikin su ya kuma furta wata kalma, Angel ta duro daga saman gadonta Yadda kasan gardin ƙato, facial muscles ɗinta har kerma su ke yi, launin ƙwayar idanuwanta sun 6ace 6at sai farin, Har wani gyara wuyanta ta ke yi, tana banƙare ƙirjinta da bayanta, gadan gadan ta nufo gadajen su, aiko jiki na 6ari Suka soma ƙoƙarin saukowa don su nemi wurin 6uya, Kamar walƙiya deeja taga Angel agabanta, Damƙar wuyanta tai tare da wujijjiga ta, kafin ta ɗaga ta da hannu ɗaya ta buga ta ga ƙasa, nan take deeja ta suma, ganin hakan yasa hankalin sauran yai matuƙar tashi, da gudu Parveen ta nufi sashen toilet ita da Hibba da Rubina da niyar su 6oye, kafin su kai ga ƙarasawa jikin ƙopar ta riga su isa, sai dai suka ganta agabansu, Hannu biyu tasa ta shaƙi wuyan Parveen dana hibba, Ta ɗaga su sama, suna ta kuka kamar ransu zai fita, Rubina na ƙoƙarin bi ta gefe ta shige, aiko ta sanya ƙafarta ɗaya ta taɗiyeta, kanta ya bugu da ƙasa jini harta hanci, Innallahi wa'inna ilaihirraji'un.

Basu ta6a ganin tashin hankali makamancin na yau ba, Angel bata ji bata gani, bugun mutuwa take nakaɗa musu, ko da ta ɗaga su pareen da hannayenta, A saman floor ta maka su, babu wanda hancinsa baiyi bleeding ba a cikinsu, saboda wani irin ƙarfine irin na dawakai, idan ta daki mutun dukkan sassan jikin shi ke amsawa.

Waro ido waje Hanna da sauran su ka yi, kowannan su Ya shiga ja da baya suna a jere tsakiyar ɗakin Jikin su nata kerma muryar su a tsananin tsorace suke roƙonta suna faɗin Dan Allah Angel kada ki kashe mu, ki tausaya mana halin da mu ke a ciki, laifin me muka yi maki? Yau ke da kanki kike neman halaka mu! Magana suke yi amma sam babu alamun tana jinsu, abunda basu sani na, A halin yanzu Angel ba ita ɗaya bace.

Ganin maƙiya ta ke yi musu, Burinta kawai ta kashe su har Lahira, shin ina labarin azeeza da jamima dake a la6e ƙarƙashin gado, kowannan su yasha jinin jikinshi, tsabar tsoro yahana su motsa, Sai da suka ji kukan su Hannah ya cika ɗakin, tukunna suka soma ƙoƙarin fitowa, cikin tashin Hankali yasmin da ta hango kan azeeza dana jamima dake shirin fitowa ta ƙarƙashin gado, ta dinga girgiza musu kai alamar karsu fito su koma, da hannu ta dinga yi masu alamar su koma ƙarƙashin gadon.

Ƙwaƙƙwarar damƙa Angel ta kai ma wuyan Eve da Yasmin, ta juyar dasu su ka fuskanci bango, ta daddage ta buga kansu jikin sa, tuni jininsu ya wanke jikin bangon a ƙasa suka sulale kowannan su ba numfashi, Mayar da idanuwanta ta yi akan Sarah da Hanna da suka rage, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, Zufa ta ko'ina ta shiga tsastsafo musu, sai kuka su ke yi haɗi da yi mata magiya, Sai kewaye cikin ɗakin su ke yi, Ganin da gaske fa ba ƙyale su zata yi ba, hakan yasa Sarah ta watsa da gudu zata shige sashen toilet ɗinsu, sai dai kafin ta ƙarasa, Taji an damƙi ƙafafuwanta ruƙo bana wasa ba, Gaba ɗaya ta kife saman floor Kanta ya daku, ƙugun ta ya bada wani irin sauti ruƙuƙus.

Hanna ce ta yi saura a tsakiyar ɗakin, tsautsayi ya fiddo da jamimah, Karaf akan idon Hanna tana ƙoƙarin buɗe baki tace mata ta koma ƙarƙashin gadon, kwatsam Angel ta nufo wurin Jamima, tana tafiya tamkar damusa har wani gyara wuyanta take yi, tana lashe baki, da gudun gaske Hanna ta ɗauke jamima ajikinta ta ƙanƙame ta tana faɗin

"Dan Allah kada ki yi mata komai, Kin ga ita ƙarama ce na roƙe ki, idan ma bugun ne ki haɗa da nata ki yi mini, amma ki ƙyale jamima, zata iya rasa ranta....." kafin ta ƙarasa maganar, Angel ta ware hannayenta biyu ta yi masu ƙwaƙƙwaran ruƙo, da hannar da jamimar da ta rungume a jikinta, Dukkan su ta haɗa, ta cuccu6esu ta daddage ta maka su ga saman floor, nan hake haƙorin jamima ɗaya ya 6allo daga bakinta jaga jaga da jini, har saman kumatunta, kuka tamkar ranta zai fita, tuni ta saki fitsari ta cikin wandonta saboda tsabar raɗaɗin da ta ji.

Hannah da ke ruƙe da ita tuni ta sume, kunnuwanta ne suka dinga motsi suna jiyo mata shessheƙar kukan mutun, nan fa ta shiga neman wanene, Gadajen ta dinga bi tana ɗaɗɗaga su har Allah Ya kawo ta kan gadon da azeeza ta 6oye, Tana ɗaga gadon idanuwanta suka sauka akan azeeza da ke ta yin kerma ta ƙanƙame jikinta, sam ta kasa ɗagowa ta yi tozali da fuskar Angel.

Gyara wuyan ta ta yi kamar yana yi mata ƙaiƙayi har wani sauti ya bada muƙus, A tsananin tsorace Azeeza ta soma yin rarrafe don ta gudu daga wurin, aiko ta daddage ta ɗaura ƙafarta ɗaya saman yatsun hannun azeeza ta ta ke su ta murje duk suka faffashe, jini ya soma tsastsafowa, a nan ƙasa ta baje a sume, wata irin mahaukaciyar dariya Angel ta fashe da ita.

Sautin kukan jamimah daya karaɗe cikin ɗakin nasu ne ya janyo hankalin Angel kanta, ita kaɗai ce bata kai ga suma ba, Lashe baki ta yi tare da Nufar inda jamima take a kwance ƙasa cikin mawuyacin hali, Kafin ta ƙarasa gare ta ta ji an damƙi ƙafafuwanta, Sai dai wanda ya ruƙe ƙafafuwan nata, ya gaza Kifar da ita ƙasa saboda tsabar ƙarfinta.

A sukwane ta jiyo da kanta don taga wani isasshen ne Wannan mai ƙarfin halin, Karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar Deeja wadda hawaye suka wanke ta, muryarta cikin shessheƙar kuka ta ke faɗin Angel kin bamu mamaki yau ke da kan ki ki ke neman kashe mu, ashe dama ba ƙaunar mu ki ke yi ba, ban ta6a tunanin zaki iya raunata wani a cikin mu ba....."

Ɗaga ƙafarta ɗaya ta yi da niyar ta murje kan deeja da ƙarfi deeja ta ambaci"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! " shi kaɗai ne abunda ta iya furtawa la66anta na kerma.

tamkar an daki kanta da guduma, haka ta sanya hannayenta biyu ta daddafe kanta, wani irin jiri ta soma gani acikin idanuwanta, muryarta na rawa ta shiga ambaton

"La Hawla Wala Quwwata Illa Billah" Jikinta ne ya soma jijjiga, ta runtse idanuwanta saboda wata irin sarawa da kanta ke yi mata, Deeja nata kallonta, tangal tangal ta soma yi zata faɗi ƙasa.

Allah sarki duk da irin abunda ta yi musu hakan bai hana Deeja yunƙurawa ta miƙe tare da yin saurin tallabo Angel don kada ta faɗi ƙasa ta bugu, A hankali ta zaunar da ita, tare da zuƙunnawa gefenta, tana ambaton sunanta cikin sanyin murya ta wanda ya karaya"Angel, Allah yasa kin dawo hayyacin ki, Ni nasan ba yin kan ki bane" Tana magana hawaye nabin fuskarta, hannayenta tallabe da Angel, tsawon lokacin tun sautin kukan jamima na fita da ƙarfin shi har yakai ga disashewa, a ƙarshe ma ta sume, yanzu su biyu ne su ka rage a cikin ɗakin masu numfashi.

Muryarta ƙasa ƙasa ta soma magana"idan har dagaske ne abunda ya faru ba mafarki ba, Deeja ki kashe ni, kawai in mutu, meyasa na aikata ma ku hakan? Da hannayena nabi kowannanku da jahilin bugu, duk da irin haƙurin da ku ke bani amma naƙi sauraron ku, saboda rashin imani........'

girgiza kai deeja ta shiga yi tana faÉ—in

"ba laifin ki bane Angel, Ba yin kan ki bane, ko a mafarki bana tunanin zaki iya yi mana hakan balle kuma a zahiri......"

raba jikin ta ta yi daga na Deeja ta yunƙura ta miƙe jiki ba ƙwari take bin kowani 6angare na ɗakin su da kallo, bakomai ta ke gani acikin idanuwanta ba face jinin su, gasu nan a kwankwance kamar gawawwaki,

Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Lamarin ya yi matuƙar girgizata, kamar mahaukaciya haka ta shiga bin hannayenta da kallo, Acikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne da fargaba, lokaci ɗaya ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da gudun gaske ta nufi bangon ɗakin su, Deeja ta miƙe da hanzari tabi bayanta, Daddagewa ta yi ta dinga buga kanta jikin bango da niyar ta kashe kanta, bugu bana wasa ba, Goshinta da hancinta dukansu sai da suka faffashe, Zallar jininta jawur dashi ya dinga gangarowa ta saman goshinta yana wanke fuskarta, hatta la66anta bata bari ba, cizonsu ta dinga yi da haƙoranta duk ta gurgujesu, jini ya dinga tsargowa, duk yadda Deeja taso ta janye Angel daga jikin bangon abun ya faskara, Saboda bata acikin hayyacinta, takai maƙura, idanuwanta sun makance kunnuwanta basu ji, mutuwa kawai take son ta yi awannan lokacin, ta tsani kanta, tsana mara misaltuwa, zuciyarta tagama hasala.

Cikin muryar kuka Deeja ke roƙonta tana faɗin ta yi hakuri tadaina cutar da kanta, saboda ba yin kanta bane abunda ya faru, tace Angel ki tsaya in yi maki bayanin abunda ya faru, kada ki kashe kan ki don Allah, idan ki ka mutu kika barni ya ki ke so inyi da raina, mu kaɗai fa muka rage da zamu iya taimakon ƴan uwan mu da su ke acikin mawuyacin hali, Ki tausayamin Angel, wayyo Allahna, Ya Allah ka kawo mana ɗauki, wannan wata irin masiface! Zubewa ta yi a saman gwiwowinta, ta ci gaba da kuka hannunta dafe da goshinta.
Chapter 146 · 0% Book details