← Book details Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 179

Sashe 116

Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mu kuma fa"? kamar daga saman suka jiyo muryoyinsu Naufal, da sauri suka raba jikinsu daga Na juna, Su ukun nan ne, Mubeen da Javed, sai kallon su suke yi, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish Ware masu hannuwanshi yae alamar suzo suma ya rungumesu, aiko da sauri suka ƙarasa Ya haɗasu duka ajikinshi, Lamarin yayi matuƙar burgesu, Gwanin ban sha'awa, musamman yadda Danish Ya sake dasu Yana faɗa masu da ɗaɗan kalamai akan irin ƙaunar da yake yi masu abunda bai ta6a yi ba," Suna Cikin hakan suka Jiyo muryar azeeza da shagwa6a tana fadin"To mu fa? Baza a rungume mu ba," atare suka ɗago suna kallonta, ta ruƙe qugu abakin ƙopa, Haris yace"sarkin rigima, ki koma ciki, gamu nan zuwa, ɗaya bayan ɗaya sai Danish yabi ku ya rungume ku," Fuskarta ɗauke da murmushi ta watsa da gudu ta koma cikin ɗakin, tana faɗa masu parveen cewa Ga Danish nan xai zo ya rungumesu ajikin shi, Parvee tace har na ƙosa in shaƙi ƙamshin Jikin shi," kamar wata mayya,

Kusan atare suka shigo Cikin ɗakin, Haris yana a ruƙe da hannun Danish, ya zama tauraro Acikin taurari, A tsakiyar ɗakin suka tsaya, A lokacin angel ta koma gefen gadonta, har ta cire wrap coat dinta, ta ɗaurata saman mattress, ta ɗaure fuska babu walwala,

"Ka faÉ—a musu irin mahimmancin da suke dashi awurinka kamar yadda ka faÉ—a mana" acewar haris,

Natsuwa Danish yayi, A yayin da yake bin su da kallo sun jera layi kamar mabuƙatan dake jiran abasu sadaka, duk sun ƙagara su ji mai zaice, Bakowa yake son gani ba face ANGEL, ta wutsiyar idon shi ya hangota, saman gado sai hura hanci take yi, kamar Zakaran daya sha sigari,

"A yau inaso na faɗa maku, irin mahimmancin da kuke dashi awurina, You are more than just a friends saboda kun xarce hakan, Na ɗauke ku tamkar iskar da nake shaƙa, wurin yin numfashi domin in tsira, baku da banbanci da bugun zuciyata, Ina matuƙar ƙaunar ku, I luv you more than words can say bani da tamkarku a duniyar nan, i can even sacrifice my life for u guys" tunda ya soma jawabin nan, angel take ta satar kallon la66ansa, wani irin yanayi take ji mara misaltuwa, duk ta rasa sukuni,

"We're not only prisoners, we're life partners, bonded together by fate.
We were meant to be under the same roof, sharing a common destiny.
My hope is that one day we can be proud of each other, and Proud of the journey we've taken and the challenges we've overcome, we are more than just cellmates, we are family."

saboda tsabar daÉ—in kalaman shi da suke ji, har wani lumshe ido sukeyi, muryar tashi ce kamar ana busa sarewa gashi ya iya jawabi kamar jinin sarakai,

"Abubuwa da dama sun faru atsakaninmu, masu daɗi da marasa daɗi, dama shi haka zaman tare yake, sai ana haƙuri da juna, ni mai laifine amma still ina da damar da zan gyara kuskure na, duk da nasan akwai waɗanda suke yi min kallon mara amfani, inaso suyi mini uziri, nima bana so na dawwama ahaka, kodan saboda farin cikin ku, Zanyi ƙoƙari na gyara alaƙar dake atsakanina da kowannanku......." wannan magnar da Danish yayi tayi matuƙar karya musu zuciyoyinsu, musamman deeja da Angel, sunji wani irin acikin zuciyoyinsu,

"Aduk lokacin dana aikata ba dai dai ba, ku yi min uziri kada kuce zaku ƙaurace min, cos that's not the solution, kamata yae ku ja ni, ajikinku kamar yadda haris yake yi min shi kaɗai ne acikin ku yake faɗa min cewa nayi kuskure in gyara, kuma ina jin dadin hakan, Bayan shi mutun ɗaya ce nasan zata Sanya ni ahanyar dai dai, ko ban fada ba kunsan kowacece......." daƙyar ya ƙarasa maganar, saboda raunin da zuciyarshi tayi mashi, tunawa da ƴar uwarsu Batool, mai kyakkyawar zuciya,

"Duk da abunda nayi ma batool, Ni shaida ne akanta, idan yau ta dawo Cikin mu, bazata ta6a gudu na ba, zata fahimce ni, but why wasu suke ganin laifi na"? da sauri angel ta kifa kansa saman pillow, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, sosai ta ƙanƙame pillow ɗin, kalaman shi sun kashe mata jiki, yanayin yadda yake furta su, da alama abun yana hurting ɗinsa.

"Ƙaurace min bashi bane mafita, saboda muna son junanmu, zamu cutar da kanmu ne, gaba bata da amfani, amma in mu ka yi haƙuri da juna, wata rana xamu cimma nasara,"

tana ji aranta cewa waÉ—annan kalaman saboda ita yake furta su,

Bai ƙara cewa komai ba, tun da yakai ƙarshen maganarshi, Jiki na rawa azeeza da parveen suka nufe shi, atare suka faɗa jikinshi, suna kuka, Hannayenshi biyu ya sanya wurin rungumesu, Jiki asanyaye Deeja da su hanna suka matsa kusa dashi, Suma suka kwanta bayan Su parveen dake rungume ajikinshi, Tsabar farin Ciki ne yasa su haris suka ɗaga hannayensu suna tafa mashi, Hada su naufal da javed and mubeen, atare ƴan matan suka haɗa baki suna faɗin"We luv u so much our elder bro Danish, muna matuƙar ƙaunarka, munsan cewa ba za ka ta6a bari a cutar damu ba, da son ranka, sai don ba yadda xaka yi ne, mu ma mun gane kuskuren mu naƙin fahimtarka......" Sosai Danishi yaji daɗin kalamansu, hada yafiyarshi suka nema akan bugun da su kayi mashi lokacin da aka ɗauki Batool, Yace masu bakomai ya cancanci hakan ne, Ɗaya bayan ɗaya saida yabi kowaccensu, Ya rungumeta ajikin shi, Su parveen an samu abunda ake so, Har wani ƙanƙame shi take yi, kamar zata 6alla wuyanshi da hannayenta, har sai da haris yaja wuyan rigarta, ya janyeta daga jikin Danish Cikin zolaya yake faɗin"Halan Yayi maki kama da Tsokar nama ne? Shiyasa kike ƙoƙarin lashe jikin shi," Gaba ɗaya suka saki dariya, shima Danish ɗin murmushi ne akan fuskarshi, Mubeen ne ya lura da angel data kifa kanta saman pillow, ya ɗaga murya tare da cewa"Jama'a mun manta da Mai girma Angel" yayi maganar yana nunata da hannun shi, haris yace"yawwa ƙwara daka tuna min, Angel ki taso kema ki rungumi ɗan uwanki, kamar yadda kowa yayi, yau muna Cikin nishaɗi,"

da biyu haris yai maganar yasan basu shiri, banza ta yi dasu bata ce komai ba, Azeeza ta ruƙo hannun danish tana faɗin"Pls Muje wurinta ka rungume ta itama," janye hannun shi yai daga ruƙon da azeeza tayi mashi, Saboda ba zuwa zaiyi ba, A sharuɗɗan alƙawarin da suka ɗaukar ma juna, Zai nisance ta, da kuma gujewa haɗa ido, idan har yaje kusa da ita Alƙawarin xai karye,

Atare suka hada baki suna fadin Pls Danish Muje dan Allah, itama mu sanyata farin Ciki, " ganin yaƙi basu haɗin kai yasa suka koma wurin angel suna lallashinta akan ta taso suje itama ta rungumi ɗan uwanta, duk tana jin sautin muryoyinsu acikin kunnuwanta, sai magiya suke yi mata amma taƙi ɗagowa daga kan pillow, ransu ya 6aci, haris yace Tunda mun bisu ta arziƙi sun ƙiya, muyi amfani da ƙarfin mu"

Ya kai ƙarshen maganar yana nannaɗe hannun rigarshi, suma sauran suka nannaɗe nasu hannuwan rigunan, alamar xasu yi dambe, dama ɗabi'arsu ce, naɗe hannun riga, Atare suka tarar ma danish, suka dinga janshi, kamar dutsi sai nishi suke yi, saboda ya toge yaƙi basu haɗin kai, duk yadda yaso su ƙyale shi amma hakan ya faskara, ba zato ba tsammani suka wurga shi saman gadon angel gaba ɗaya ya faɗa saman jikinta, Har wani firgita ta ɗanyi, sai kuma ta lafa,

Su azeeza sai ihu suke Yi suna dariya, Hada tafa musu hannu,

Bawan Allah Fargaba duk ta cika shi, so yake ya É—aga ta amma yana shakkar su haÉ—a ido da ita, kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, Tana iya jiyo sautin numfashinsa dake sauka saman fatar kafaÉ—arta,

"Alƙawari Ya karye tunda Kun hada jiki, Ko ba haka ba guys? Haris ne yae musu tambayar suka haɗa baki wurin cewa"Yeah" sai tiƙar dariya suke yi hankalinsu kwance, kamar waɗanda A ka yi wa Albishir da mukullin fita daga cikin kurkukun ƙaddara,

Ita kanta angel mutuwar kwance ta yi, tun da ya faɗo saman jikinta, ta gaza motsa koda yatsun hannunta ne, sai faman sauke ajiya zuciya take yi, yafi a ƙirga, maimakon taji haushin kwanta mata jiki da yayi saima taji wani irin sanyi mai daɗi yana ratsa zuciyarta, ta yi matuƙar yin kewar shi, almost 1 month Basu shiri da juna, till today da Allah yasa Su haris suka taimaka wurin hankaɗo shi, yanzu aiki ya rage nata wurin ƙoƙarin ganin sun haɗa ido, hakan zai tabbatar da cewa Alƙawarin su ya karye...............💋

*❤❤❤PRISONERS❤❤❤*

Ƴar ƙara ta saki kamar wadda aka Cixa, a matuƙar ruɗe Danish ya ɗago da kanshi daga saman shoulder ɗinta, sam bai yi tsammanin idanuwanta a buɗe suke ba, saboda ta ɗan lumshe su, tana ganin ya ɗago ta zaro su acikin nashi, har saida yaji gaban shi ya faɗi, Su haris dake kewaye da gadon sai ihu suke yi suna faɗin"Alƙawarin Ya karye, Ya 6alle, Ya ruguje Ya rushe," gwanin ban dariya Sai nishaɗi suke yi abun su, A wani irin yanayi suke kallon juna, ɗaga mashi gira tayi tare da kashe mishi ido ɗaya yadda kasan ƴar duniya tace"Alƙawari Ya karye, Irin wannan kallo haka kamar xaka Lashe ni," lumshe idanuwan shi yae still ya sake opening dinsu slowly on her face, ya rasa dalilin kallon ƙurullan da yake yi mata, ko na second ɗaya baya son ya kawar da eyes ɗinshi daga kallon kyakkyawar fuskantarta.
Chapter 116 · 0% Book details