Sashe 84
Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yana aciki kwance saman gado yana bacci, Yazo yana kuka ya faɗa min wai kin ce zaki 6alla mashi mota, Daƙyar na samu na lallashe ya daina kuka ya kwanta," dariya aneelerh tasaki tare da cewa"Ya takura mun ne mami, ina tsaka da yin bacci na ya daddage ya danna jiniyar motar, baki ga yarda na zabura ba, Ni nayi tunanin ƴan sanda ne suka zo ashe shine" Dariya mami tayi tana girgiza kai tace"Allah ya shirya min jikana, " aneelerh ta amsa da amin, kafin Ta juya ta nufi falo, Agaban dining ta hango ana tana jera kayan breakfast ɗinsu, Ƙarasawa tayi inda take atsaye ta miƙa mata wayar tare da yi mata godiya, don ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease tasan benazir tana araye, Idan Allah yasa suna da tsawaicin kwana wata rana Allah zai haɗa su ne, ta wani 6angaren kuma Abun ya tsaya mata acikin zuciyarta, Irin yadda taga benazir a hoton hankalinta kwance babu wata damuwa akan fuskarta,
Yinin ranar da tunanin benazir tayi shi, Da rana ne Abie Ya dawo daga wurin aikinshi, Yazo musu da babban albishir Na ƙara mashi matsayi da akayi zasu koma Abuja da zama, mami tayi farin ciki, aneelerh kuwa sam bataso haka ba, Ita fa duk wani abu da zai rabata da jos ba son shi take Yi ba, gani take kamar idan ta ɗaga ƙafa tabar garin shikenan ba zata ƙara ganin mutanan nan ukun da ta rasa ba, waɗanda a koda yaushe take Addu'ar Allah ya Bayyanar mata dasu, babu yarda ta iya yanzu dole tabi iyayenta don bata son rabuwa dasu, tafi so duk Inda zasu je ƙafarta ƙafarsu,
*Back To prison*
Ƙwaƙƙwaran Juyi angel tayi da niyar ta gyara kwanciyarta, sai ji tayi an tokare bayanta, A matuƙar ruɗe ta juyo tana kallonshi, waro ido waje tayi ganin danish saman gadonta, Aikuwa rai a6ace ta sanya ƙafarta da ƙarfi ta ture shi gaba ɗaya ya gangara ƙasa Kanshi Ya bugu sosai har saida yafirta"ash!!" saboda zafin da ya ji, Zazzaga mashi masifa ta soma Yi ta inda ta shiga bata nan take fita ba, sautin muryarta ya karaɗe Kunnuwan masu bacci ɗaya bayan ɗaya su batool suka dinga farkawa Suna tambayar lafiya me ya faru?
Nuna danish ta yi da yatsan Hannunta tace"wlh kaɗan ka gani, Idan har baka fita sabgata ba, Ina mace kana namiji Ka kwana a gadona, Salon kawai kaja mini zunibi," Tun da ta fara Yi mashi faɗa, bai motsa daga kwancen da yake a ƙasa ba, ya dafe gefen goshin shi da hannu, Yaji zafin buguwar da kanshi yayi,
Saukowa su batool su Ka yi daga saman beds É—insu, fuskokinsu duk A yamutse idanuwansu sun kumbura sakamakon kukan da suka sha Jiya da za'a tafi da deeja,
Abakin gadon angel suka tsaya suna kallonsu ita da danish, Ta rufe ido sai faɗa take mashi hada pillow ta jefe mashi saman fuska, Ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, shouting ɗin da take yi mashi ba ƙaramin gigita shi yake yi, daurewa kawai yake yi,
"Pls angel, Ki yi haƙuri Ki ƙyale shi hakanan, kodan saboda lallurarshi ta rashin son hayaniya zai iya rikicewa, Hanna ce tayi maganar, angel ta watsa hannu tare da cewa"Idan ya tashi ya haukace ƙarewa ma, wlh ko ajikina, tun farko saida naja mashi kunne akan ya ni santa kanshi dani amma yaƙiya, saboda head fish ne dashi"
Girgiza kai batool ta ɗanyi idonta akan angel tace"Sister badan halina ba, Pls Ki bar maganar nan, Ki barshi yaji da kanshi, Nasan kina fushi dashi ne saboda abunda ya faru jiya, Ki yi haƙuri ki manta komai, kuma ki daina fushi dashi saboda Baya ƙaunar yaga ana share shi, Yana shiga damuwa" daƙyar batool takarasa maganar ganin irin kallon da angel ke jefa mata,
Gyaɗa kai tayi tare da jinjina kai tace"Shikenan zan ƙyale shi amma babu ruwanshi dani! Ni kawai bana son Yana kallona ko Yana yi mini magana, " Tana kammala maganar ta sauko daga saman gadonta ta bi ta gefensu Ta shige toilet,
Zuƙunnawa batool tayi agaban Danish Ta ruƙo hannunshi acikin nata, Ba ƙaramin tausayin shi taji ba, ganin sahun marin da angel tayi mashi asaman fuskarshi har yau bai disashe ba,
Cikin sanyin murya tace"Am sorry danish, Kamar yarda tace ka ƙyale ta, to ka rabu da ita har zuwa time da zata huce, if not zata cigaba da Ƙyararka ne, Nasan zata dawo da kanta ne ta nemi yi maka magana," sai lokacin ya samu ya miƙe zaune, ya jingina bayanshi jikin bango, ɗaya bayan ɗaya ya shiga binsu azeeza dake atsaye da kallo, matan ne gaba ɗayansu, Sai daga bisani Haris da su naufal Suka Sauko daga saman gadajensu, A inda yake zaune suka tsaya cirko cirko suna kallon shi,
"Kuma fushi ku ke yi da ni? Kamar yadda take fushi dani"? Yayi masu tambayar idonshi akansu, atare suka haÉ—a baki wurin cewa a'a, Kallon haris yayi tunkafin yayi mashi magana haris yai saurin cewa"am not angry with u, kaima ka sani bazan iya fushi dakai ba, just banji daÉ—in abunda ya faru ba jiya, amma komai ya riga daya wuce" jinjina kai danish yayi kafin ya kuma cewa"komi nake yi ina yi ne saboda ku, amma nasan zaiyi wuya ku fahimci hakan, sai nan gaba"
Naufal yace"Pls danish, mu komai ya wuce awurinmu, abunda ya faru ya riga daya faru ba wanda ya isa ya dawo dashi baya, so pls mu manta kawai, baida amfani tuna baya," Danish yace"idan ku kun fahimce ni, ita taƙi ta fahimce ni, tun daren jiya nake bata hakuri amma taƙi ta saurare ni," sai lokacin suka gane inda damuwarshi ta dosa, dama shi haka yake sam baya son wani yana fushi dashi tun fil azal, gaba ɗaya yake rasa sukuni,
"Danish kada ka damu kanka, In dai angel ce Zata kula ka, Ae bata iya fushi ba, tana da saurin hawa da kuma saurin sauka," acewar javed,
Ta6e baki yai tare da cewa"Its okey, ngde da kulawarku agare ni, " daga haka Ya miƙe jiki ba ƙwari Ya Nufi toilet, domin yin wanka,
Kafin Giants su kawo musu Breakfast ɗinsu, Sai da kowannan su Ya yi wanka, Basu jima da hallara A cikin ɗakin nasu ba, Sai ga Giants ɗin sun shigo ɗauke da kayan abincinsu, bayan sun ajiye musu saman dining carpet, duk suka zazzauna kewaye da farantan, Yau farfesun naman kaza aka kawo musu da zafinshi hada tiriri Yaji kayan ƙamshi, ga kuma dambun nama da aka haɗo musu dashi, sai Kayan marmari kamar kullum da kuma soft drinks, Abun na ɗaurewa angel kai, ganin irin badagon da ake yi da nama agidan kurkukun, sam bata yarda da irin wannan Lafiyayyar cimar da ake kawo musu ba, kullum basu da abinci sai nama kala kala! Na kaza na shanu na rago, wani naman ma batasan na wace dabbar bane, tana yawan tambayar kanta ko su wanene ke girka abincin kurkukun daga gani ƙwararru ne a 6angaren catering, sun iya sarrafa abinci, wani naman saboda tsabar dahuwar shi kana jefa shi abaki tunkafin ka taune da haƙori zai dagargaje da kanshi, ita dai fargabarta kada ace abincin da ake basu su naci, da ransu za'a fanshe, duk in zuciyarta ta saƙa mata hakan sai taji gabanta ya faɗi rasss! Don kuwa ko gwamnati bata aikin banza, balle kuma mutanan da Ba Allah ne aransu ba, Sunsan dalilin dayasa suke basu lafiyayyan abinci wata'ƙil kodan suna amfani dasu ne, Allah wa'alamu
kafin su fara Shan farfesun saida ta tunasar dasu akan su yi bismilla, Kullum ne sai ta tuna musu, hatta haris yau da tace su yi bismillah sai da yayi duk da bai musulunta ba, danish ne kawai baiyi ba, Ta lura dashi duk wani abu daya ƙunshi sunan Allah aciki bai furta shi, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, Har suka kammala cin abinci, da zarar sun haɗa ido dashi sai ta dinga jefa mashi harara, duk yabi ya tsargu ya hana zuciyarshi sakat, farfesun ma ba'a cikin kwanciyar hankali yasha shi ba,
Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan Suka fuce daga Cikin É—akin,
Ganin suna yunkurin zuwa saman gado su kwanta ne, yasa angel ta dakatar dasu, tace su motsa jikinsu, Idan sun kammala su watsa ruwa ajikinsu, Sannan Sun kwanta su huta, babu musu suka amsa mata da toh, banda danish da haris, tuni sun haye saman gadajensu, Shi haris damuwar rashin deeja ne yasa shi ƙin ta6uka komai, tunanin abunda ya faru daren jiya kafin atafi da ita ya tsaya mashi arai, Yaji tausayinta sosai, su kansu sauran ƴan uwan nasu sun damu da deeja, Ba yadda zasu yi ne shiyasa suka barma Allah komai,
A tsakiyar ɗakin suka Jera layi suna yin exercise, kamar wasan ƴar tseral haka suka dinga zubawa da gudu idan suka kai ƙarshen bango sai su dawo su sake komawa, Sai da suka tara uwar zufa ajikinsu tukunna kowa Ya nufi toilet domin watsa ruwa, Bayan sun fito ne, parveen ta matsa ma angel akan tayi mata irin kalabar da tayi ma su azeeza, Dama tun ranar da ta ganta ta kwallafa rai akan tana so itama, kafin marece yayi angel tayi ma parveen kalaba biyu akanta, ba ita kaɗai ba hada rubina tayi mawa, Bayan ta kammala musu kitson, Kowa Ya koma saman gadonshi ya zauna, Fira suka soma yi atsakaninsu acikin firar ne, suka tambaye ta, wai da tace musu wata rana zasu fita idan suka fita ina zasu je? Su da basu san komai na wajen kurkuku ba, murmushi tayi tare da cewa su kwantar da hankalinsu, Gaba ɗayansu zasu yi rayuwa agidan daddynta, Tace daddyna yana da gida, kuma gidanmu ɗaki Shida ne, Akwai palour ɗaya, dani da azeeza da batool zamu ware ɗaki ɗaya, Parveen da deeja da hanna zasu ware nasu ɗakin ɗaya, sai Eve da hibba da rubina suma zasu ɗauki ɗaya, nawa kenan? Suka ce mata Uku, tace toh, sauran ɗakunan guda uku, Javed da Naufal tare da Mubeen zasu ɗauki ɗaya, sai Haris shi da wancan Maji daɗin gadon suma zasu ɗauki ɗaki ɗaya," da ta ambaci maji daɗin gado hada harara ta wurga ma danish, ya lumshe idanuwanshi tamkar baiji me tace ba,